Al Hassan Ɗan Ali Raliyallahu
Anhu
5.1 Sunansa Da Asalinsa
Sunansa Al
Hassan ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib.
Mahaifiyarsa ita ce Faɗimah ɗiyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Ana yi masa kinaya da Abu Muhammad.
An
haife shi a tsakiyar watan azumin shekara ta uku bayan hijrah, kuma Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne da kansa ya sanya masa suna, ya
kuma yanka masa rago.[1]
Al
Hassan ɗaya ne daga cikin mutanen da su
kayi kama da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a siffar jikinsu.
An bayyana cewa, kamannunsa da Mnazo Sallallahu Alaihi Wasallama sun fi
yawa a saman jikinsa, a yayin da shi kuma Hussaini ya fi kama da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama a ƙasansa.
Duk da ƙarancin shekarun Al Hassan a zamanin kakansa, amma
yana tuna kaɗan daga abubuwan
da suka auku a wannan lokaci. Abul Haura'i ya tambaye shi, me kake tunawa a
zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Sai ya ce, na ɗauki wani ɗan dabino daga
dukiyar sadaka, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cire shi
daga bakina da sauran yawuna a kansa ya mayar da shi a inda na ɗauko shi.[2]
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya kasance ya na son 'yan tagwayen nan[3]
na 'yarsa, so wanda ba ya ɓoyuwa. Ya kan
kuma yi musu addu'a ya ce, "Ya Allah! Haƙiƙa ina son su, Ya Allah! kai ma ka so su".
Wannan kuwa ya sa masu kwarjini sosai da ƙauna a wurin
Sahabbai waɗanda ƙaunar Manzon Allah ta sa suna son duk abin da ya ke ƙauna.
5.2 Siffarsa
An
siffanta Al Hassan da cewa, kyakkyawa ne, mai kwarjini da fara'a da son jama'a
da kyauta da yawan Ibada.
Daga
cikin ƙoƙarinsa
a Ibada ya yi hajji har sau goma sha biyar, a mafi yawansu ya kan tafi da ƙafafunsa, a lokacin da ake janye da raƙumansa. Haka kuma an ruwaito cewa, sau uku Al Hassan
ya na kasa dukiyarsa kashi biyu ya yi sadaka da kashi ɗaya, kuma a kullum ya kan karanta Suratul Kahf kafin ya yi bacci.
Daga cikin karimcinsa da yawan
sadakarsa an ba da labarin ya ji wani
bawan Allah ya na addu'a ya na roƙon Allah ya ba
shi Dirhami dubu goma, nan take Al Hassan ya koma gida ya aika masa da waɗannan kuɗi.
Al Hassan kuma mutum ne mai yawan
aure, yawan matan da ya aura kuwa sun kai 90. A ko da yaushe ya na tare da
macce huɗu, idan ya saki nan take zai sake
aure. Mutane kuma na son haɗa zuri'a da shi don sharifantakarsa.[4]
Daga cikin matan da ya aura
akwai Ummu Ishaƙ ɗiyar Ɗalhah wadda ta haifa masa Ɗalhah. Bayan mutuwarsa sai ƙaninsa Hussaini ya aure ta, shi kuma ta haifa masa
Faɗimah.
5.3 Darajojinsa
Al Hassan ya yi
tarayya da ɗan uwansa Al
Hussaini wajen kasancewarsu shugabannin matasan aljanna.[5]
Al
Hassan ya keɓanta da wata
babbar martaba wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bada
bushara da ita, cewa, shi shugaba ne wanda zai kawo ƙarshen wata tarzoma wadda zata gudana a tsakanin
manyan ƙungiyoyi biyu na Musulmi kamar
yadda za mu gani a nan gaba.[6]
5.4 Al Hassan Ya Gadi Mahaifinsa
Al
Hassan na daga cikin waɗanda suka bai wa
Ali shawarar kada ya fita daga Madina. Tare da kuma ya tsani yaƙin da aka yi, amma ya yi ɗa'a ga mahaifinsa wajen fita tare da shi. Daga
bisani da al'amurra suka dagule Ali ya rinƙa ce masa
"Kaicona da na bi shawararka".
A
lokacin wafatin Ali akwai a cikin Sahabbai waɗanda
su ke gaba da Al Hassan kamar Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas da Sa'id ɗan Zaid waɗanda ke cikin mutane goma da suka samu busharar
aljanna daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sa'ad kam ma ai
ya yi takara da Ali kamar yadda mu ka gani a ƙarshen
khalifancin Umar. Ga zahiri shi ma Sa'id ya cancanta, sayyiduna Umar ya ƙi sanya shi ne a cikin kwamitin saboda dangantakarsu
domin ƙaninsa ne ta wajen mahaifinsa
kuma shi yake aure da ƙanwarsa wadda mu
ka ba da labarin ita ce dalilin musuluntarsa.
Ban
da waɗannan akwai tsararrakin Al Hassan kamar
su Abdullahi ɗan Umar da
Abdullahi ɗan Abbas (ƙanin Ali ta wajen mahaifinsa) da kuma Abdullahi ɗan Zubair (Jikan Sayyiduna Abubakar ta wajen
mahaifiyarsa).
Al
Hassan ya nuna rashin sha'awarsa ga wannan al'amari bayan da ya ga irin wahalar
da mahaifinsa ya sha akai. Ga shi kuma ya yi la'akari da irin yanayin magoya
bayan ubansa, wato mutanen Iraƙi waɗanda ba su da biyayya ko kaɗan. To, amma kuma ya zama tilas Al Hassan ya karɓi mubaya'a bayan da jagororin rundunar Ali suka nace
a kan haka.
5.5
Ramin Shuka Ba Zurfi Sai Tarin Albarka
Kafin ya miƙa hannunsa ayi
masa mubaya'a sai da Al Hassan ya sharɗanta ma su su yaƙi duk wanda ya yaƙa, wanda kuma ya
sulhunta da shi su amince a kan sulhun.
Wannan sharaɗi da al Hassan ya sanya ya kashe ma mayaƙa jiki ƙwarai har suka
rinƙa tsegumi a kansa. Suna cewa, Al Hassan
ba zai kammala aikin babansa ba na yaƙar mutanen Sham.
Ana haka ne wasu daga rundunar
sojinsa suka kai masa hari da wuƙa da nufin kashe
shi a lokacin da aka samu raɗe raɗin cewa, an kashe Ƙaisu
ɗan Sa'ad, ɗaya
daga cikin kwamandodinsa, magoya bayan Ƙaisu su kayi ma
Al Hassan a ture a cikin hemarsa har ya samu rauni a cinya, suna tuhumarsa da
cewa shi ya sa aka kashe shi, alhali kuwa maganar tun asalinta jita - jita ce
kawai.
Allah dai ya kuɓutar da Al Hassan daga mutuwa a wannan hari da aka
kai masa. Bayan wasu 'yan watanni sai ya mirmije daga raunin da ya samu. Wannan
ya ƙara sanya ƙyamar
mutanen Iraƙi a gare shi da
ma khalifancin baki ɗaya.
Bayan da ya samu sauƙi Al Hassan ya yi wata huɗuba mai gauni a kan mimbari wadda a cikinta yake
zargin mutanen Iraƙi da rashin
ladabi, yana kuma faɗakar da su game
da matsayinsu (Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan
huɗubar ta sanya mutane da yawa a
Masallacin Kufa yin kuka.
A daidai wannan lokaci da mu ke
magana a kansa, Mu'awiyah na can a cikin jama'arsa, mutanen Sham, waɗanda suka shahara da cikakkiyar biyayya a gare shi.
Sun kuma yi masa Mubaya'a a matsayin khalifa tun bayan wafatin Ali. Idan faɗansu da Ali ba mai dalili ba ne ta fuskar jayayya a
kan shugabancinsa, a yanzu faɗa mai cikakken
dalili zai fara tun da ya ke an samu sarakuna biyu masu amsa suna iri ɗaya.
Mutanen Iraƙi kuwa ba su gushe ba suna ingiza Al Hassan har sai
da ya yi shiri da nufin yaƙar Mu'awiyah
kamar yadda mahaifinsa ya yi. Ya tsara runduna ta mutane 40,000 (dubu arba'in),
ya soma da aika gungun farko waɗanda aka kira
"Rundunar Alhamis" a ƙarƙashin jagorancin wani jarumi da ake ce ma Ƙaisu ɗan Sa'adu ɗan Ubadah. Adadin wannan runduna ya kai mutum 12,000
(dubu goma sha biyu). Sun kuma tasar ma birnin Sham in da suka yada zango a
wani wuri da ake kira Maskan.
A nasa ɓangaren, rahotanni sun zo ma Mu'awiyah game da
fitowar rundunar Iraƙi. Saboda haka
sai ya fito da kansa don ya tarbe su, ya yi nasa sansani a wurin wata gada da
ake kira Mambij.
5.6 Zama Lafiya
Yafi Zama Ɗan Sarki
Al Hassan dai
tun da farko mun faɗi ba ya son
wannan arangama wadda ta ci ƙarfin Musulmi,
ta hana su kwanciyar hankali ballantana ci gaba da yaɗa addini. Shi kuma Mu'awiyah da ya haɗu da "Rundunar Alhamis" sai hankalinsa ya
tashi. Na hannun damansa, Amru ɗan Ass ya ce
masa, wannan runduna ba zata watse ba sai sun kashe irinsu a cikin jama'armu.
Mu'awiyah ya ce, to, idan ko haka ta faru yaya za ayi da yawan zawarawa da
marayu? Wane shugaba zai ji daɗin mulki a irin
wannan yanayi? Daga ƙarshe sai su
kayi shawarar aika waƙilai zuwa wurin
Al Hassan don neman sasantawa.
Wakilan
da Mu'awiyah ya tura su ne, Abdullahi ɗan Amiru ɗan Kuraiz da kuma Abdur Rahman ɗan Samurah. Sun kuma tarar da Al Hassan sun tattauna
da shi inda ya bayyana ma su ƙudurinsa na
sauka daga khalifanci ya danƙa ragwamarsa ga
Mu'awiyah bisa ga sharuɗɗan da za su
sanya don neman a zauna lafiya, al'ummar Musulmi taci gaba. To, amma fa Al
Hassan ya gamu da cijewa ta wajen kwamandan "Rundunar Alhamis" Ƙaisu ɗan Sa'ad wanda
bai goyi bayan haka ba, kuma ya keɓe kansa da
rundunarsa don ƙalubalantar
wannan sulhu.
5.7 Ja Da Baya Ba Tsoro Ba
Al Hassan dai ya
dage a kan wannan manufar tasa wadda ta tabbatar masa da faɗin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
cewa, "Wannan jikan nawa shugaba
ne. Kuma Allah zai sasanta waɗansu manyan
rundunoni biyu daga cikin Musulmi a dalilinsa"[7]
A
ranar da zai miƙa mulkin ga
Mu'awiyah, Al Hassan ya yi wata huɗuba wadda ta nuna
kaifin basirarsa da tausayinsa ga wannan al'umma, in da ya bayyana masu
dalilansa na son zaman lafiya domin zama lafiya ya zama ɗan sarki, kai ya ma fi zama sarkin. A cikin wannan
huɗubar har wayau yana cewa:
...Ku sani wanda
ya fi kowa dabara shi ne wanda ya ji tsoron Allah.
Wanda ya fi kowa
wauta kuwa shi ne wanda ya kangare (daga ɗa’ar Allah).
Ya ku mutane!
Tun farkon wannan al'amari (yana nufin yaƙi) ni ne na fi
ku ƙyamarsa, a yanzu kuma ni ne na kawo
gyara a cikinsa.
Zan mayar da haƙƙi ga ma'abocinsa, ko kuma in haƙura da haƙƙena don maslahar
al ummar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Ya kai
Mu'awiyah! ka sani wannan al'amari Allah ya ɗora ma ka shi
don wani alheri da yake tare da kai ko kuma don sharrin da ya sani a wurinka.
Sannan ya karanta
wannan ayar:
﴿ وَإِنْ أَدْرِي لَعَلَّهُ فِتْنَةٌ لَكُمْ وَمَتَاعٌ إِلَى
حِينٍ ﴾ [سورة الأنبياء:111].
Ma'ana:
Kuma ni ban sani
ba, wataƙila fitina ne a gare ku da ɗan jin daɗi zuwa wani
lokaci. Suratul Anbiya', Aya ta 11.
Al
Hassan dai ya yi amfani da sharaɗin da ya sanya
ma mutanen Iraƙi wanda a
dalilinsa ya zame masu tilas su karɓi wannan sulhu.
Allah kuma a cikin rahamarsa sai ya karkato da zuciyar Ƙaisu ɗan Sa'ad da
rundunarsa bayan cijewar da su kayi. Al Hassan ya samu shawo kan Ƙaisu daga baya kuma har ya kawo shi da kansa a wurin
Mu'awiyah. Ƙaisu duk da haka
sai da ya laƙe hannunsa can
ga cikinsa a maimakon ya miƙa shi ya yi
mubaya'a ga sabon khalifa. Amma dai Mu'awiyah ya daure ya kai nasa hannun can
su kayi musafaha, hujja ta tabbata a kan Ƙaisu ke nan don
ya yi mubaya'a.
Wannan
shekarar ta zame ma musulmi watan bakwai maƙarar rani. Domin
kuwa kusan dukkan Musulmi sun haɗu a kan jagora ɗaya in ban da ƙungiyar
Khawarij. Akan haka ne aka raɗa mata suna Amul
Jama'ah wato, shekarar haɗin kai.
5.8 Kyakkyawar Sakayya Ga Al Hassan
Da yake wanda duk ya bar wani abu
saboda Allah to, Allah zai musanya masa ya ba shi wanda ya fi shi ko ya bai wa
zuri'arsa, wannan karimci na Al Hassan zai gamu da sakayya ta Ubangiji can a ƙarshen zamani domin kuwa daga cikin zuri'arsa Allah
zai fitar da Mahdi, wanda zai amshi ragamar shugabancin Musulmi don ya kawo
gyara a wannan lokaci.[8]
5.9 Matsayin
Hussaini A Kan Wannan Sulhu
Al
Hussaini ya lizimci kawaici game da abinda ya faru amma a zuci bai ji daɗin yin hakan ba. To, sai dai ya yi mubaya'a ya ɓoye damuwarsa.
A
lokacin wafatinsa Al Hassan ya kira ɗan uwansa ya yi
masa gargaɗi, ya ce, kada ka bari mutanen
Iraƙi su ruɗa
ka. Kada kuma ka kuskura ka kwance mubaya'ar da ka yi ma Mu'awiyah. Ka sani
alamu sun nuna Allah ba zai haɗa annabta da
khalifanci a gidanmu ba. Don haka kada ka sa kanka cikin nemansa.
Duk
tsawon mulkin Mu'awiyah kuwa Al Hussaini ya riƙe
wasiccin ɗan uwansa. Amma a lokacin da
Mu'awiyah ya ɓullo da wata
maganar naɗin yarima da yi masa mubaya'a,
kuma ya zaɓi ɗansa
Yazidu, to, a nan Al Hussaini ya cije, ya ƙi ba da
mubaya'arsa ga yarima mai jiran gado. Haka shi ma Abdur Rahman ɗan Abubakar ya yi, bai yi wannan mubaya'a ba.
A
lokacin da Mu'awiyah ya haƙiƙance mutuwa ta zo masa kusa ya kira ɗansa Yazidu ya yi masa wasicci wanda za mu kawo shi
a nan gaba, a cikinsa kuwa har da maganar wasu mutane da suka haɗa da Al Hussaini wanda Mu'awiyah ya ce, ka kula da
alfarmar gidansu da son da jama'a su ke masa.
5.10 Mutuwar Al Hassan
Al
Hassan ya rayu sama da shekaru goma bayan sauka daga muƙaminsa. A cikin waɗannan
shekarun an samu kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da Sarki Mu'awiyah. Sukan
karɓi kyaututtukansa shi da ɗan uwansa Al Hussaini kuma su gaida shi gaisuwar
girmamawa irin wadda ake masa.
A
shekara ta Arba’in da biyu bayan hijira ne Al Hassan ya
ci wani abinci mai guba wanda shi ne ya zama ajalinsa.[9]
Kuma ana tuhumar wata tsohuwar matarsa da suka rabu da yin wannan makirci.
Sanin gaibu sai Allah.
Da
Al Hassan ya lura da kusantowar ajali sai ya yi wasicci ga ɗan uwansa da abin da mu ka faɗa, kuma ya neme shi da ya roƙa masa alfarma daga wurin Uwar Muminai A'ishah domin
yana son a yi masa makwanci kusa da kakansa. Ya ce, amma idan ba ta aminta ba
ka kai ni a maƙabartar Baƙi'ah in da sauran Musulmi.
Da
Al Hassan ya cika Nana A'isha ta yi na'am da buƙatarsa,
amma kuma shaiɗan ya zuga
Marwanu, ɗaya daga cikin dangin khalifa
Usman wanda ya yi tsaye a kan ba za a rufe Al Hassan a wurin ba, domin a
lokacin wafatin Usman an nemi wannan alfarma kuma A'isha ta amince amma aka
hana shi. An samu ruɗani sosai a kan
wannan, amma daga baya Abu Huraira ya sasanta tsakaninsu kuma an rufe Al Hassan
a maƙabartar Baƙi'ah.[10]
Sarautar
Al Hassan dai kamar ramin shuka ce, ba zurfi sai tarin albarka. Domin kuwa duka
duka wata shida ne ya yi akan wannan muƙamin ɗauke da mubaya’ar mutanen Iraƙi da wasu sassa na daular musulunci, a dai dai
lokacin da Mu’awiyah ke jimƙe da mubaya’ar
mutanen Sham. Sai ga shi a dalilin Al Hassan da haƙurinsa kan al’umma ya haɗu akan shugaba guda sun dawo kamar tsintsiya mai maɗauri ɗaya.
[1]
Bayan
haka ne aka samu cikin ƙaninsa Hussaini
bayan haifuwarsa da wata biyu, wanda shi kuma aka haife shi a cikin watan sha'aban
na shekara ta 4 bayan hijra.
[2]
Al
Isabah Fi Tamyizis Sahabah, na Ibnu Hajar, Tahƙiƙin Ali Muhammad Al Bijawi, Bugun Darul Jil, Beirut,
1412H, (2/69).
[3]
Mun
riga mun faɗi cewa, ba tagwaye ba ne. Amma saboda kusancin
shekarunsu (wata goma sha ɗaya ke tsakaninsu)
da kuma al'adar Bahaushe da ta gudana a kiransu tagwaye mu ma muka tafi a kan haka. Don haka ya
zama dole mu yi tambihi.
[5]
Al
Jami',
na Tirmidhi, Hadisi na 3768 da kuma Al Musnad, na Ahmad, (3/3 da 3/62)
da Al Mustadrak, na Hakim, (3/167) kuma Tirmidhi ya inganta shi.
[7]
Duba Sahihul Bukhari
a Kitabul Manaƙib, Babin
darajojin Al Hassan da Al Hussaini da kuma Siyar A'lam an Nubala' (3/259).
[8]
Mutane sun kasu kashi uku
dangane da Mahdi. Akwai masu ganin cewa, Mahdi shi ne Annabi Isah, akwai kuma
masu ganin shi ne Sarkin Musulmi Mahdi ɗan Abun Ja’afar
Al Mansur daga zuri'ar Abbas (Baffan Manzon Allah SAW) wanda yana daga cikin
jerin sarakunan daular Abbasiyyah. Su kuma a wurin Rafilawa ('Yan shi'a masu
da'awar bin Imamai 12) sun ce shi ne Muhammad ɗan
Hassan Al Askari daga zuri'ar Hussaini. Bayan haka aka yi Muhammad ɗan Tomarat a ƙasar Maroko
wanda ya ce shi ne Mahdi, ya kashe bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba, ya
ƙwace matansu da 'ya'yansu da zuri'arsu.
Bayansa kuma aka yi Ubaidullahi ɗan Maimun Al Ƙaddah (asalinsa Bayahude ne, amma a cikin majusawa
ya tashi) shi ma ya ce Mahdi ne. Kuma ya ce yana cikin Ahlulbaiti.
Sa'annan aka yi wani mai da'awar shi ne Mahdi a Sudan a ƙarni na goma sha uku bayan hijira. Mahdin gaskiya
dai yana nan tafe, kuma daga zuri'ar Al Hassan yake kamar yadda hadissai
ingantattu suka tabbatar. Duba Al Manar Al Munif na Ibnul Ƙayyim, shafi na 43.
[9]
Wannan yana nuna cewa,
iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba su san gaibi ba.
Domin kuwa da Al Hassan ya san gaibi ba zai ci abincin da aka sanya guba a
cikinsa alhalin yana sane ba, domin wanda ya yi haka kamar ya kashe kansa
kenan.
[10]
Yana
cikin hikimar Allah cewa, ba wani Annabi ko Sahabi da aka san wurin ƙabarinsa a haƙiƙance in ban da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama da waziransa biyu da ke kwance a ɗakin
Nana A'ishah. Duba Takhlisul Ikhwan na Mujaddadi Usmanu ɗan Fodio.
DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO
DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO