GABATARWA
A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!
WWW.MUMBARINMALAMAI.BLOGSPOT.COM
WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA TARIHIN MUSULUNCI DA TARIHIN MALAMAN SUNNAH MAGABATA DAMA MALAMAM MU NA YANZU ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!
DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{mumbarinmalamai@gmail.com]
Wednesday, 28 September 2011
INGANTACCEN TARIHIN SAYYADI RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WA ALA ALIHI WASALLAM (DARASI NA DAYA 1)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Gabatarwa
Muhimmancin Wannan Tarihi
Tarihin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya banbanta da sauran tarihohi irin na manyan mutane da jagorori da ake karantawa.
1. Da farko dai karanta wannan tarihi ibada ne.
2. Madubi ne na rayuwar da Allah Tabaraka Wa Ta'ala yake son mu kwaikwayi irin ta.
3. Babu wata hanyar da take tabbatar mana da gaskiyar wannan taliki da aka aiko mana kamar karanta tarihin rayuwarsa.
4. Babu kuma wata hanya da za ta dawwamar da so da kaunarmu a gare shi sama da nazarin rayuwarsa mai albarka wadda take cike da ababen girma da wani dan adam bai da irin su.
5. Sanin wannan tarihi mai albarka na taimaka mana wajen sanin makamar ayoyi da yawa da hadisai a cikin tarihin fiyayyen halitta ta hanyar sanin dalilin saukar aya ko munasabar da ta sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya fadi hadisi, wanda zai taimaka matuka wajen gane hakikanin ma'anar nassi.
6. A cikin wannan tarihi ne zamu ga irin gudunmawar da sahabban manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam suka ba shi da taimakonsa da suka yi wajen isar da sakon musulunci. Allah Tabaraka Wa Ta'ala da kansa ya fadi cewa, da su ne ya karfafe shi har ya samu nasarar kafuwar addini (Suratul Anfal: 62 da Suratut Taybah: 88).
7. Kamar yadda a cikin sa ne zamu ga irin tarbiyyar da manzon Allah ya yi masu bisa ga umurnin da maxaukakin sarki ya ba shi a Suratu Ali Imran: 164 da Suratul Jum'ah: 2.
Kaicon mutanen da suka yanke alakarsu da wadannan bayin Allah wadanda manzon Allah ya tarbiyyantar da su domin mu koyi tarbiyyarsa daga wurin su. Mutanen da tarbiyyar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ta kama jininsu da tsokarsu har ta kai suka sayi aljannar Allah da ayyukansu. Kamar yadda Allah ya ce:
((إن الله اشترى من المؤمنين أنفسهم وأموالهم..))
(Suratut Taubah: 111)
((لكن الرسول والذين آمنوا..))
(Suratut Taubah: 88-89)
Kuma Allah ya shelanta ya yarda da su (Suratut Taubah: 100, Suratul Ma'ida: 6, Suratul Fathi: 18 da kuma Suratul Mujadila: 22)
Su ne kuma Allah ya ba da shedar abinda ke cikin zukatansu na gaskiya da imani (Suratul Anfal: 63, Suratul Fathi: 18-19).
Kuma Allah ya bayyana matsayinsu ya banbanta da na sauran musulmi duka wadanda ba su ba (Suratul Hujurat: 7).
Wai shin akwai wata daraja da kai ta su bayan Allah Tabaraka Wa Ta'ala ya ce ya lizimta masu "Kalimatut Taqwa" (Ita ce kalmar shahada) ya ce kuma sun fi kowa cancantar ta da zama ma'abotanta?! (Suratul Fathi: 26).
8. Babu shakka sanin tarihin gwagwarmaya da fadi-tashin kafa addinin musulunci da aka yi tun zamanin farko yana haskaka mana tafarkin da ya kamata mu bi wajen tsayar da addinin Allah. Da yawa a yau akwai masu tunanin hanyar gyara ita ce, mu kafa gwamnatin musulunci sannan sai mu sa - da karfi - gwamnatin ta gyara mutane. Sai mu ce ma su a koma ga tafarkin Sirah, mu ga yadda shugaban tafiya (SAWW) ya yi. Haka lamarin yake ga abubuwa da dama da suka shafi siyasarmu ta da'awa da malanta da makamantansu.
9. Kamar yadda masu kira zuwa ga musulunci ke samun miqaqqen tafarki a cikin wannan tarihi haka su ma masu tafiyar da mulki da jagororin al'umma da masu fatauci da yan qwadago da qungiyoyin sa kai.. Da maza da mata da manya da qanana.. Kai, da ma kowa da kowa.
10. Duk wata matsala da zaka shiga a rayuwarka idan ka karanta tarihin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam za ka tarar da wata mai kama da ita da hanya mafi sauqi ta warware ta. Misali, maraici, talauci, arziki, mulki, matsalolin aure, na tarbiyyar 'ya'ya, qalubalen siyasa da fuskantar 'yan adawa dss.
Haqiqa, duk musulmin da bai san tarihin manzonsa ba zuwan sa a duniya ya zama kamar zuwan zomo a kasuwa.
MATSAYIN WANNAN TARIHI
Allah Tabaraka Wa Ta'ala ya fifita tarihin ma'aikinsa a kan na sauran 'yan adam da duniya take ji da su.
1. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam shi kadai ne wanda aka haifa a cikin hasken rana, kamar yadda wani bature yake cewa. Abin nufi, babu wani abin da zaka so ka sani game da rayuwarsa wanda ma'abotansa ba su sanar da mu ba. Tun daga rayuwarsa ta cikin gida har zamantakewarsa da masoyansa da magabta. Kai, har abinda mutane ke boyewa na sirrin rayuwarsu, shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam an bayyana nasa domin shi abin koyi ne ga musulmi fai da boye.
Dubi yadda aka sifaita mana jikinsa kamar kana zaune a gabansa. Hatta da farin gashin da yake a gemunsa an qirge mana yawansa. Motsinsa kowane iri an bayyana shi a cikin tarihinsa. Tun daga yadda yake zama da tafiya da cin abinci da sa sutura da kawaici da magana da komai da komai. Dubi "As-Shama'il Al-Muhammadiyyah" na Imam Abu Isa At-Tirmidhi ko kuma "Zad Al-Ma'ad" na Ibnul Qayyim misali ba abin da ba zaka gani ba wanda ya danganci nasa salo na rayuwa wanda shi ne samfurin rayuwar da Allah yake so bani Adama su koya. Tambayi mabiyan annabi Isah (AS) me suka sani game da rayuwarsa? Ballantana duk sauran addinai irin na gargajiya da makamantansu!
2. Sai kuma ingancin da kaffatanin wannan tarihi yake da shi. Saboda babu na-ji-na-ji a cikinsa. Kome aka fada an san wanda ya cirato shi kuma ta ina ya cirato shi. Don haka in ka ga ana rigima kan wata magana da ta danganci rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam to, ma'abota sani ne ba su zo ba. Yanzu suna fayyace maka kowace ruwaya da matsayinta.
3. Ga shi kuma wannan tarihi ya cika ya batse ta kowace fuska. Rayuwar kowa akwai a cikinsa. Karamin yaro, maraya, matashi, dattijo, maigida, talaka, malami, mai sarauta, dan kasuwa, jagora, soja, farar hula, liman.. Kai har da dan gudun hijira bai rasa abin koyi a cikin wannan tsarkakakken tarihi.
4. Tsaftataccen tarihi ne da ba abin yasuwa a cikin sa. Ko sau daya ba zaka ji wani sharri ko zalunci ko duk wani abinda lafiyayyen hankali yake kyama ba a cikin sa. Rayuwa ce ta wanda Allah ya aiko shi don ya zama rahama ga talikai. Dubi duk kaifin adawar mutanen Makka, kai har da algungumai Yahudawan da suka yi makwautaka da shi a Madina. Ka taba jin wanda ya tuhumce shi da wata magana ko aiki mai zubar da mutunci?
5. Tare da haka kuma wannan rayuwa ce mai saukin koyi. Ba ta wuce iya ikon dan adam da aka halicce shi a kai ba. In ban da mu'ujizoji - kamar Isra'i da Mi'iraji - mene ne dan adam ba zai iya kwaikwayon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba a cikin sa? BY Dr. MANSUR SOKOTO…………………ZAMUCI GABA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment