GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINMALAMAI.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA TARIHIN MUSULUNCI DA TARIHIN MALAMAN SUNNAH MAGABATA DAMA MALAMAM MU NA YANZU ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{mumbarinmalamai@gmail.com]

Tuesday 4 March 2014

TARIHIN AL HASSAN ƊAN ALI RALIYALLAHU ANHU

Al Hassan Ɗan Ali Raliyallahu Anhu

5.1 Sunansa Da Asalinsa
            Sunansa Al Hassan ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib. Mahaifiyarsa ita ce Faɗimah ɗiyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ana yi masa kinaya da Abu Muhammad.
            An haife shi a tsakiyar watan azumin shekara ta uku bayan hijrah, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne da kansa ya sanya masa suna, ya kuma yanka masa rago.[1]
            Al Hassan ɗaya ne daga cikin mutanen da su kayi kama da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a siffar jikinsu. An bayyana cewa, kamannunsa da Mnazo Sallallahu Alaihi Wasallama sun fi yawa a saman jikinsa, a yayin da shi kuma Hussaini ya fi kama da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a ƙasansa.
Duk da ƙarancin shekarun Al Hassan a zamanin kakansa, amma yana tuna kaɗan daga abubuwan da suka auku a wannan lokaci. Abul Haura'i ya tambaye shi, me kake tunawa a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Sai ya ce, na ɗauki wani ɗan dabino daga dukiyar sadaka, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cire shi daga bakina da sauran yawuna a kansa ya mayar da shi a inda na ɗauko shi.[2]
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance ya na son 'yan tagwayen nan[3] na 'yarsa, so wanda ba ya ɓoyuwa. Ya kan kuma yi musu addu'a ya ce, "Ya Allah! Haƙiƙa ina son su, Ya Allah! kai ma ka so su". Wannan kuwa ya sa masu kwarjini sosai da ƙauna a wurin Sahabbai waɗanda ƙaunar Manzon Allah ta sa suna son duk abin da ya ke ƙauna.

5.2 Siffarsa
            An siffanta Al Hassan da cewa, kyakkyawa ne, mai kwarjini da fara'a da son jama'a da kyauta da yawan Ibada.
            Daga cikin ƙoƙarinsa a Ibada ya yi hajji har sau goma sha biyar, a mafi yawansu ya kan tafi da ƙafafunsa, a lokacin da ake janye da raƙumansa. Haka kuma an ruwaito cewa, sau uku Al Hassan ya na kasa dukiyarsa kashi biyu ya yi sadaka da kashi ɗaya, kuma a kullum ya kan karanta Suratul Kahf  kafin ya yi bacci.
Daga cikin karimcinsa da yawan sadakarsa  an ba da labarin ya ji wani bawan Allah ya na addu'a ya na roƙon Allah ya ba shi Dirhami dubu goma, nan take Al Hassan ya koma gida ya aika masa da waɗannan kuɗi.
Al Hassan kuma mutum ne mai yawan aure, yawan matan da ya aura kuwa sun kai 90. A ko da yaushe ya na tare da macce huɗu, idan ya saki nan take zai sake aure. Mutane kuma na  son haɗa zuri'a da shi don sharifantakarsa.[4]
Daga cikin matan da ya aura akwai  Ummu Ishaƙ ɗiyar Ɗalhah wadda ta haifa masa Ɗalhah. Bayan mutuwarsa sai ƙaninsa Hussaini ya aure ta, shi kuma ta haifa masa Faɗimah.

5.3 Darajojinsa
            Al Hassan ya yi tarayya da ɗan uwansa Al Hussaini wajen kasancewarsu shugabannin matasan aljanna.[5]
            Al Hassan ya keɓanta da wata babbar martaba wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bada bushara da ita, cewa, shi shugaba ne wanda zai kawo ƙarshen wata tarzoma wadda zata gudana a tsakanin manyan ƙungiyoyi biyu na Musulmi kamar yadda za mu gani a nan gaba.[6]

5.4 Al Hassan Ya Gadi Mahaifinsa
            Al Hassan na daga cikin waɗanda suka bai wa Ali shawarar kada ya fita daga Madina. Tare da kuma ya tsani yaƙin da aka yi, amma ya yi ɗa'a ga mahaifinsa wajen fita tare da shi. Daga bisani da al'amurra suka dagule Ali ya rinƙa ce masa "Kaicona da na bi shawararka".
            A lokacin wafatin Ali akwai a cikin Sahabbai waɗanda su ke gaba da Al Hassan kamar Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas da Sa'id ɗan Zaid waɗanda ke cikin mutane goma da suka samu busharar aljanna daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sa'ad kam ma ai ya yi takara da Ali kamar yadda mu ka gani a ƙarshen khalifancin Umar. Ga zahiri shi ma Sa'id ya cancanta, sayyiduna Umar ya ƙi sanya shi ne a cikin kwamitin saboda dangantakarsu domin ƙaninsa ne ta wajen mahaifinsa kuma shi yake aure da ƙanwarsa wadda mu ka ba da labarin ita ce dalilin musuluntarsa.
            Ban da waɗannan akwai tsararrakin Al Hassan kamar su Abdullahi ɗan Umar da Abdullahi ɗan Abbas (ƙanin Ali ta wajen mahaifinsa) da kuma Abdullahi ɗan Zubair (Jikan Sayyiduna Abubakar ta wajen mahaifiyarsa).
            Al Hassan ya nuna rashin sha'awarsa ga wannan al'amari bayan da ya ga irin wahalar da mahaifinsa ya sha akai. Ga shi kuma ya yi la'akari da irin yanayin magoya bayan ubansa, wato mutanen Iraƙi waɗanda ba su da biyayya ko kaɗan. To, amma kuma ya zama tilas Al Hassan ya karɓi mubaya'a bayan da jagororin rundunar Ali suka nace a kan haka.

5.5   Ramin Shuka Ba Zurfi Sai Tarin Albarka
Kafin ya miƙa hannunsa ayi masa mubaya'a sai da Al Hassan ya sharɗanta ma su su yaƙi duk wanda ya yaƙa, wanda kuma ya sulhunta da shi su amince a kan sulhun.
Wannan sharaɗi da al Hassan ya sanya ya kashe ma mayaƙa jiki ƙwarai har suka rinƙa tsegumi a kansa. Suna cewa, Al Hassan ba zai kammala aikin babansa ba na yaƙar mutanen Sham.
Ana haka ne wasu daga rundunar sojinsa suka kai masa hari da wuƙa da nufin kashe shi a lokacin da aka samu raɗe raɗin cewa, an kashe Ƙaisu ɗan Sa'ad, ɗaya daga cikin kwamandodinsa, magoya bayan Ƙaisu su kayi ma Al Hassan a ture a cikin hemarsa har ya samu rauni a cinya, suna tuhumarsa da cewa shi ya sa aka kashe shi, alhali kuwa maganar tun asalinta jita - jita ce kawai.
Allah dai ya kuɓutar da Al Hassan daga mutuwa a wannan hari da aka kai masa. Bayan wasu 'yan watanni sai ya mirmije daga raunin da ya samu. Wannan ya ƙara sanya ƙyamar mutanen Iraƙi a gare shi da ma khalifancin baki ɗaya.
Bayan da ya samu sauƙi Al Hassan ya yi wata huɗuba mai gauni a kan mimbari wadda a cikinta yake zargin mutanen Iraƙi da rashin ladabi, yana kuma faɗakar da su game da matsayinsu (Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan huɗubar ta sanya mutane da yawa a Masallacin Kufa yin kuka.
A daidai wannan lokaci da mu ke magana a kansa, Mu'awiyah na can a cikin jama'arsa, mutanen Sham, waɗanda suka shahara da cikakkiyar biyayya a gare shi. Sun kuma yi masa Mubaya'a a matsayin khalifa tun bayan wafatin Ali. Idan faɗansu da Ali ba mai dalili ba ne ta fuskar jayayya a kan shugabancinsa, a yanzu faɗa mai cikakken dalili zai fara tun da ya ke an samu sarakuna biyu masu amsa suna iri ɗaya.
Mutanen Iraƙi kuwa ba su gushe ba suna ingiza Al Hassan har sai da ya yi shiri da nufin yaƙar Mu'awiyah kamar yadda mahaifinsa ya yi. Ya tsara runduna ta mutane 40,000 (dubu arba'in), ya soma da aika gungun farko waɗanda aka kira "Rundunar Alhamis" a ƙarƙashin jagorancin wani jarumi da ake ce ma Ƙaisu ɗan Sa'adu ɗan Ubadah. Adadin wannan runduna ya kai mutum 12,000 (dubu goma sha biyu). Sun kuma tasar ma birnin Sham in da suka yada zango a wani wuri da ake kira Maskan.
A nasa ɓangaren, rahotanni sun zo ma Mu'awiyah game da fitowar rundunar Iraƙi. Saboda haka sai ya fito da kansa don ya tarbe su, ya yi nasa sansani a wurin wata gada da ake kira Mambij.

5.6 Zama Lafiya Yafi Zama Ɗan Sarki
            Al Hassan dai tun da farko mun faɗi ba ya son wannan arangama wadda ta ci ƙarfin Musulmi, ta hana su kwanciyar hankali ballantana ci gaba da yaɗa addini. Shi kuma Mu'awiyah da ya haɗu da "Rundunar Alhamis" sai hankalinsa ya tashi. Na hannun damansa, Amru ɗan Ass ya ce masa, wannan runduna ba zata watse ba sai sun kashe irinsu a cikin jama'armu. Mu'awiyah ya ce, to, idan ko haka ta faru yaya za ayi da yawan zawarawa da marayu? Wane shugaba zai ji daɗin mulki a irin wannan yanayi? Daga ƙarshe sai su kayi shawarar aika waƙilai zuwa wurin Al Hassan don neman sasantawa.
            Wakilan da Mu'awiyah ya tura su ne, Abdullahi ɗan Amiru ɗan Kuraiz da kuma Abdur Rahman ɗan Samurah. Sun kuma tarar da Al Hassan sun tattauna da shi inda ya bayyana ma su ƙudurinsa na sauka daga khalifanci ya danƙa ragwamarsa ga Mu'awiyah bisa ga sharuɗɗan da za su sanya don neman a zauna lafiya, al'ummar Musulmi taci gaba. To, amma fa Al Hassan ya gamu da cijewa ta wajen kwamandan "Rundunar Alhamis" Ƙaisu ɗan Sa'ad wanda bai goyi bayan haka ba, kuma ya keɓe kansa da rundunarsa don ƙalubalantar wannan sulhu.

5.7 Ja Da Baya Ba Tsoro Ba
            Al Hassan dai ya dage a kan wannan manufar tasa wadda ta tabbatar masa da faɗin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa,  "Wannan jikan nawa shugaba ne. Kuma Allah zai sasanta waɗansu manyan rundunoni biyu daga cikin Musulmi a dalilinsa"[7]
            A ranar da zai miƙa mulkin ga Mu'awiyah, Al Hassan ya yi wata huɗuba wadda ta nuna kaifin basirarsa da tausayinsa ga wannan al'umma, in da ya bayyana masu dalilansa na son zaman lafiya domin zama lafiya ya zama ɗan sarki, kai ya ma fi zama sarkin. A cikin wannan huɗubar har wayau yana cewa:
...Ku sani wanda ya fi kowa dabara shi ne wanda ya ji tsoron Allah.
Wanda ya fi kowa wauta kuwa shi ne wanda ya kangare (daga ɗa’ar Allah).
Ya ku mutane! Tun farkon wannan al'amari (yana nufin yaƙi) ni ne na fi ku ƙyamarsa, a yanzu kuma ni ne na kawo gyara a cikinsa.
Zan mayar da haƙƙi ga ma'abocinsa, ko kuma in haƙura da haƙƙena don maslahar al ummar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Ya kai Mu'awiyah! ka sani wannan al'amari Allah ya ɗora ma ka shi don wani alheri da yake tare da kai ko kuma don sharrin da ya sani a wurinka.
Sannan ya karanta wannan ayar:

﴿ وَإِنْ أَدْرِي لَعَلَّهُ فِتْنَةٌ لَكُمْ وَمَتَاعٌ إِلَى حِينٍ ﴾ [سورة الأنبياء:111].
Ma'ana:
Kuma ni ban sani ba, wataƙila fitina ne a gare ku da ɗan jin daɗi zuwa wani lokaci.   Suratul Anbiya', Aya ta 11.
            Al Hassan dai ya yi amfani da sharaɗin da ya sanya ma mutanen Iraƙi wanda a dalilinsa ya zame masu tilas su karɓi wannan sulhu. Allah kuma a cikin rahamarsa sai ya karkato da zuciyar Ƙaisu ɗan Sa'ad da rundunarsa bayan cijewar da su kayi. Al Hassan ya samu shawo kan Ƙaisu daga baya kuma har ya kawo shi da kansa a wurin Mu'awiyah. Ƙaisu duk da haka sai da ya laƙe hannunsa can ga cikinsa a maimakon ya miƙa shi ya yi mubaya'a ga sabon khalifa. Amma dai Mu'awiyah ya daure ya kai nasa hannun can su kayi musafaha, hujja ta tabbata a kan Ƙaisu ke nan don ya yi mubaya'a.
Wannan shekarar ta zame ma musulmi watan bakwai maƙarar rani. Domin kuwa kusan dukkan Musulmi sun haɗu a kan jagora ɗaya in ban da ƙungiyar Khawarij. Akan haka ne aka raɗa mata suna Amul Jama'ah wato, shekarar haɗin kai.

5.8 Kyakkyawar Sakayya Ga Al Hassan
Da yake wanda duk ya bar wani abu saboda Allah to, Allah zai musanya masa ya ba shi wanda ya fi shi ko ya bai wa zuri'arsa, wannan karimci na Al Hassan zai gamu da sakayya ta Ubangiji can a ƙarshen zamani domin kuwa daga cikin zuri'arsa Allah zai fitar da Mahdi, wanda zai amshi ragamar shugabancin Musulmi don ya kawo gyara a wannan lokaci.[8]
5.9 Matsayin Hussaini A Kan Wannan Sulhu
            Al Hussaini ya lizimci kawaici game da abinda ya faru amma a zuci bai ji daɗin yin hakan ba. To, sai dai ya yi mubaya'a ya ɓoye damuwarsa.
            A lokacin wafatinsa Al Hassan ya kira ɗan uwansa ya yi masa gargaɗi, ya ce, kada ka bari mutanen Iraƙi su ruɗa ka. Kada kuma ka kuskura ka kwance mubaya'ar da ka yi ma Mu'awiyah. Ka sani alamu sun nuna Allah ba zai haɗa annabta da khalifanci a gidanmu ba. Don haka kada ka sa kanka cikin nemansa.
            Duk tsawon mulkin Mu'awiyah kuwa Al Hussaini ya riƙe wasiccin ɗan uwansa. Amma a lokacin da Mu'awiyah ya ɓullo da wata maganar naɗin yarima da yi masa mubaya'a, kuma ya zaɓi ɗansa Yazidu, to, a nan Al Hussaini ya cije, ya ƙi ba da mubaya'arsa ga yarima mai jiran gado. Haka shi ma Abdur Rahman ɗan Abubakar ya yi, bai yi wannan mubaya'a ba.
            A lokacin da Mu'awiyah ya haƙiƙance mutuwa ta zo masa kusa ya kira ɗansa Yazidu ya yi masa wasicci wanda za mu kawo shi a nan gaba, a cikinsa kuwa har da maganar wasu mutane da suka haɗa da Al Hussaini wanda Mu'awiyah ya ce, ka kula da alfarmar gidansu da son da jama'a su ke masa.

5.10 Mutuwar Al Hassan
            Al Hassan ya rayu sama da shekaru goma bayan sauka daga muƙaminsa. A cikin waɗannan shekarun an samu kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da Sarki Mu'awiyah. Sukan karɓi kyaututtukansa shi da ɗan uwansa Al Hussaini kuma su gaida shi gaisuwar girmamawa irin wadda ake masa.
            A shekara ta Arba’in da biyu bayan hijira ne Al Hassan ya ci wani abinci mai guba wanda shi ne ya zama ajalinsa.[9] Kuma ana tuhumar wata tsohuwar matarsa da suka rabu da yin wannan makirci. Sanin gaibu sai Allah.
            Da Al Hassan ya lura da kusantowar ajali sai ya yi wasicci ga ɗan uwansa da abin da mu ka faɗa, kuma ya neme shi da ya roƙa masa alfarma daga wurin Uwar Muminai A'ishah domin yana son a yi masa makwanci kusa da kakansa. Ya ce, amma idan ba ta aminta ba ka kai ni a maƙabartar Baƙi'ah in da sauran Musulmi.
            Da Al Hassan ya cika Nana A'isha ta yi na'am da buƙatarsa, amma kuma shaiɗan ya zuga Marwanu, ɗaya daga cikin dangin khalifa Usman wanda ya yi tsaye a kan ba za a rufe Al Hassan a wurin ba, domin a lokacin wafatin Usman an nemi wannan alfarma kuma A'isha ta amince amma aka hana shi. An samu ruɗani sosai a kan wannan, amma daga baya Abu Huraira ya sasanta tsakaninsu kuma an rufe Al Hassan a maƙabartar Baƙi'ah.[10]
            Sarautar Al Hassan dai kamar ramin shuka ce, ba zurfi sai tarin albarka. Domin kuwa duka duka wata shida ne ya yi akan wannan muƙamin ɗauke da mubaya’ar mutanen Iraƙi da wasu sassa na daular musulunci, a dai dai lokacin da Mu’awiyah ke jimƙe da mubaya’ar mutanen Sham. Sai ga shi a dalilin Al Hassan da haƙurinsa kan al’umma ya haɗu akan shugaba guda sun dawo kamar tsintsiya mai maɗauri ɗaya.








[1] Bayan haka ne aka samu cikin ƙaninsa Hussaini bayan haifuwarsa da wata biyu, wanda shi kuma aka haife shi a cikin watan sha'aban na shekara ta 4 bayan hijra.
[2] Al Isabah Fi Tamyizis Sahabah, na Ibnu Hajar, Tahƙiƙin Ali Muhammad Al Bijawi, Bugun Darul Jil, Beirut, 1412H, (2/69).
[3] Mun riga mun faɗi cewa, ba tagwaye ba ne. Amma saboda kusancin shekarunsu (wata goma sha ɗaya ke tsakaninsu) da kuma al'adar Bahaushe da ta gudana a kiransu tagwaye mu ma muka tafi a kan haka. Don haka ya zama dole mu yi tambihi.
[4] Siyar A'lam An Nubala', na Dhahabi, (3/253).
[5] Al Jami', na Tirmidhi, Hadisi na 3768 da kuma Al Musnad, na Ahmad, (3/3 da 3/62) da Al Mustadrak, na Hakim, (3/167) kuma Tirmidhi ya inganta shi.
[6] Duba wannan busharar a cikin Sahihul Bukhari, (7/74) da Al Jami', na Tirmidhi, hadisi na 3775.
[7]  Duba Sahihul Bukhari a Kitabul Manaƙib, Babin darajojin Al Hassan da Al Hussaini da kuma Siyar A'lam an Nubala'  (3/259).
[8]  Mutane sun kasu kashi uku dangane da Mahdi. Akwai masu ganin cewa, Mahdi shi ne Annabi Isah, akwai kuma masu ganin shi ne Sarkin Musulmi Mahdi ɗan Abun Ja’afar Al Mansur daga zuri'ar Abbas (Baffan Manzon Allah SAW) wanda yana daga cikin jerin sarakunan daular Abbasiyyah. Su kuma a wurin Rafilawa ('Yan shi'a masu da'awar bin Imamai 12) sun ce shi ne Muhammad ɗan Hassan Al Askari daga zuri'ar Hussaini. Bayan haka aka yi Muhammad ɗan Tomarat a ƙasar Maroko wanda ya ce shi ne Mahdi, ya kashe bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba, ya ƙwace matansu da 'ya'yansu da zuri'arsu. Bayansa kuma aka yi Ubaidullahi ɗan Maimun Al Ƙaddah (asalinsa Bayahude ne, amma a cikin majusawa ya tashi) shi ma ya ce Mahdi ne. Kuma ya ce yana cikin Ahlulbaiti. Sa'annan aka yi wani mai da'awar shi ne Mahdi a Sudan a ƙarni na goma sha uku bayan hijira. Mahdin gaskiya dai yana nan tafe, kuma daga zuri'ar Al Hassan yake kamar yadda hadissai ingantattu suka tabbatar. Duba Al Manar Al Munif na Ibnul Ƙayyim, shafi na 43.
[9]  Wannan yana nuna cewa, iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba su san gaibi ba. Domin kuwa da Al Hassan ya san gaibi ba zai ci abincin da aka sanya guba a cikinsa alhalin yana sane ba, domin wanda ya yi haka kamar ya kashe kansa kenan.
[10]  Yana cikin hikimar Allah cewa, ba wani Annabi ko Sahabi da aka san wurin ƙabarinsa a haƙiƙance in ban da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da waziransa biyu da ke kwance a ɗakin Nana A'ishah. Duba Takhlisul Ikhwan na Mujaddadi Usmanu ɗan Fodio.



DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO

Tuesday 17 December 2013

TARIHIN SAYYADINA ALI ƊAN ABU ƊALIB RALIYALLAHU ANHU

 Ali ɗan Abu Ɗalib Raliyallahu Anhu

Sunansa da Asalinsa
Sunansa Ali ɗan Abu Ɗalib ɗan Abdul Muɗɗalib ɗan Hashim. Shi ne ƙanin Manzon Allah, domin kakansu ɗaya shi ne, Abdul Muɗɗalib.
Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima ɗiyar Asad ɗan Hashim wadda ita ma ta gama kaka da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Tashinsa
An haifi Ali a shekara ta ashirin da uku kafin Hijira, an aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Ali yana da shekara goma. Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama ya girmi Ali da shekaru talatin. Kuma kamar yadda mahaifinsa ya riƙa Manzon Allah ya kula da shi, shi ma Manzon Allah ya riƙa Ali ya kula da shi.

 Darajojinsa
Kasancewar Ali ya tashi a hannun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tun ba a aiko shi ba, ya bai wa Ali damar ya shaƙi ƙamshin Musulunci tun a rana ta farko. Ali kuwa bai yi wata wata ba ya amsa kiran Allah a hannun yayansa kuma mai gidansa. Don haka Ali shi ne mutum na farko da ya karɓi addinin Musulunci bayan matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Nana khadijah.
            Duk da kasancewarsa yaro ne ƙarami, amma Ali ya ba da gudunmawa wajen kafuwar Musulunci. A tare da shi aka yi Bai'atul Aƙaba, wadda Allah ya ce, ya yarda da waɗanda su kayi ta. Haka kuma ya kwanta a kan shimfiɗar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da zai yi hijira.
            A yaƙin farko da aka yi tsakanin Musulmi da Mushrikai, yaƙin Badar, Ali ya yi fito na fito da babban arnen nan Walid ɗan Utbah kuma ya kashe shi. Sannan ya taimaka ma baffansa Hamza wajen kashe mahaifin wancan na farkon, Utbah ɗan Rabi'ah. A yaƙin khandaƙ kuma shi ya yi fito na fito da Amru ɗan wuddu al Amiri wanda jarumawa ke fargaban karawa da shi, kuma Ali ya halaka shi. A ranar yaƙin Khaibar kuma shi aka bai wa tuta bayan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi alƙawarin bayar da ita ga wanda ya siffanta da cewa, yana son Allah da Manzo kuma Allah da Manzo na sonsa.
            Ali ya auri 'yar Manzon Allah, Fatimah, wadda bai yi ma ta kishiya ba har Allah ya karɓi rayuwarta.
            Ali shi ne ya zamo gwamnan Madina a lokacin da Manzon Allah ya fita da mafi yawan Sahabbai zuwa yaƙin Tabuka. Wannan ya sanya Ali bai ji daɗi ba don rashin kasancewa tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da manyan Sahabbai. Amma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwantar da hankalinsa da cewa, matsayinsa a wurin Manzo ya yi daidai da na Annabi Haruna ga yayansa Musa, duk da yake shi Manzon Allah ba wani Annabi a bayansa.
            Ali ya wakilci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wajen isar da saƙon Suratut Taubah zuwa ga kafiran Makka. Ya kuma je ne a ƙarƙashin jagorancin Sayyiduna Abubakar.

 Matsayin Ali a zamanin Khalifofi
            Ali ya yi mubaya'a ga Abubakar tun da farko kamar yadda ya gabata a baya. Amma bai lizimci fadar Sarkin Musulmi Abubakar ba sai bayan rasuwar uwar gidansa Fatimah, wadda ya kasance yana jinyarta tsawon watanni ukku ko kuma shida.
            Ya halarci yaƙin da Abubakar ya yi da murtaddai (waɗanda suka fita Musulunci bayan rasuwar Manzon Allah) da Annabawan ƙarya, da kuma waɗanda suka ce ba sauran ba da Zakka tun daga wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. A wurin yaƙar musailamatu ne wanda Khalid ɗan Walid ya jagoranta a zamanin Abubakar, Ali ya samu gajiyar matarsa khaulatu ɗiyar Ja'afar ‘yar ƙabilar Banu Hanafi, wadda ta haifa masa Muhammad al Akbar, wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah.
            A zamanin Sarkin Musulmi Umar kuwa, Ali ya karɓi muƙamin alƙalanci, ya kuma yi gwamna a Madina a lokuta da dama.[1]
            Daga baya kuma, surukuta ta shiga tsakaninsa da Sarki Umar ɗan Khaɗɗabi a lokacin da 'yarsa, Ummu Kulsum, wadda Nana Fatima ta rasu ta barta tana ƙarama ta soma girma, sai Sayyiduna Umar ya yi sha'awar aurenta. Ali kuwa bai yi wata wata ba ya ɗaura masa aure da ita. Wannan karimci na Ali ya ƙarfafa danƙon zumunci da ƙauna a tsakaninsa da Sarki mai ci a wannan lokaci, wanda ya bayyana cewa, ba ya da fata kamar ya haɗa zuri'a da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abin da bai tabbata ba a surukutarsa ta farko da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, domin kuwa 'yarsa Hafsah ba ta haifu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ɗin ba. Wannan gurin nasa kuwa ya cika domin sharifiya Ummu Kulsum ta haifa masa 'ya'ya guda biyu, namiji da mace waɗanda ya sa ma su suna Zaidu da Ruƙayyah.
            A lokacin rasuwarsa, Umar ya kafa wani kwamiti na mutum shida waɗanda ya ɗora ma su alhakin zaɓen sabon Sarki daga cikinsu. Ali yana daga cikin membobin wannan kwamiti. Ga dukkan alamu Umar ya yi sha'awar a naɗa Ali, amma tsentseninsa da mu ka sani bai bar shi ya ayyana shi ba, wataƙila saboda surukutar da ke tsakaninsu, sai ya bar Musulmi su zaɓa da kansu, kuma a cikin ikon Allah zaɓin bai faɗa a kan Ali ba a wannan lokaci.[2]
            Ba za mu yi mamakin Umar ya yi sha'awar Ali ya gade shi ba domin sun fi kama da juna a ɗabi'unsu da tsarin rayuwarsu kamar yadda Usman ya fi kama da Abubakar a wajen sanyin halinsa da jin kunyarsa.
            Da aka zaɓi Usman kuwa, Ali shi ne mutum na farko da ya yi masa mubaya'a kamar yadda mu ka gani a baya. Ya kasance a matsayin wazirinsa mai ba shi shawara ko da yaushe kamar yadda yake yi a zamanin Umar.
            Mun kuma riga mun ji irin gudunmawar da Sayyiduna Ali ya bayar wajen kariyar Usman kafin Allah ya ƙaddari aukuwar abin da ya alƙawarta na shahadarsa a hannun 'yan tawaye, mutanen Iraƙi.

 Ali ya zama Sarkin Musulmi
            Bayan da ajali ya cika da Sarkin Musulmi Usman ɗan Affan, al'amurra duk sun rikice a birnin Madina. Ga shi kuma ba'a dawo daga aikin hajji ba wanda Sahabbai da dama suna can, sai 'yan tawaye suka fara tunanin hanyar da zata fisshe su. Abu na farko da su kayi tunani a kansa kuwa shi ne, su taka rawa wajen naɗa khalifa na gaba. A kan haka sun zagaya wurin Ali da Ɗalhah da Zubairu da Ibnu Umar, amma duka sai suka yi biris da su, ko wanensu ya ƙi amincewa da ya karɓi mubaya'arsu domin ba su ne ya kamata su yi wannan ba.[3]
            Haka dai al'amari ya dagule ma su, suka rasa wanda zai fid da su daga wannan rami da suka auka, ga kuma alhazzai suna kan hanya sun kusa isowa Madina, sai su kayi barazanar kashe dukkan waɗanda suka nema da wannan al'amari suka ƙiya ma su. Anan ne fa ya zama dole Ali ya karɓi wannan aiki bisa ga shawarar wasu Sahabbai da suka lura al'amarin zai ida caɓewa ga baki ɗaya.
            An dai samu natsuwa kaɗan da yin mubaya'a ga Ali a Madina. Haka kuma bayan mutanen Madina, daga Iraƙi ma (Biranen Kufa da Basrah) in da can ne mafi yawan 'yan tawayen suka fito, an aiko da mubaya'a, haka ma mafi yawan sojojin Musulmi waɗanda su ke a wuraren yaƙi sun aiko mubaya'arsu.
            Labarin kisan gilar da aka yi wa Usman ya ci gaba da yaɗuwa a sauran birane, yana tafiya lokaci ɗaya da labarin naɗa sabon Khalifa, shi ne Ali. Tambayar da mafi yawa su ke fara yi ita ce, to, ina 'yan tawayen? Me Ali ya yi game da su da aka naɗa shi? Wace irin rawa ya taka yana a Madina a lokacin faruwar wannan lamari?. Rashin samun gamsasshiyar amsa ga wanda bai san haƙiƙanin yadda abin ya faru ba ta sanya mutane da dama daga sauran garuruwa kamar Misra da Yaman da Makka duk ba su yi mubaya'a ba.
Amma waɗanda suka fi kowa adawa da wannan mubaya'a su ne mutanen Sham[4]. Dalili kuwa shi ne, Sham tana ƙarƙashin riƙon Mu'awiyah ne ɗan Abu Sufyan wanda ɗan uwa ne na jini ga marigayi khalifa Usman. Mu'awiyah kuwa mutum ne mai farin jini a wurin talakawansa. Ga shi kuma nan take bayan faruwar wannan ɗanyen aiki aka je da rigar Sayyiduna Usman wadda take cike da jininsa zuwa wurin Mu'awiyah a cikin yanayi wanda ke sa tausai da takaici a kan zaluntar sa da aka yi.
Mu'awiyah ya yi huɗuba mai gauni a kan wannan lamari, kuma ya nemi goyon bayan talakawansa a kan ramuwa da ɗaukar fansa a kan 'yan ta'adda. Mutanen Sham kuwa suka amsa kiransa ƙwansu da kwarkwatarsu. Har ma matan aure sai da suka ɗauki alwashi ba za su sake ɗaukar janaba ba sai an ga ƙarshen 'yan ta'adda.
  Ali ya kafa sabuwar gwamnati
Ikon Allah! Duk wannan abin da ke gudana shi Ali yana can Madina yana yanke shawarar sabunta gwamnati wadda kuma babu Mu'awiyah a cikinta, kamar yadda babu sauran mafi yawan gwamnoni waɗanda ya gada daga gwamnatin da ta gabata. Da Allah ya so wannan abu ya zo da sauƙi to, da Ali ya dakata kamar yadda ƙaninsa Ibnu Abbas ya nuna masa, ya bari sai mutanen Sham sun miƙa wuya, idan tafiya ta yi tafiya sannan sai ya canza Mu'awiyah. To, amma ƙaddara ta riga fata, domin kuwa ba haka Mabuwayin Sarki ya hukunta ba. Don haka sai Ali ya zartas da abinda ya yi niyya.
A Makka kuwa, Uwar Muminai Nana A'ishah tana can ba ta baro ba, domin ta nemi iznin Khalifa Usman a kan zata yi aikin hajji, daga can ne kuma labarin yadda juyin mulki ya kaya ya ishe ta. Tana cikin juyayin wannan lamari sai ga Ɗalha da Zubairu waɗanda suka sulale daga Madina bayan sun yi wa Ali mubaya'a kuma a asirce, sun nemi Ali ya bari su nemo goyon bayan jama'a daga sauran garuruwa don a gama da 'yan ta'adda sai Ali ya ce, su dakata. Daga nan sai suka nuna masa suna da buƙatar fita zuwa Makka amma bai san abin dasu ke nufi ba.[5]
Shawarwari da tuntuɓar juna sun ci gaba a tsakanin jama'a a garin Makka bayan da ya tabbata cewa dai mafi yawan 'yan tawayen har sun fice daga Madina sun nufi garuruwansu. Ɗalha da Zubairu sun ci nasarar shawo kan Nana A'ishah don ta fita tare da su ta ƙarfafi jama'a a kan babban jihadin da su ke son yi a kan 'yan ta'adda. Kuma an yanke shawarar a nemo agaji daga Iraƙi, a kuma fara da ‘yan ta’adda da ke can.
Da suka kama hanyar zuwa Iraƙi, kafin su je Basrah sun shuɗa da wani tafki wanda aka ambaci sunansa al Hau'ab. Jin an faɗi sunansa ke da wuya sai Nana A'ishah ta yi shirin komawa domin ta taɓa jin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana ce ma matansa: wacce ce a cikinku zata ji kukan karnukan Hau'ab, ta shiga gumuzun yaƙi har a kashe mutane a dama da hagunta, kuma ta tsira da ƙyar bayan ta kusa ta halaka?
Al'amarin da Rabbus Samawati ya hukunta ba wurin kauce masa. Don haka sai Ɗalhah da Zubairu suka hana ta komawa, suka ce da ita, ba ruwanki da yaƙi, abin da mu ke so kawai shi ne, 'ya'yanki Musulmi su gan ki, su san kina da goyon bayan wannan lamari don su samu kuzarin ba da himma a cikinsa. Nana A’isha sam bata gamsu da haka ba, amma ƙaddara ta riga fata.[6]

4.5 Yaƙin Basasar Raƙumi
 Matsayin Ɗalha da Zubairu
            Tun da farko kamar yadda muka gani, Ɗalhah da Zubairu sun nemi Sayyiduna Ali ya ba su dama domin su je Basrah da Kufa su nemo agajin mayaƙa saboda a hukunta ‘yan tawaye kafin su bar Madina, amma Ali yana ganin lokacin yin haka bai yi ba.
            Daga baya sai suka neme shi iznin su je Makka kamar da nufin yin Umrah. Da suka je Makka sai ra’ayinsu ya haɗu da ra’ayin Nana A’ishah a kan nemo taimako domin a tunkari waɗannan ‘yan ta’adda. Da haka ne suka sami damar fita zuwa Basrah tare da Uwar Muminai a daidai lokacin da Sarkin Musulmi Ali yake cikin shirin fita zuwa Sham domin ya tilasta mutanenta a kan yi masa mubaya’a da su da jagoransu Mu'awiyah. Saboda ya aika sabon gwamnansa Sahlu ɗan Hunaifu  zuwa can an koro shi.[7]
            A lokacin da labarin fitowar su Zubairu ya kai ga Sarkin Musulmi Ali sai nan take ya canza shawara daga tafiya Sham ya tasar ma hanyarsu domin ya dakatar da su daga zuwa Basrah. Saboda bai kamata su yi gabansu da sha’ani irin wannan ba tare da sun tuntuɓi shugaba ba kuma sun tafi a kan umurninsa. Nufinsa idan ya haɗu da su a kan hanya sai ya dakatar da su tun ba su kai ba. Amma ina! ƙaddara ta riga fata. Kafin ya farga tuni sun kai Basrah har sun fara zartas da abinda ya kai su.
            Daga ɓangaren gwamnan Basrah kuwa, Usmanu ɗan Hunaif Raliyallahu Anhu aikawa ya yi da wakilai biyu Imrana ɗan Hussaini da Abul Aswad al Du’ali domin su tattauna da jagororin mutanen Makka don su ji abin da ke tafe da su. Dukkansu sun faɗi cewa, sun zo ne suna neman agaji domin faɗa da ‘yan ta’adda waɗanda suka kashe Khalifan Manzon Allah a cikin gari mai daraja, a kuma wata mai alfarma.
            Gwamna ya fahimci lalle akwai tashin hankali domin kuwa kafin isowar su Ɗalha sai da ya tara mutane a Masallaci domin ya yi shawara da su a kan matakin da zai ɗauka, sai wani mutum ya yi katsalandan kafin gwamnan ya ce komai, ya ce, Ya ku jama’a waɗannan mutane suna neman ɗaukar fansar Usmanu ne, mu kuma ba mu muka kashe shi ba. Idan ko suna neman aminci ne to, ya suka baro garin da ko tsuntsu ba’a firgitawa a cikinsa? Nan take wani ya tashi ya ce masa, Ai sun zo ne domin mu taimaka musu a kan waɗanda su kayi kisa ko suna a cikinmu ko ba su a cikinmu. Sai kawai mutane suka fara jifarsa. Duka wannan ya faru a lokacin da labari ya game gari cewa, rundunar Makka tana bisa hanya amma tukuna ba su riga suka iso ba.
            Da jama’ar Ɗalha suka iso Basrah ba su shiga a cikin gari ba sai da suka yada zango a wani wuri da ake kira Mirbad  in da masu goyon bayan tafiyarsu suka je suka same su. Shi ma kuma gwamnan sai ya tafi da tawagarsa domin ya tattauna da su.
A lokacin da suka isa, Ɗalhah da Zubairu sun yi jawabai suna masu bayyana takaici a kan abinda ya faru a Madina, suka kwaɗaitar da mutane a kan ɗaukar fansa. Amma wasu mutane da ke cikin tawagar ɗan Hunaif – gwamnan Basrah – sun mai da martani a kansu. Nana A’ishah ma sai da ta sa bakinta. Nan take sai aka fara jefe jefe, wasu kuma daga cikin mutanen Basrah suka ƙara runtuma cikin rundunar Uwar Muminai. Daga baya dai hankali ya kwanta.
            Ba a watse daga wannan haɗuwar ba sai ɗaya daga cikin ‘yan tawaye waɗanda suka je wurin kashe Khalifa Usman ana ce da shi Hakimu ɗan Jabalah wanda kuma shi ke jagorantar ɓangaren mahaya dawakai a rundunar gwamnatin Basrah ya yi ƙoƙarin tada faɗa. Duk ƙoƙarin da Nana A’isha ta yi a kan ganin an kwantar da hankali bai yi amfani ba, domin kuwa sai da wannan taƙadarin ya hasa wutar yaƙi. An dai wuni ana gwabzawa a tsakanin rundunonin guda biyu, kuma aka wayi gari aka ci gaba, aka yi hasarar rayuka da dama daga ko wane ɓangare, aka kuma jikkata mutane da dama.
            A lokacin da rundunar Makka ta samu sa’a sai suka kama gwamna a hannu, amma Nana Aishah ta sa baki aka sake shi, sannan ta yi umurni aka rinƙa kamo waɗanda aka sani cikin ‘yan ta’adda mutanen Basrah, aka kuma kashe da yawa daga cikinsu. Sai dai wasu kam sun gagara domin danginsu sun fito sun taimaka masu sun basu kariya. Misali wani mashahuri a cikinsu ana ce masa Hurƙusu ɗan Zuhairu, mutum dubu shida suka fito daga cikin ƙabilarsa - Banu Sa’ad – don kariyarsa shi kaɗai. Abin da Ali ya hango ya fara tabbata kenan. Amma dai shi Alin yana kan hanya bai iso ba tukuna.
            Da Sarkin Musulmi Ali ya kusanto Basrah sai ya aika wani jarumi mai suna Ƙa’aƙa’u ɗan Amru don ya kira Ɗalha da Zubairu zuwa ga ɗa’a da dawowa ƙarƙashin shugaba saboda a haɗa kan jama’a. Ga yadda tattaunawarsu ta kasance:
            Isowar Ƙa’aƙa’u ke da wuya sai ya tunkari Uwar Muminai ya tambaye ta abinda ya fito da ita, sai ta gaya masa cewa, ta fito ne domin ta yi gyara a tsakanin mutane. Sai ya ce da ita, ki aika a kira Ɗalhah da Zubairu domin su ma in ji ta bakinsu. Da suka zo ya tambaye su sai suka ba da amsa irin ta Nana A’ishah, sai ya ce da su, zan tambaye ku, shin kuna a kan biyayya ga Sarkin Musulmi ko kun fita daga ɗa’arsa? Idan kuna a kan biyayya to, ku faɗi irin gyaran da kuke nufi sai a gaya masa ya yi. Sai suka ce masa, mu abinda ya dame mu shi ne, ƙyale waɗanda suka kashe Khalifa Usman, domin ƙyale su yin watsi ne da hukuncin Alƙur'ani.
 Ƙa’aƙa’u ya ce, to ga shi kun kashe kusan mutane ɗari shida, amma ga mutum ɗaya ya gagare ku, kuma mutane dubu shida sun ba shi kariya daga gare ku. Idan ku ka ƙyale shi kun yi watsi da littafin Allah a cewarku, idan kuma kun ce sai kun kashe shi ɓarnar da za ku janyo ma wannan al’umma tana da yawa. Yanzu dai kun tono ƙabilancin jahiliyyah ke nan a tsakanin Musulmi.
            Da Nana A’ishah ta ji wannan jawabi nasa sai ta ce, to yanzu mine ne shawara? Sai ya ce, a kwantar da hankalin mutane. Idan Ali ya iso ku shiga cikin jama'arsa, kowa ya san cewa, kalmarmu ta zama a haɗe, duk wani kangararre zai ji tsoronmu, fansar jinin Usmanu kuma sai in da ƙarfi ya ƙare.
            Ana iya cewa kusan kowa ya gamsu da wannan bayanin kuma an tsayu a kansa. A sakamakon haka an yi musayar saƙonni daga ɓangaren Ali da na mutanen Makka (ina nufin jama’ar Uwar Muminai da su Ɗalhah) kome ya fara komawa daidai.
            To, a lokacin da Sarkin Musulmi Ali ya tasar ma isa Basrah sai ya yi wata huɗuba wadda a cikinta ya ɗauki mataki mai tsauri a kan duk wanda aka san yana da hannu wajen kashe Usman, kuma ya sanya dokar kada wanda ya bi shi daga cikinsu. A nan ne ‘yan tawaye suka fahimci cewa, kashinsu ya bushe idan suka bari wannan gyara ya tabbata. Don haka sai suka koma kan teburin shawara, suka kuwa haɗu a kan sake tada fitina da hasa gobarar yaƙi a tsakanin Musulmi.
            A daidai lokacin da Uwar Muminai ta ke jiran isowar Ali sai ga labari ya zo mata, ta wurin Ka’abu ɗan Sauru, alƙalin garin Basrah cewa, ga yaƙi can ya sake ɓarkewa a tsakanin mutane. Ya ce, ki yi gaggawa wataƙila Allah zai kwantar da wannan tarzoma idan kika sa baki. Nan ta ke Nana A’ishah ta hau raƙuminta ta tasar ma wurin da ƙura ta ke tashi, sai ta tarar da Sayyiduna Ali yana ta famar dakatar da rikici. Da farko Ka’abu ne yake jan ragamar raƙuminta, amma sai ta umurce shi da ya je gaba ya kira mutane zuwa ga littafin Allah. Tuni ‘yan ta’adda suka kashe Manzon na A’ishah, ita kuma su kayi ta jifar raƙumin da ta ke a kansa.
            Ɗalhah ya samu rauni mai tsanani wanda a sakamakonsa ya koma cikin garin Basrah bisa ga shawarar Ƙa’aƙa’u, kuma a can ne ya gamu da ajalinsa. Zubairu kuma da ya lura da sauyawar al’amari sai ya zame jiki daga wurin yaƙin, amma duk da haka sai da wata ƙungiya ta 'yan tawaye a ƙarƙashin jagorancin Amru ɗan Jarmuzu suka bi shi suka kashe shi.
            Cibiyar yaƙi ta koma a wurin raƙumin da Uwar Muminai ta ke a kansa. Sama da mutane arba’in suka rasa rayukansu nan ta ke. Sayyiduna Ali ya lura da haɗarin wannan lamari sai ya ba da umurnin a soke wannan raƙumi. Wannan dabarar tasa kuwa sai ta yi nasara domin soke raƙumin ke da wuya sai mutane suka watse daga wurin. Sannan ya umurci ƙanenta Muhammad ɗan Abubakar tare da Budailu ɗan Warƙa'u da su fitar da ita daga rumfar wannan raƙumi, su nisantar da ita daga fagen yaƙi. Sannan Muhammad ya wuce da ita cikin garin Basrah a ƙarshen dare in da ta samu mafaka a gidan Safiyyah ɗiyar Harisu uwar gidan Abdullahi ɗan Khalaf.
            A ranar litinin 14/6/36 bayan hijira Sarkin Musulmi ya shiga birnin Basrah bayan da ya jagoranci sallar jana’iza ga dukkan mamatan ɓangarorin guda biyu, kuma ya yi addu’a da neman gafarar Allah ga duk wanda yake da tsarkakakkiyar niyya daga cikinsu. Sannan ya haɗu da Nana A’ishah suka jajanta ma juna bisa ga abin da Allah ya ƙaddara, ya yi mata rakkiya, ya umurci ‘ya’yansa da wasu mata arba’in daga Basrah su taka ma ta. A wurin bankwana Nana A’ishah da Ali sun yi wani jawabi mai ban tausai matuƙa, in da ko wannensu ya bayyana juyayinsa ga abinda ya faru da yadda aka keta umurninsu cikin wannan lamari. Nana A’ishah ta yabi Sarkin Musulmi Ali tana mai nuni ga tashinsa a gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta ce kuma bai taɓa muzguna mata ba a tsawon zamansa a gidan a matsayin ƙanen mijinta. Shi kuma a nasa ɓangaren sai ya nanata ma al’ummar Musulmi irin matsayin da Nana A’ishah ta ke da shi, ya ce kuma, ita matar Annabinku ce a duniya da lahira.  
            Haka dai yaƙin da ‘yan tawaye suka haddasa ya zo ƙarshe. Mafi ingancin bayani game da hasarar rayuka kuwa shine an rasa mutane ƙimanin dubu biyu da ɗari biyar (2500) daga rundunar su A'ishah, da kuma dubu huɗu (4000) daga ɓangaren Ali.
Dalillai sun nuna barrantar ko wane ɓangare na Ali da na Aishah daga wannan yaƙi. Alal misali, wanda ya kashe Zubairu ya zo ya yi bushara ga Sayyiduna Ali cewa ya kashe abokin faɗansa, amma sai Ali ya nuna ɓacin ransa kuma ya yi masa bushara da wuta! Nana A'ishah kuma ta yi nadama matuƙa, kuma ta kan yi kuka sosai har sai ta jiƙe mayafinta wajen goge hawaye. A dalilin haka ne kuma ta sauya ra'ayinta na yi mata ƙabari a cikin ɗakinta kusa da mijinta (Manzon Allah SAW) da mahaifinta (Abubakar).[8]
            Ali shi ma ya ji takaicin faruwar wannan al'amari. Ba haka aka so ba, amma ƙaddara ta riga fata. Ikon Allah! bayan wata biyu kacal da tsaida wannan yaƙi, sai ga wani irinsa ya sake ɓarkewa.



 Yaƙin Basasar Siffin

 Har Yanzu Mu'awiyah Raliyallahu Anhu Bai Yi Mubaya'ah ba
            Bayan da aka ƙare yaƙin basasar raƙumi, Ali ya aika wani Manzo mai suna Abu Muslim al Khaulani domin ya jawo hankalin Mu'awiyah a kan haɗewa da sauran al'ummar Musulmi waɗanda su kayi mubaya'a. Amma ga alama wannan karon Mu'awiyah ya fi tsananin cijewa ma fiye da in da aka fito.
            Ali ya sake aika shahararren Sahabin nan Nu'uman ɗan Bashir, shi ma dai bai ci nasara ba. Daga nan ne Ali ya yanke shawarar yaƙarsa. Ya fara tura runduna wadda ta ƙunshi mayaƙa kimanin 6000 zuwa 7000 ƙarƙashin jagorancin Ashtar An Nakha'i domin su fara kai farmaki a kansa.
            Kafin Ali ya aike da rundunarsa kuwa sai da ya jinjina ƙarfin Mu’awiyah da jama’arsa. Hanyar da ya bi wajen gano ƙarfin Mu’awiyah ita ce, ya aika wani mutum wanda ya nuna alamun shi matafiyi ne daga Iraƙi yana mai sanar da Mu’awiyah cewa, ga Ali nan tafe da rundunarsa zai yaƙe ku. Da Mu’awiyah ya ji wannan labari sai ya sa aka tara dukkan mutanen Sham in da ya yi huɗuba yana neman shawarar jama’a game da matakin da za a ɗauka, amma ba wanda ya ɗaga kansa sama ko yace uffan saboda biyayya. Daga bisani wani mutum da ake kira Zul kila’i ya kada baki yace masa, kai ne mai yanke hukunci, mu namu shi ne zartarwa. Manzon Ali ya garzaya ya faɗo masa abinda ya gani. Amma dai Ali bai karaya ya fasa abinda ya yi niyya ba.
Bayan da Mu’awiyah ya haƙiƙance Ali ya fito da rundunarsa sai shi kuma ya shirya tasa runduna mai irin yawan waccan, ya kuma fito domin karawa da su. Amru ɗan Ass ya kawo masa gudunmawa a daidai wani ruwan tafki da ake kira Siffin. A kan wannan ruwan ne ma aka ɗan samu gumuzu kafin hankali ya kwanta a soma tattaunawa tsakanin wakilan Ali da na Mu'awiyah, har a cimma yarjejeniyar yin amfani da ruwan tare da juna.
            Da yake Ali ya gano muhimmancin mutanen kufa a yaƙin da aka yi a baya, ya aika Manzo na musamman wanda shi ne Hashimu ɗan Utbata ɗan Abu waƙƙasi don ya sake nema masa goyon bayansu ta hanyar gwamnansu Abu Musa Al Ash'ari. Shi kuwa Abu Musa kamar yadda muka faɗa a baya, yana daga cikin masu ra'ayin farko na ganin bai cancanta ayi yaƙin ba. Wannan kuwa shi ya janyo Ali ya tuɓe shi daga kujerarsa, ya naɗa Ƙurazah ɗan Malik a madadinsa. Sannan ya sanya Ammar ya je ya janyo hankalin mutane don su ba da goyon baya. Ya kuma nemi ɗansa al Hassan da ya rufa masa baya, duk da yake shi ma ba mai ra'ayin yaƙin ne ba. Al Hassan kuwa ya yi ɗa'a ga mahaifinsa, amma ba inda yake cewa uffan, sai dai ya zauna saman mimbari, Ammar kuma ya gabatar da huɗuba a ƙasa da shi.
            Mutanen kufa kuwa sun amsa wannan kira na Sarkin Musulmi domin sama da mutane dubu goma sha biyu ne suka fita don mara masa baya.
            Ammar ya ci gaba da bayar da goyon bayansa ga Ali har ajalinsa ya cim masa a hannun ɗaya daga cikin mutanen Mu'awiyah. Babu shakka kuwa mutuwarsa ta kawo ruɗani mai yawa a tsakanin jama'ar Mu'awiyah. Domin kuwa da yawansu (musamman ma dai Sahabbai daga cikinsu) sun canza sheƙa daga wajen Mu'awiyah suka koma ɓangaren Ali saboda la'akari da wani sanannen hadisi a tsakaninsu wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake cewa, Ammar zai gamu da ajalinsa a hannun wata ƙungiya mai tsallake iyaka.
            Mu'awiyah daga nasa ɓangaren, ya yi riƙo da cewa, wannan ƙungiya jama'ar Ali ake nufi da ita, domin kuwa su suka fidda Ammar suka kai shi mahalaka.
            Abin da ya fi kome ban mamaki a wannan yaƙin shi ne, irin yadda abokan faɗa suka rinƙa hulɗa da junansu. Idan aka tsaya Sallah kowa yana iya shiga a ɗaya ɓangaren ya yi bukatarsa. A wuri ɗaya suke ɗibar ruwa (bayan an yi yarjejeniya a kan haka). In yamma ta yi aka tsaida buɗa wuta Ali ne yake yin Sallah a kan mamatan ɓangarorin gaba ɗaya. In aka kama fursuna ba'a kashe shi sai dai a ƙwace masa makami, in ya rantse ba zai ci gaba da yaƙi ba a sake shi, in ya ƙiya aci gaba da tsare shi. Haka kuma ba maganar ganima a wannan yaƙi. Wannan shi ya sa malamai suka ce ba'a taɓa irin wannan yaƙi ba kafinsa, suka gina hukunce hukuncen yaƙi da 'yan tawaye a kansa.

 Dakatar Da Buɗa Wuta
A lokacin da yaƙi ya yi zafi, duka ɓangarorin biyu sun sha wuya, kuma jama'a kamar ƙara ingiza su ga yaƙin ake yi, sai Mu'awiyah ya nemi a tsagaita wuta bisa ga shawarar na hannun damansa Amr ɗan Ass. Ali bai yi wata wata ba sai ya karɓi wannan tayin. Daman dai an gaji da wannan al'amari, kuma an ɗanɗani ɗacinsa har a maƙoshi. An dai cimma yarjejeniyar kafa kwamiti wanda za a ɗora masa alhakin fito da hanyar samun zaman lafiya da fita daga wannan kiki kaka da Musulmi suka samu kansu a cikinsa. Kuma Ali ya soma nadama akan shawararsa ta yaƙar waɗanda ya kira 'yan tawaye, domin ya lura babu wani alheri da zai auku a dalilin wannan yaƙi, gurinsa na tanƙwasa mutanen Sham da tilasta su yin mubaya'a ya zamo abu mai matsananciyar wuya, ga kuma jinainan Musulmi ana ta zubarwa.
Daga cikin abin da ke bayyana Ali ya soma nadama ya fara komawa ga ra'ayin waɗanda suka nuna masa kar ayi yaƙi shi ne, wakilta Abu Musa da ya yi a cikin kwamitin sulhu da aka kafa, mun kuma sani shi Abu Musa ra'ayinsa ke nan wanda a kansa Ali ya tuɓe shi daga muƙaminsa, Sannan ya ƙaurace ma yaƙin kuma ya rinƙa kiran mutane a kan kar su bai wa ko wane ɓangare goyon baya.
A nasa ɓangaren, Mu'awiyah ya wakilta Amru ɗan Ass a cikin wannan kwamiti na mutum biyu.[9]
An dai shata ranar aikin wannan kwamiti, wadda ita ce ranar 27 ga watan Ramadan 37 bayan hijira. An kuma sanya wurin haɗuwarsu, shi ne, Daumatul Jandal. Wanda ya ƙaddamar da wannan kwamiti a gaban jama'a shi ne, Ash'asu ɗan ƙais,  a madadin ɓangarorin masu jayayya da juna. Ash'as, wanda ke goyon bayan Ali, ya bai wa jama'a tabbacin za a yi aiki da duk hukuncin da wannan kwamiti ya zartas.
Riwayar Imamul Zuhuri ta nuna cewa, a wannan yaƙin basasa na Siffin an yi hasarar jama'ar da yawansu ya janyo aka rinƙa yi musu ramukan tarayya, ana haɗa kimanin mutum hamsin a ƙabari ɗaya.
Game da fursunonin da aka kama, Mu'awiyah ya fara sakin wani mutum ɗaya wanda ya neme shi alfarma a cikin wata ƙissa mai ban dariya. Domin kuwa wannan fursuna ya taso ne da mari (sarƙa) a ƙafarsa ya faɗi a gaban Mu'awiyah, sai ya ce, ka yi mini alfarma ka sake ni domin kai kawuna ne. Sai Mu'awiyah ya ce masa, to ya aka yi ni ban sanka ba? Sai ya ce, ai ni ɗa ne daga cikin ɗiyan ƙanwarka Ummu Habiba (Uwar Muminai), don haka kai kawuna ne, kuma kawun ko wane mumini.
Bayan ƙare yaƙin, Ali daga nasa ɓargaren ya saki dukkan fursunonin jama'ar Mu'awiyah da suka rage a wurinsa, abinda ya sanya Mu'awiyan shi ma  ya  saki fursunonin ɓangaren Ali. Da haka wutar yaƙin ta kwanta.
Yaƙin basasar Siffin dai ya gudana daga ranar Laraba zuwa jum'ah a farkon shekara ta Talatin da bakwai bayan hijira. Kuma an yi hasarar rayuka masu ɗinbin yawa daga ko wane ɓangare kamar yadda riwayoyi su ke nunawa.[10]
 Banbancin Ra'ayin Sahabbai Dangane Da Wannan Yaƙin
            Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun kasukashi uku dangane da wannan yaƙin.
            Kashi na farko su ne waɗanda su ke da ra'ayin cewa, yaƙin bai ma dace ba gaba ɗaya. Kuma kan al'umma ya wajaba ya haɗu a wuri ɗaya maimakon yaƙi a tsakanin junansu. Irin waɗannan bayin Allan sun yarda da khalifancin Ali kuma sun yi masa mubaya'a, amma dai yaƙin ne ba su aminta da aukuwarsa ba. Waɗannan su ne akasarin Sahabbai[11], a cikinsu har da Sa'adu ɗan Abu Waƙƙas, Muhammadu ɗan Maslamah, Abdullahi ɗan Umar bin khattabi, Abu Musa al Ash'ari (Gwamnan Kufa), Abu bakrata Al thaƙafi, Abu Mas'ud al Ansari da makamantansu. Hujjojin waɗannan bayin Allan suna da dama, kuma sun haɗa da duk hadissan da ke magana a kan barin yaƙi lokacin fitina. A cikinsu ma har da waɗanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi alƙawari da su cewa, duk halin da aka shiga kar su yi yaƙi da Musulmi.[12]
Kashi na biyu kuwa, suna ganin cewa, tun da yake Ali shi ne naɗaɗɗen Sarkin Musulmi, wanda ya wajaba a yi wa biyayya, wajibi ne a yaƙi dukkan wanda ya fanɗare masa. A kan haka suna yaƙi tare da shi a kan Mu'awiyah da jama'arsa. Suna kuma kafa hujja da dalillai na Alƙur'ani da hadisi masu nuna wajabcin biyayya ga shugabanni.
Daga cikin waɗanda suka ɗauki wannan matsayin har da fitattun Sahabbai irin su Abdullahi ɗan Abbas, Ash'as ɗan ƙais, Ammaru ɗan Yasir, Maliku ɗan Ka'abu al Hamdani da dai sauransu. Ga wata tattaunawa da ta gudana a tsakanin Ammaru da Abu Mas'ud al Ansari (daga cikin masu ra'ayin farko na ƙauracewa yaƙin) a kan wannan mabanbancin ra'ayin nasu, Buhari ya ruwaito ta kamar haka:
            Abu Mas'ud: Ya kai Ammar! Ka sani duk a cikin tsaranka babu wanda ya kai matsayinka a wurina. Kuma ba ka taɓa sanya kanka a cikin wani lamari ba wanda yake aibanta ka a wurina sai gaggawar da kake yi a cikin wannan fitina.
            Ammaru: Ya kai baban Mas'ud! Ni kuma wallahi ba ka da wani aibi a gurina kai da abokinka (Amr ɗan Ass) wanda yake aibata ku tun bayan rasuwar Manzon Allah kamar janye jikinku daga wannan lamari (yana nufin taimaka ma Ali).        
A yayin da kashi na uku na Sahabbai su ko su ke ganin cewa, Mu'awiyah ne yake da haƙƙen ya nemi fansar jinin ɗan uwansa khalifa Usman, kuma dole ne a taimaka masa don ya cimma biyan wannan buƙata. Suna kafa hujja da ayar Suratul Isra'i wadda Allah a cikinta yake cewa,

) وَمَنْ قُتِلَ مَظْلُومًا فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِ سُلْطَانًا فَلَا يُسْرِفْ فِي الْقَتْلِ إِنَّهُ كَانَ مَنْصُورًا (33)( سورة الإسراء: 33
Ma'ana:
Wanda duk aka kashe shi a kan zalunci to, haƙiƙa mun sanya hujja ga waliyyinsa (a kan ya nemi fansa), sai dai kar ya wuce iyaka a wajen kisan (ramuwa), domin lalle shi abin taimakawa ne.
Suratul Isra'i, Aya ta 33
Haka kuma suna kafa hujja da hadissan da suka bayyana cewa, fitina zata auku, kuma idan ta auku Usman shi yake a kan gaskiya tare da mutanensa. Sai suna ganin su ne mutanen Usman tun da su ke faɗa dominsa.
Daga cikin masu wannan ra'ayi akwai Sahabbai kamar Amru ɗan Ass, Ubadata ɗan Samitu, Abud Darda’i, Abu Umamata al Bahili, Amru ɗan Ambasata da dai sauransu.

 Ƙaddara Ta Riga Fata
            Muna iya lura daga abinda ya gabata cewa, duk yaƙe - yaƙen nan ba wanda aka yi shi don a tunɓuke Ali daga muƙaminsa, hasali ma a yaƙin Siffin shi ne ya kai hari, kuma ya fara yaƙin. A Jamal kuma ya iske fitina an riga an rura wutarta, sai aka jawo shi da ƙarfi da shi da su Ɗalhah a cikinta.
            Idan muka yi la'akari da hadisin da Ali ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, A yi bushara ga duk wanda ya kashe Zubairu da wuta, da hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma Ɗalhah bushara da zai yi shahada za mu gane cewa, suna da uzuri a yaƙinda ya shiga tsakaninsu da Ali. Domin kuwa dama ba shi suka zo yaƙa ba, cim masu ya yi suna faɗa da makasan Usman, ya zo ya kira su zuwa bin doka da mayar da al'amarin a hannun gwamnati don kada bangon Musulunci ya ida tsagewa, ana haka sai 'yan fitina suka tada yaƙi a tsakaninsu.
            Wannan ra'ayin da Ali ya yi tsayin daka a kansa na kar a kashe 'yan tawaye sai hankali ya kwanta ba shi da wani banbanci da ra'ayin shi wanda aka kashen, don kuwa Usmanu ai shi ya hana tun da farko a karkashe su, shi ma yana gudun irin abin da shi ne Ali ke gudu a yanzu.
            Shi ma Mu'awiyah a kan wannan batu ne su kayi yaƙi da Ali, shi yana ganin haƙƙinsa ne a ba shi makasan ɗan uwansa ya gama da su, ko a bar shi da su a gani. Shi kuma Ali na cewa, in kana son haka, ka amince da shugabancin da aka naɗa tukuna, sai ka kawo ƙara ga gwamnati ta duba ta yi magani. Mu'awiyah na nan a kan bakarsa, ni ba zan yi ma ka mubaya'ah ba in dai har ba za ka iya ɗaukar fansar wanda ya gabace ka ba, kuma ba za ka ba ni dama ni da ni ke da haƙƙe ba.[13]
            Ikon Allah, wai na kwance ya faɗi! To, ya za ka yi da wannan lamari? Idan ka diba kowa da hujjarsa, ko da yake hujjar Ali ta fi ƙarfi. To, amma yaƙin ba wani alfanu a cikinsa. Don haka ne ma waɗanda suka ɗauki matsayin ƙaurace ma yaƙin suka fi rinjaye ta fuskar samun madogara a Shari'ah, kuma shi ya sa Ali ya gwammace da ma ya bi ra'ayinsu har ma ya kan ce ma ɗansa al Hassan, kaicona da na bi shawararka! Ina ma na mutu tun shekaru ashirin da suka wuce![14]. Ganin haka ya sa al Hassan da ya karɓi mulki bayan mahaifinsa ya yi gaggawar samar da kwanciyar hankali ta hanyar sauka daga haƙƙensa wanda Musulmi suka zaɓe shi kamar yadda za mu gani a nan gaba. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yaba masa a kan wannan abin da zai yi tun ma bai yi shi ba.
            Laifin Mu'awiyah wanda mu ke fatar Allah ya yafe masa tare da sauran duk waɗanda abin ya shafa shi ne, rashin yin mubaya'ah a lokacin da ya cancanta, amma kuskure ne mu ɗauka cewa, yana neman khalifancin ne tun da farko.
            Sannan yana da kyau mu sani cewa, ko wannensu, Ali da Mu'awiyah sun ji zafin abinda ya faru daga baya. Ali ya kasance yana cewa, "kaicona da na mutu tun shekaru ashirin da suka gabata".[15] Shi kuma Mu'awiyah ya yi nadama a lokacin da ya je aikin Hajji, ya je ziyarar Madinah sai ya samu wasu Sahabbai waɗanda suka haɗa da Sa'adu ɗan Abu Waƙƙas da Abdullahi ɗan Umar da kuma Abdullahi ɗan Abbas. Anan ne Sa'ad ya ba shi labarin cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma Ali, "Kana tare da gaskiya, kuma gaskiya na tare da kai duk in da ka juya". Mu'awiyah ya zare masa ido yana mai barazanar cewa, sai ya kafa masa hujja a kan cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faɗi haka. Wannan ya sa suka tashi gaba ɗaya suka je wurin Nana Ummu Salamah wadda ta tabbatar masu da gaskiyar maganar. Anan ne fa Mu'awiyah ya bayyana nadamarsa yana cewa, Ya baban Ishaƙ! Ba abin zargi a kanka bayan ka ji wannan daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ƙin bin Ali da ka yi.[16] Ni kam da na ji wannan daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Wallahi da na yi hidimarsa har ƙarshen rayuwata.[17]

 Bango Ya Tsage A Rundunar Ali
            Ga dukkan alamu abin da Sayyiduna Ali ya kauce ma a lokacin da ya karɓi zaɓin yin sulhu na rabuwar kan Musulmi sai da ya auku. Domin kuwa dawowarsa daga wannan yaƙi ke da wuya sai ya lura da wata sabuwar ƙungiya ta fita daga cikin jama'arsa. Sun dai warware mubaya'arsu daga Ali har ma sun naɗa wani shugaba mai suna Shabas ɗan Rib'iyyu, sun kuma naɗa limamin da zai rinƙa ba su Sallah, shi ne, Abdullahi ɗan Kawa. Wannan ƙungiya ita ake kira Khawarij.
            Dalilin warewar Khawarij kuwa shi ne, a cewarsu, wai kafa kwamitin da aka yi kafirci ne. Saboda an sanya 'yan kwamiti a matsayin ɗagutu (masu yanke hukunci) koma bayan Allah, har ma suka kafa hujja da zancen Allah da yake cewa,

(إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ)
Ma'ana:
"Hukunci bai zamo ba face ga Allah".
                                    Suratul An'am: 57
            Wannan sabon ƙalubalen ya daɗa dagula lissafin Sarkin Musulmi Ali, ya kuma ƙara ɗauke hankalinsa daga ɗamarar da ya sha ta karya ƙarfin mutanen Sham. Amma kuma ya bi abin a hankali ta hanyar aikewa da saƙonni da manufar fahimtar da su. An kuma ci nasara a kan wani ɓangare nasu, amma har wayau an samu waɗanda suka cije, adadinsu ba zai kasa dubu huɗu ba (4000) a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi ɗan Wahbu wanda kuma aka sani da Rasibi. Daga ƙarshe ya zama tilas Ali ya yaƙe su.

 Tsugunne Ba Ta Ƙare Ba
            Da ranar haɗuwar kwamiti ta zo, jama'a sun hallara a wurin da aka shata don su shedi abin da wakillan nan biyu za su tattauna. Daga cikin waɗanda suka shedi wannan lamari daga ɓangaren Ali akwai: ƙaninsa Abdullahi ɗan Abbas da Ash'as ɗan ƙais da Abdullahi ɗan Ɗufail da Uƙbatu ɗan Ziyad da Hujru ɗan Yazid a cikin mutane da dama.
            Daga ɓangaren Mu'awiyah kuwa, an samu halartar ƙaninsa Utbah ɗan Abu Sufyan da Abul A'war al Sulami da Mukhariƙ ɗan Haris da Subai'u ɗan Yazid da Abdur Rahman ɗan Khalid ɗan Walid, su ma a cikin mutane da dama.
             Tattaunawar waɗannan 'yan kwamiti ba ta yi nisa ba sai da suka cimma matsaya cewa, wannan lamari yafi ƙarfin su yanke shi su kaɗai, don haka suka nemi a gayyato mutanen Shura, ana nufin waɗanda su Umar ya wakilta a lokacin rasuwarsa don su yi zaɓen shugaba.[18] To, amma anya kuwa za a cimma wata manufa ko da an kira su, bayan kunnowar kan da khawarij su kayi?
Tun a wannan lokaci dai Ali ya fahimci cewa, tsugunne fa ba ta ƙare ba, ga shi dai yanzu ana son a raba hankalinsa gida biyu. Daga nan ne ya yanke shawarar ƙyale mutanen Sham domin ya fuskanci haɗarin da ke gabansa na cikin gida daga ɓangaren khawarij. Su ma khawarij ɗin Ali ya yi masu jinkiri har sai sun bayyana wani abin da zai wajabta yaƙarsu a fili.
Ana cikin haka ne khawarij suka kashe wani Sahabi ana ce da shi Abdullahi ɗan khabbab tare da matarsa wadda suka soke cikinta suka fitar da ɗan da ke cikinta. Matakin farko da Ali ya ɗauka kuwa shine, ya aike masu wani ɗan saƙo da zai isar masu da gargaɗi, sai nan take suka kashe shi wannan ɗan saƙo.
Daga nan ne Ali ya shelanta yaƙarsu a madadin yaƙar Mu'awiyah, ya fatattake su har ya kasance ba waɗanda suka tsira sai kaɗan daga cikinsu.  
 Wani abin ban mamaki ga khawarij shi ne, yadda su kayi fice wajen kafirta Musulmi amma kuma suka fi kowa yawan ibada, kamar yawan salloli da azumi da karatun Alƙur'ani har ma ana yi masu suna Ƙurra'u (Makaranta ko Masu karatu). Ga su kuma da tsananin haƙuri a wajen karawa da abokan gaba. Dalillan da suka sa wasu daga cikin rundunar Ali suka ji tsoron yin arangama da su.
Amma wani abin sha'awa da yake nuna tsarkin zukatan Sahabbai shi ne cewa, duka ɓangarorin can guda uku da muka ambata a baya, a wannan karo sun goyi bayan Ali a kan wannan yaƙi. An samu da dama daga cikin kashin farko waɗanda mu ka ce sun ƙaurace ma yaƙar Mu'awiyah sun zo a wannan karon sun yaƙi Khawarij  a ƙarƙashin tutar Ali. Wataƙila wannan ba zai rasa nasaba da hadissai da shi Ali da kuma wasu Sahabbai suka ruwaito ba a kan yaƙar Khawarij da falalarsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana.[19] Hujjar da ba za a same ta a yaƙar Mu'awiyah da mutanen Sham ba domin shi wannan ijtihadi ne daga Sarkin Musulmi, ba umurni ne daga Annabi ba.

Ali Ya Yi Shahada
Waɗanda suka tsira daga yaƙin da muka ambata daga cikin Khawarij su ne suka zama ajalin Sarkin Musulmi Ali tun kafin babban kwamiti wanda ya haɗa mutane biyu na farko da muka ambata tare da mutanen shura su fara zama don gano bakin zaren wannan matsala. Khawarij dai sun shirya wata maƙarƙashiya wadda ke da nufin kawo ƙarshen Ali da Mu'awiyah da Amru ɗan Ass baki ɗaya, waɗanda su ne ɗagutai na wannan zamani a cewarsu. Sun kuma shata rana da lokacin da za su gudanar da wannan ɗanyen aiki. Ranar kuwa ita ce, ranar 17 ga Ramadan, shekara ta Arba’in bayan hijira a daidai lokacin da ko wanensu yake fitowa sallar asubahi.
Bisa ga haka ne, Abdul Rahman ɗan Muljam ya tasar ma Kufa, mazaunin Sayyiduna Ali. Al Barak ɗan Abdullahi shi kuma ya je Sham, mazaunin Mu'awiyah, a yayin da Amru ɗan Bakr al Tamimi zai tasar ma wajen Amru ɗan Ass. Da lokaci ya yi, ko wannensu ya zartas da abin da aka ɗora masa.
Shi dai Al Barak da ya je wajen Mu'awiyah, bai samu sa'arsa ba, saboda an ɗago shi tun bai kammala mugun aikin ba. Sai dai ya ji ma Mu'awiyah rauni a cinya, wadda ya yi kwanukka yana jinyarta. A kan wannan dalili Mu'awiyah ya nemi matsara a karon farko a tarihin sarakunan Musulunci. Shi ma dai Amru kwanansa suna gaba, domin a ranar da aka shirya yin wannan ta'asa an yi dace ba shi da lafiya. To, da yake cikin duhun asubahi ne, ɗan saƙon khawarij sai ya kashe limamin da ya bayar da Sallah a rannan zaton cewa, gwamnan ne da kansa. Don haka Na'ibi wanda kuma shi ne kwamandan 'yan sanda, kharijah ɗan Huzafa sai ya yi shahada a madadin mai gidansa. Amma a kufa, an zartar da wannan aika aika kamar yadda khawarij suka tsara ta, domin ɗan Muljam ya kai hari ga Sarkin Musulmi Ali a kan hanyarsa ta zuwa Masallaci, ya kuma same shi ta inda yake buƙata. Da wannan ne khalifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na huɗu ya samu shahada kamar yadda magabatansa guda biyu (Umar da Usman) suka samu, ya kuma huta da waɗannan fitinu da suka dabaibaye mulkinsa na tsawon shekaru huɗu.
An bayyana cewa, Mu’awiyah ya nuna damuwa ainun akan kisan Ali, har sai da matarsa tace masa, ba kai ne jiya ka gama yaƙarsa ba? Ya ce mata, kin san irin mutumin da aka yi hasara kuwa?[20]
Ali ya yi shahada a ranar 17 ga Ramadan 40 bayan hijira. Don haka mulkinsa ya kasance shekaru uku da wata tara. Ya kuma bar zuri'a mai yawa wadda ta haɗa da 'ya'ya maza 14 da ‘ya’ya mata 17. Da yawansu sun yi shahada a karbala tare da wansu Hussaini kamar yadda za mu gani a nan gaba. Waɗanda suka bar zuri'a daga cikinsu sun haɗa da Hassan da Hussaini (ta wajen ɗansa Abubakar Zainul Abidin) da Muhammad (wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah) da kuma Abbas da Umar.[21]
  

[1]  A Madina ba a yin gwamna na din din din a wannan lokaci, saboda Khalifa shi yake riƙe da ita kamar yadda yake a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma duk lokacin da Khalifa zai fita daga Madina saboda wani dalili to, ya kan naɗa ma ta gwamna wanda aikinsa zai ƙare da zaran Khalifa ya dawo. Da Allah zai ƙaddara wafatinsa kuwa to, da gwamnan Madina shi zai yi riƙon ƙwarya kafin al'umma ta tsai da sabon shugaba. Don haka matsayin gwamnan Madina a lokacin ya kai ace masa mataimakin sarkin musulmi.
[2]  Dalilin wannan magana shi ne, Abdullahi ɗan Umar ya shiga wurin babansa bayan da ya kafa wancan kwamiti, sai shi Khalifa ɗin ya ce masa, in da mutane za su zaɓi mai sanƙon can tabbas ya ɗora su a kan hanya. Sai ɗan nasa ya ce masa, to, me zai hana ka ayyana shi? Sai ya ce, a'a, ba zan ɗauke ta a raye ba kuma in ɗauke ta bayan na mutu.
[3]  Wannan yana ƙara nuna maka cewa, waɗannan ja'irai ba Usman su ke nufi da yaƙi ba, domin kuwa duk wanda ya shirya juyin mulki za ka tarar yana da wani tsayayyen ɗan takara da zai kafa. To, su kam ba su da kowa. Gurinsu dai shi ne fitina, kuma duk yadda ta kaya sun aminta.
[4]  Sham a wancan lokaci ta haɗa ƙasar Siriya ta yau, da Lebanon da Jordan da kuma Falasɗinu.
[5]  Duba Imam Ali, na Rashid Ridha, bugun Darul Kutub Al Ilmiyyah, 2001, shafi na 74. Kar dai mu manta cewa, Zubairu fa shi ne ya janye haƙƙensa ya bar wa Ali a lokacin da suka yi takara bayan rasuwar Umar. Ko bayan mutuwar Usman ma Zubairu yana cikin waɗanda aka nema don a naɗa shi amma ya kauce. Saboda haka kada wani ya yi tunanin Zubairu yana da wata jayayya ne ga karɓar ragamar mulki da Ali ya yi. Banbancin ra'ayinsu anan shi ne na lokacin tunkarar 'yan ta'adda. Kuma Zubairu da ire irensa su na ganin ra'ayin Ali ya yi sassaucin da ba za su iya ɗauka ba. Don haka suka yi gabansu da ɗaukar matakin da suka ga ya dace. Babu shakka kuwa sun yi kuskure a wannan mataki, amma Allah zai ba su ladar ijtihadinsu na ganin sun aza al'umma ga abin dasuka ƙudurta shi ne daidai kamar yadda Allah zai ba Ali ladar nasa ijtihadin na yaƙar waɗanda suka ƙi yi masa mubaya'a tare da cewa da ya barsu, ya yafe sashen haƙƙensa da wannan ya fi zama alfanu ga Musulunci da Musulmi.
[6] Wannan ingantacciyar magana ce duk da ya ke Malam Ibnul Arabi ya yi suka a kan ta a cikin littafinsa Al Awasim Minal Ƙawasim. Don tabbatar da ingancinta ka duba Al Musnad  na Imam Ahmad (6/52) da Al Mustadrak na Hakim (3/120) da Fathul Bari na Ibnu Hajar (13/45) da kuma Silsilatul Ahadis As Sahiha na Albani (1/473). Amma shi Malam Ibnul Arabi ya damu ne da riwayar maƙaryata wadda ta ce, Ɗalha da Zubairu sun yi mata shedar ƙarya suka ce wannan wurin ba shi ne Hau'ab ba, don haka sai ya raunana labarin gaba ɗaya.
[7]  Wannan dai shi ne hukuncin Allah. Domin kuwa a Makka ma an koro sabon gwamnan da Ali ya tura, shi ne, Khalidu ɗan Ass. Amma sababbin gwamnonin da  ya tura a Yaman (Ƙaninsa Ubaidullahi ɗan Abbas) da Masar (Ƙais ɗan Sa'ad) ba su gamu da wata tsangwama ba. A Makka ɗin ma dai daga baya ya naɗa ƙaninsa Ƙusamu ɗan Abbas, kuma ya samu karɓuwa.
[8] Usdul Gaba, na Ibnul Asir (3/88-89)
[9]  Yana da kyau mu san matsayin waɗannan Sahabban guda biyu. Shi dai Abu Musa daɗaɗɗen ma'aikaci ne kuma gogaggen ɗan siyasa (idan za mu iya kiran sa haka, domin siyasa tana nufin mulki). Ya yi gwamna a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har sau biyu, a garuruwan Zubaid da Adan. Duk a tsawon mulkin Umar kuma shi ne gwamnansa na Basra, daga baya ya samu canjin aiki zuwa Kufa a zamanin Usman. Ali bai cire shi daga muƙaminsa ba da farko sai bayan da al'amurra suka rikice. Haka kuma yana cikin waɗanda suka hardace Alƙur'ani tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sa'annan ƙwararren masanin Shari'a  ne wanda har an ƙirga shi daga cikin masanan Shari'a guda shida waɗanda ke fatawa a Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tun a zamaninsa. A lokacin mulkin Ali kuma an shedi cewa, ba wanda ya kai ilminsa in ban da Ali. Shi kuma Amr ɗan Ass shi ne wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yaba da cewa, mutane sun musulunta, amma Amru ya yi imani (yana nuni ga ƙarfin addininsa). A lokacin da ya musulunta da kansa ne ya yi hijira zuwa Madina bayan sulhin Hudaibiyah, a lokacin al'amarin Musulunci bai yi ƙarfi ba. Saboda kaifin basirarsa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya taɓa sa ya yi hukunci a tsakanin wasu mutane, in da har ya ce, in yi hukunci a gabanka Manzon Allah? Ya ce, eh. Ka yi, shi mai hukunci idan ya yi hukunci ya yi daidai yana da lada biyu, idan ya yi kuskure yana da lada ɗaya. (Duba wannan ƙissar a cikin Sahihul Bukhari, Kitabul I'tisam 8/157). Shi ma dai Amru ɗan Ass ya fara riƙa muƙami ne a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sa'adda ya jagorantar da shi ga yaƙin da aka sani da suna Dhatus Salasil.
[10]  Sai dai wasu riwayoyin sun wuce hankali. Domin kuwa yaƙin gaba ɗayansa bai wuce kwana uku ba, ana tsayawa a yi Sallah, kuma ba a yi da dare. Idan aka tara sa'oin yaƙin ba za su wuce awa 30 ba. Amma sai ga wasu riwayoyi na cewa, an kashe sama da mutum 70,000. Ko a Ƙadisiyyah kuwa mutum 8,500 ne a ka kashe, kuma duk masana tarihi sun haɗu a kan cewa, yaƙin Siffin bai yi zafin na ƙadisiyyah ba. Haka dai ma su ƙarin gishiri a labari su ke yi a ko wane lokaci. Duba littafin Asmal Maɗalib Fi Sirati Amiril Mumina Ali bin Abi ɗalib, na Dr. Ali Muhammad al Silabi, (2/653-654).
[11]  Al Hassan ɗan Abil Hassan al Basri – ɗaya daga cikin manyan tabi'ai da suka yi zamani da Sahabbai - ya ce, a lokacin da fitina ta auku Sahabbai da su ke raye yawansu ya kai dubu goma, amma ba ka samun talatin daga cikinsu a waɗannan fitinu. Imamu Ahmad ya ruwaito wannan a Musnad. Ibnu Taimiyyah ya ce isnadin wannan magana na daga mafi ingancin isnadi da ake riwaya da shi a bisa doron ƙasa. Duba Minhajus Sunnah nasa (3/186).
[12]  Duba Sahih al Bukhari, kitabul Fitan, (8/95) da Sunan al Tirmidhi, kitabul Fitan, (3/332) da kuma Musnad Ahmad (4/225).
[13] Muƙaddima, na Ibnu Khuldun, (1/257).
[14]  Duba Usdul Gabah (6/209)
[15] Minhajus Sunnah, na Ibnu Taimyyah (6/209) da Usdul Gabah (6/209)
[16] Sa'adu bai bi Ali ba don yana ganin ko Ali na da haƙƙi barin haƙƙin yafi zama alheri. Ali kuma daga baya ya yaba ma matsayin Sa’adu da Abdullahi ɗan Umar na rashin shiga wannan yaƙi kamar yadda yazo a Fathul Bari na Ibnu Hajar (12/67).
[17] Duba Tarikhu Dimashƙ na Ibnu Asakir, (22/246). Wannan Hadisin kuwa yana cikin littafin Al Mustadrak na Hakim, (3/119) kuma ya inganta shi.
[18]  To, amma fa ba ana nufin su sauke Ali su zaɓi wani shugaba ba, domin Ali shugaba ne zaɓaɓɓe wanda dukkansu 'yar majalisar shurar sun yi masa mubaya'a a Madina. Ba akan shugabancinsa ake jayayya ba, a kan haƙƙensa na mubaya'a da haƙƙen Mu'awiyah na ɗaukar fansa, yaya za a yi a sasanta? Maganar cewa wai, 'yan kwamiti sun zartas da a cire Ali, ko kuma Amru ya yaudari Abu Musa na daga cikin batutuwa marasa tushe waɗanda wasu maƙaryata da ba su san girman waɗannan mutanen ba suka ruwaito.
[19]  Ka duba hadissan falalar yaƙar khawarij a cikin Sahihul Bukhari, Kitabul Fitan, Babu Ƙatlil Khawarij.
[20] Al Bidayah Wan Nihayah na Ibnu Kathir, (8/14, 130).
[21] Duba Itti'adhul Hunafa Bi Akhbaril A'immatil Faɗimiyyin Al Khulafa, na Maƙrizi, juz'i na ɗaya, za ka same shi a duniyar gizo a kan wannan layin: http://www.alwarraƙ.com.


DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO