Sayyadina Umar Ɗan Khaɗɗabi Raliyallahu Anhu
Sunansa da Asalinsa
Sunansa Umar ɗan Khaɗɗabi ɗan Nufail ɗan Abdul Uzza ɗan Rayahi ɗan Abdullahi ɗan
Ƙurɗi ɗan Razahi ɗan Adiyyu ɗan Ka'abu ɗan Lu'ayyu ɗan Galibu al Adawi al Ƙurashi.
Ya haɗu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a zumunci ta wajen kakansa na
takwas Ka'abu ɗan Lu'ayyu wanda shi ne kakan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na bakwai.
Mahaifiyarsa ita ce ƙanwar Abu Jahli, Hantamah ɗiyar Hisham ɗan Mughirah daga ƙabilar
Makhzum.
Haifuwarsa:
An haifi Sayyiduna Umar bayan yaƙin nan da aka fi sani da Harbul Fijar a shekara ta Arba’in da uku
kafin hijira. Don haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da shekaru goma cif.
Siffarsa Da Ɗabi'unsa:
An siffanta Umar da cewa, mutum ne dogo, kakkaura, mai sanƙo a kansa. Ga shi
kuma jawur yake kamar ƙwara. Saboda tsawonsa idan ka hango shi daga nesa za ka
yi tsammanin mahayi ne.
Game da ɗabi'unsa kuwa, Umar ya gadi
kaushin hali daga mahaifinsa. A lokacin ƙuruciyarsa ya kasance yana yi wa
mahaifin nasa kiyon raƙumma. Mahaifin kuwa yana wahalar da shi sosai, yana kuma
dukansa idan ya saɓa masa.
Mahaifin Umar, al Khaɗɗabi ya kasance yana wahalar da ƙanensa Zaidu musamman ma
lokacin da ƙanen nasa ya ƙyamaci bautar gumaka, ya je neman addinin gaskiya na
Annabi Ibrahim. Shi kuma Umar ya kan wahalar da ɗan baffansa kuma mijin ƙanwarsa
Sa'idu ɗan Zaid, musamman a lokacin da ya san ya musulunta tare da matarsa.
2.4 Rayuwarsa Kafin Zuwan Musulunci
Muna iya raba rayuwar Sayyiduna Umar
gida biyu; kashi na farko ya yi shi kafin zuwan Musulunci, kashi na biyu kuma a
cikin Musulunci. A kashi na farko na rayuwarsa, Umar bai zamo wani mutum mai
cikakken muhimmanci ba, duk da yake yana cikin 'yan majalisa. Amma furta kalmar shahadarsa ke da wuya sai ya koma
wani muhimmin mutum wanda rayuwarsa take da muhimmin ambato daga wannan rana har zuwa ranar
tashin ƙiyama.
Umar shi ne wakilin ƙabilarsa ta
Banu Adiyyin a majalisar zartaswa ta ƙuraishawa wadda ta ke da kujeru goma
kamar yadda muka faɗa a baya. Kuma ofis ɗinsa shi ke kula da hulɗar ƙuraishawa
da sauran ƙabilu musamman ga abin da ya shafi yaƙi da sulhu da makamantansu
kamar yadda ya gabata a tarihin Abubakar.
Yadda Musulunci Ya Ratsa
Zuciyarsa
Umar ya musulunta a shekara ta biyar
kafin hijira bayan talakawan Musulmi sun sha wuya sosai a hannunsa. To, ya aka
yi ya musulunta? Wane irin sirri ne ya karya zuciyarsa a daidai wannan lokaci?
Tun da farko dai Allah ya yi masa gamon katar ne da addu'ar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa lokacin da ƙunci da
wahala suka tsananta a kan talakawan Musulmi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roƙi Allah ya ƙarfafi addininsa
da ɗayan mutane biyu, duk wanda ya fi soyuwa zuwa ga Allah a cikinsu; Umar ɗan
Khattabi ko kawunsa Abu Jahli ɗan Hisham. Zaɓin Allah sai ya faɗa a kan Umar.
Farkon bayyanar tasirin wannan addu'a shi ne lokacin da wasu raunanan Musulmi
za su yi hijira zuwa Habasha sai Umar ya gamu da su. Sai ya tambayi Ummu
Abdillahi ɗiyar Hantamah ina suka nufa? ta ce masa, za mu bar mu ku garinku tun
da kun ƙuntata mana, kun hana mu 'yancin mu yi addinin da muka zaɓa, kun hana
mu saƙat kamar mu ba 'yan gari ba ne. Za muje in da za mu samu sauƙi da
kwanciyar hankali tun da ƙasar Allah faɗi gare ta. Da ta gama faɗin wannan
magana sai Umar ya ce, Allah ya kai ku lafiya!
Wannan addu'a ta Umar kuwa ta bai wa kowa mamaki, domin ba a san shi da tausaya
wa Musulmi ko kaɗan ba. Da Ummu ta faɗa ma Amiru ɗan Rabi'ah abin da ya faru
sai ya ce ma ta, hala kina zaton Umar ya musulunta? Sai ta ce, eh, don na ga ya
tausaya mana sosai saɓanin al'adarsa. Amiru ya ce, to sai in jakin gidansu ya
musulunta!
Ana cikin haka ne wata rana Umar ya shiga Masallacin ka'aba domin ya yi ɗawafi
ya gaida iyayen gijinsa, sai ya yi kiciɓis da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana Sallah. A wannan karon sai ya ɗan
mayar da hankali domin ya ji abin da Manzo yake karantawa. Aka yi daidai kuwa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana karanta suratul Haƙƙah, sai
karatun ya kama shi sosai har ya ce, wallahi Ƙuraishawa
sun yi gaskiya da suka ce mawaƙi ne. Amma wallahi waƙarsa tana da daɗi. Bai
rufe bakinsa ba sai Manzon Allah ya kawo inda Allah ke cewa,
)فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ (38) وَمَا لَا
تُبْصِرُونَ (39) إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (40) وَمَا هُوَ بِقَوْلِ
شَاعِرٍ قَلِيلًا مَا تُؤْمِنُونَ (41)(
Ma'ana:
To, ba sai na yi rantsuwa da abin da
kuke iya gani ba. Da abin da ba ku iya gani. Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas
maganar wani manzo mai daraja ce (Jibrilu AS).
Da Umar ya
ji haka sai ya ce, to in ko haka ne boka ne kenan. Sai ya ji ance,
)وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ
(42) تَنْزِيلٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ (43)(
Ma'ana:
Kuma shi ba maganar boka ba ne. Kaɗan
ƙwarai za ku iya tunawa. Abin saukarwa ne daga Ubangijin halitta duka.
A nan sai ransa ya ɗarsa masa cewa,
to ko ƙarya ce yake yi? Sai karatun ya ci gaba:
)وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ
(44) لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ (45) ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ
(46) فَمَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ (47) وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ
لِلْمُتَّقِينَ (48) وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنْكُمْ مُكَذِّبِينَ (49)
وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ (50) وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ (51)
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (52)(
Ma'ana:
Kuma da (Manzon Allah) ya faɗi wata magana, ya jingina ta
gare mu. Da mun kama shi da dama. Sa'an nan, lalle ne, da mun katse masa lakka.
Kuma daga cikinku babu wasu masu iya kare (azabarmu) daga gare shi. Kuma lalle
ne shi (Alƙur'ani) tunatarwa ce ga masu taƙawa. Kuma lalle ne mu, wallahi, muna
sane da cewa daga cikinku akwai masu ƙaryatawa. Kuma lalle ne shi (Alƙur'ani)
wallahi baƙin ciki ne ga kafirai. Kuma lalle shi gaskiya ce ta yaƙini. Saboda
haka, ka tsarkake sunan Ubangijinka, Mai girma.
Kafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama sallah jikin Umar ya yi
sanyi sosai, zuciyarsa ta sauya duk yadda ba a zato, amma dai lokacin bai yi ba
tukuna.
Bayan kwana uku da musuluntar baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Hamza, sai Umar ya gamu da wani daga cikin talakawan
Musulmi sai ya fara gaya masa magana mai kaushi kamar yadda ya saba, a lokacin
Musulmi sun fara jin ƙarfin yin magana saboda musuluntar Hamza, sai wannan
bawan Allah ya kada baki ya ce masa, to, kai Umar ka na wahalar da kanka a kan
matsalar da ko cikin gidanku ba ka magance ta ba! Umar ya ce, wane ne ya
karkace a cikin gidanmu? Sai ya ce, ƙanwarka da mijinta.
Jin haka ke da wuya sai Umar ya fusata ya tasar ma gidan
Fatimah ɗiyar Khattabi. Da ya isa sai ya ji sautin karatun Alƙur'ani, amma
kafin a buɗe masa ƙofa sai da aka ɓoye takardun da ake karatu don gudun
sharrinsa. Kafin Fatimah ta gama yin maraba da yayan nata tuni har ya kai ma ta
duka yana neman a ba shi abin da ake karantawa. Da suka lura al'amarin nasa
babu tausai ko kaɗan a ciki sai ƙanwarsa ta ce masa, an ƙi a ba ka, kuma
Musulunci ko kana so ko ba ka so sai an yi. Ka yi duk abin da kake iyawa!
Nan take sai jikin Umar ya yi sanyi, hankalinsa ya fara dawo
masa, ya ji kunyar wannan raini da ya janyo ma kansa daga ƙanwarsa wadda ta ke
ganin girmansa tana mutunta shi. A cikin lumana sai ya nemi ƙarin bayani. Allah
Sarki! Kafin marece Umar ya bi sawun Musulmi.
Musulunci Ya Ɗaukaka Da Shigowarsa
Musuluntar Umar ke da wuya sai ya nemi a fito da addini sarari; a daina ɓoye
shi kamar garar kunya. A wannan ranar ne Musulmi suka fito a cikin garin Makka
su kayi wani jerin gwano a ƙarƙashin jagorancin Umar da Hamza don su bayyana wa
mushrikkai cewa, yanzu fa Musulunci ya samu gata, ya yi shingi ya huta da
ratse.
Gudunmawarsa Ga Musulunci
Tun daga musuluntarsa, Umar ya lizimci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya kasance a ƙarƙashin ɗa'arsa, ba ya zartar da kome ko da
a gidansa sai da iznin Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama. Kuma Umar ya yi amfani da ƙarfin
jikinsa da kwarjinin da yake da shi a idon kafirai don ya yi kariya ga Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da
sauran Musulmi. Ko a lokacin hijira ma, Musulmi sun shirya kowa ya fita a nasa
lokaci wanda ya yi masa, yana mai ɓoye ma idanun kafirai, sai shi Umar ne kaɗai
ya fita da rana tsaka yana ce ma kafirai wa zai ce kule in ce masa cas?!.
A Madina kuwa, Umar na ɗaya daga cikin zaratan mayaƙa waɗanda su kayi ruwa da
tsaki wajen kare martabar Musulunci da ruguza abokan faɗansa.
Ya kusanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har
ya kai matsayin wazirinsa na biyu. A shekara ta uku bayan hijira sai Allah ya
karrama shi da surukuta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama in da Manzo ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka
ɗaura aure, sai ta zama ita ce ta uku daga cikin matansa bayan rasuwar
uwargidansa Khadijah.
2.6 Umar Ya
Dace Da Alƙur'ani
A wurare da dama Umar ya dace da hukuncin Alƙur'ani kafin saukarsa. Misali,
Umar ne ya ba da shawarar kada Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halarci sallar jana'iza a kan munafukai, kuma sai Alƙur'ani ya
sauka da wannan hukuncin. Haka kuma Umar ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shawarar ya hana mutane shiga
gidansa, kuma Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Shi ne kuma ya nemi a
shamakance mata daga maza ta hanyar amfani da hijabi, sai Allah ya saukar
da wahayi a kan haka. Ya bada shawarar a kashe
fursunonin Badar, Allah ya ƙarfafi ra'ayinsa a Suratu Ali Imran. Waɗannan duka
suna nuna irin kaifin basirarsa da kusancinsa ga Allah da sanin abin da Allah
yake so da wanda ba ya so.
Umar Ya Zama Sarkin Musulmi
Abubakar ya ayyana ma Musulmi Umar a matsayin wanda zai gade shi bisa ga
shawararsu kamar yadda ya gabata. Don haka da Abubakar ya cika nan take mutane
su kayi masa mubaya'a kuma ya kama aiki.
Wani muhimmin abinda ya kamata a sani game da khalifancin Umar shi ne kwarjinin
da yake da shi matuƙa a idon jama'a. Amma kuma duk da haka talakawa sun more a
lokacin khalifancinsa, domin kuwa ya kasance yana kula da al'amurransu ta ko
wane fanni. Bayan dai kulawarsa da tsayuwar addini, Umar yana kulawa da jin daɗin
rayuwar jama'a da inganta lafiyarsu da gyaruwar tattalin arzikinsu da samun
kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakaninsu.
Irin kwarjinin da Umar yake da shi a zukatan jama'a ya sanya wata mata ta yi ɓarin
cikinta a lokacin da ta samu labarin an kai ƙararta ga Sarkin Musulmi Umar.
Wannan ya sanya Umar ya tara jama'a ya nemi shawararsu a kan wannan abinda ya faru don sanin ko
diyya ta wajaba a kansa. Ya kuma yi aiki da ra'ayin Ali na biyan diyyar
jinjirin da aka rasa.
Ba za mu yi mamakin wannan mata ba
idan muka san cewa, manyan Sahabbai irin su Zubairu ɗan Awwam da Sa'adu ɗan Abu
Waƙƙas sukan tafi wajen Umar da nufin gaya masa wata magana ko gabatar da wata
buƙata, amma su je su dawo ba su samu damar yin haka ba saboda kwarjininsa da ya
cika masu fuska. Ibnu Abbas ma duk da irin kusancin da yake da shi ga Umar amma
ya yi shekara ɗaya yana son ya tambaye shi game da wata aya bai samu damar haka
ba saboda kwarjininsa.
Wani wanzami kuma ya saki iska saboda tsoro a lokacin da Sarkin Musulmi Umar ya
yi tari shi kuma yana yi masa aski.
Umar kansa ya kan damu wani lokaci da yadda jama'a
suke fargabansa, har ma ya kan ce, Ya Allah! Ka san na fi tsoronka
fiye da yadda su ke tsorona.
A game da kulawarsa da talakawa kuwa, Umar ya shahara da ziyarar sa ido wadda
yake yi a cikin dare yana sintiri a tsakanin hanyoyi da gidaje don sanin halin
da ƙasarsa ta ke ciki. A cikin irin wannan ziyarar ne yake gano idan akwai ɓarayi
ko wasu miyagu ko maɓarnata masu fakewa a cikin duhun dare su yi aikin assha,
ko kuma baƙo wanda bai samu masauki ba.[1]
Da yawa Sarkin Musulmi Umar ya yi aikin agaji ga wasu
talakawan da su ke da buƙata wadda ya gano ta a dalilin wannan sintiri da yake
yi. Misali, ya samu wani baƙo tare da matarsa tana naƙuda su kaɗai a cikin wata
bukka, sai ya dawo gida ya nemi matarsa Ummu Kulsum ɗiyar Ali don ta je ta
taimaka ma wannan baiwar Allah, a lokacin da shi kuma ya ɗauki kayan abinci ya
hasa wuta ya yi masu dafuwa wadda mai jego ta ke buƙata.[2]
Wannan sintiri na Umar kuma ya haifar da sauyin wasu dokoki da tsare tsare a
gwamnatinsa. Misali, a dalilin haka ne ya sanya doka game da masu zuwa jihadi
kar su wuce wata huɗu ba a dawo da su gida ba, domin ya ji wata mata ta matsu
tana koke game da daɗewar mijinta a fagen fama.[3]
Ya kuma sabunta doka game da rabon arziki inda ya sanya ma
duk jaririn da aka haifa a Musulunci albashi na kansa bayan a da sai wanda aka
yaye shi ne ake ba albashi, amma a cikin dare sai ya lura da wani yaro yana
yawan kuka, da ya nemi bayani sai ya gano uwarsa ta yaye shi kafin lokaci don
tana son a rubuta masa albashi. A kan haka ya yi wannan sabuwar doka.[4]
Haka kuma ya canza ma wani saurayi da ake ce ma Nasru ɗan
Hajjaj wurin zama ya tayar da shi daga Madina ya koma Basrah saboda ya ji wasu
mata a cikin dare suna taɗi game da kyawonsa, da ya bincika sai aka gaya masa
har yana shiga a cikin gidaje, don haka Umar ya ji tsoron aukuwar fitina a
gidajen bayin Allah waɗanda suka je wurin jihadi suka bar matansu a gida, sai
ya ɗauki wannan mataki don magance ta.
Ban da wannan kuma Umar ya kan zauna bayan ko wace Sallah don sauraren buƙatun talakawa. Ya kan kuma
shiga kasuwa don ya gane ma idonsa abin da ke gudana don ya hana yin cuta.
Misali, akwai lokacin da ya tarar da wani baƙo yana sayar da man kaɗe a kan wani
farashi da ba a saba da shi ba, sai ya umurce shi da ya sayar a kan farashin
da aka sani, ko kuma ya fita daga wannan kasuwa. Kuma ya kan hana
yin kasuwanci ga wanda bai san yadda ake yinsa ba.[5]
Ƙaunar Da Umar Yake Bayyana Ma Ahlulbaiti
A cikin littafinmu Su wane ne masoyan
ahlulbaiti? Mun yi bayani game da irin gatancin da iyalai da dangin Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suka
rinƙa samu a zamanin khalifancin Umar Raliyallahu Anhu. Mun bayyana yadda ya tsara rabon arzikin ƙasa ta yadda
iyalai da dangin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama za
su more fiye da kowa. Bari mu ɗan ɗebo daga abin da muka faɗa a can:
"Bisa ga wannan rajista kuwa, Sayyiduna Ali shi ne ya
fi kowa samun kaso mai tsoka, in ban da Matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da
ɗan uwan mahaifinsa Abbas. Sai ga khalifan da kansa ya na karɓar albashi ƙasa
da na iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama."
"Haka kuma a cikin bitar da Umar ya ke yi wa rajistar,
ya tarar da sunayen Hassan da Hussaini a matsayinsu na ‘ya’yan Ali dai dai da
sauran ƙananan yara ‘ya’yan Sahabbai, suna da dirhami dubu biyu ko wannensu.
Amma sai Sayyiduna Umar ya cire su, ya riskar da su da babansu, aka yanka masu
dubu biyar-biyar, ya ce, saboda kusancinsu da Manzon Allah da irin son da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ɗin
yake yi masu."[6]
"Abdullahi ɗan Umar ya yi koke game da nasa albashin, domin Sayyiduna Umar
ya ƙara ma Usamatu ɗan Zaid Dirhami ɗari biyar a kan albashinsa. Shi kuma a ganinsa, ba
wani abinda ya raba shi da Usamatu, domin su tsara ne, waɗanda suka tashi tare,
suka je wuraren jihadi ɗaya tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama. Amsar da Babansa ya ba shi ita ce:
“Na fifita shi ne a kanka, don Manzon Allah ya fi sonsa a kanka, ya kuma fi son
mahaifinsa a kan naka”[7]
"A cikin matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ma,
sai da Umar ya fifita Nana A’ishah a kan sauran mata (waɗanda suka haɗa da ɗiyarsa
Hafsah), la’akari da fifikonta wajen son da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
ke yi mata. Duk da ya ke wasu kan cewa, tun da Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama bai banbanta su ba a kyautukansa, shi ma ya daidaita su.
Sa’annan ya mayar da albashinsu iri ɗaya."
"Idan mu ka koma wajen sauran dangin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, za mu ga irin matsayin da su ke samu a wurinsa. Misali,
Umar ne kaɗai a zamanin mulkinsa ya ke kusanto da ƙanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Abdullahi ɗan Abbas, duk da ƙanƙantarsa. Idan aka yi masa
magana ya kan ce: “Yaro da gari abokin tafiyar manya ne”. Ya na nuni da
irin ilminda ya ke da shi".
"Game da mahaifin nasa kuma (Ina nufin Abbas, baffan
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Umar ya taɓa yin ciris da fushinsa. Wannan ya faru a
lokacin da aka ci garin Makkah, domin shi Umar ɗin ya na da ra’ayin duk a gama
da maƙiyan musulunci waɗanda suka ƙare rayuwarsu wajen yaƙar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi kuma Abbas ya na da ra’ayin a yafe masu. Da zancen ya
haɗa su sai Abbas ya fusata, ya ce, don dai ba suna ‘yan ƙabilarka ba ne! Anan
sai Umar ya ce masa, Ni, ba ni da wani ƙabilanci ga jama’ata a kan musulunci.
Don wallahi ranar da ka musulunta nafi farin ciki bisa ga a ce khaɗɗabi ne,
babana, ya musulunta, don kuwa na san irin farin cikin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan musuluntarka".[8]
Haka kuma a cikin wancan littafin mun faɗi irin yadda Umar
ya ke gabatar da makusantan Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama a kan nasa dangi da makusanta. Ga ɗaya daga cikin labaran da muka
cirato don ƙarfafa wannan bayani: "Wata rana Umar ya aike ma 'yar
uwarsa As Shifa'u ɗiyar Abdullahi domin ta zo yana son ganinta, ko da ta zo sai
ta tarar da wata baƙuwa wadda ita ce Atika ɗiyar Usaid. A lokacin da Umar ya gansu a tare sai ya ɗauko wasu mayafai
guda biyu babba da ƙarami, ya bai wa Atika babbar ita kuma Shifa'u ya ba ta ƙarami.
'yar uwarsa ba ta ɓoye damuwarta ba a kan wannan banbanci sai ta ce masa, haba
Sarkin Musulmi, kai ne fa ka aika kira na wannan kuma ita ta zo da kanta, a
musulunta kuma na riga ta, sannan ni 'yar uwarka ce, ya za kayi min haka? Umar
ya amsa mata da cewa, a haƙiƙa na kira ki ne don in baki su duka, amma da na
ganta na tuna kusancinta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai naga ta fi dacewa da in ba ta
babba, don haka sai ki yi haƙuri".[9]
Yadda Umar Yake Kula Da Dukiyar
Jama'a
Umar ya kasance mai yawan tsentseni dangane da dukiyar al'umma da yake kula da
ita a matsayinsa na shugaban Musulmi. Kuma ya kan tsananta ma kansa da iyalansa
dangane da ita. Ga wasu daga cikin labaran irin taka tsantsan da yake yi:
1. Umar
ya kan kashe fitilar gwamnati idan ya ƙare aikinda ya shafi jama'a
sannan ya kunna tasa domin kada ya shiga haƙƙen da ba nasa ba.
2. A
lokacin da yaronsa ya ba shi madara ya sha yana tsammanin daga raƙumarsa ne, amma
daga baya ya gane daga raƙumar gwamnati ne sai da ya shawarci surukinsa
Sayyiduna Ali a kan wannan, Ali ya nuna masa ba kome.
3. Ya
samu labarin ɗansa ya kiyata raƙumarsa a cikin raƙuman gwamnati, sai ya hane
shi kuma ya umurce shi da ya mayar da abin da ta haifa a cikin taskar gwamnatin tun da yake
da abincin gwamnati aka yi kiyonta.
4. Matarsa
Ummu Kulsum ɗiyar Sayyiduna Ali ta aika da kyautar turare zuwa ga matar sarkin
Ruma ta hannun Manzon da ya aika masa. Da aka zo mata da tukuici sai ya umurce
ta da ta mayar da shi cikin dukiyar gwamnati tun da yake Manzon da ya kai saƙon
gwamnati ce ta aike shi. Da ta kai ƙara wurin mahaifinta, Ali ya goyi bayan
khalifa Umar, sai dai ya ba da shawarar a cire ma ta daidai abin da ta aike da
shi.
5. Ya kan hana
matansa su yi amfani da abin da ya rage idan aka raba Turare ko Mai ko ire
irensa ko da kuwa su shafa kansu da abinda ya saura a hannayensu ne domin yana
ganin ba halaliyarsu ba ne.
Yadda Umar
Yake Naɗa Muƙamai
Babban abin da Umar yake kula da shi a wajen naɗa shugaba shi ne ƙwarewarsa a
irin aikin da ake buƙata. Da yawa Umar ya kan naɗa mutum a kan wani muƙami ya bar wasu waɗanda sun
fi shi daraja saboda la'akari da iyawarsa ga wannan aiki fiye da su. Ya kan gwada mutum lokaci mai tsawo kafin
ya ba shi muƙami kamar yadda ya tsayar da Ahnafu ɗan Ƙaisu tsawon shekara guda
a Madina, sannan ya ce masa, na jarabta ka na lura da alheri a zahirinka, kuma
ina fatar baɗininka ya kasance haka. Sannan ya yi masa wa'azi, ya naɗa shi
gwamna.
Wani abin da zai bayyana mana ma’aunin da Umar ke gane wanda ya cancanci muƙami
da shi, shi ne, labarin yadda ya naɗa Shuraihu a matsayin alƙali. Ga yadda
labarin ya ke:
Watarana halifa Umar ya ɗauki hayar
doki daga wani talaka, ya kuma yi masa sharaɗin cewa, su biyu ne zasu hau dokin
da shi da wani amininsa. Ga alama wannan dokin bai yi ƙwarin da zai ɗauki ɗawainiyar
Umar tare da abokinsa ba. Amma duk da haka wannan bawan Allah ya amince, wataƙila
don ganin Sarkin Musulmi zai yi amfani da shi. Kuma ko ba komai idan dokin ya
samu matsala Umar mai iya ranka masa ne. To, amma hasashen wannan bawan
Allah sai bai zamo dai dai ba, domin kuwa a lokacin da dokin ya kasa Umar ya
umurce shi ne da ya haƙura ya ɗauki kayansa. Amma sai shi kuma ya ce bai yarda
ba sai an bashi diyyar raunana masa abin hawa da aka yi. Da suka kasa cimma
yarjejeniya sai Sarkin Musulmi Umar ya neme shi da ya samar da wanda zai yi
hukunci a tsakaninsu. A nan ne wannan bawan Allah ya ba shi sunan Shuraihu,
wanda ya ke ba sahabi ba ne amma yana daga cikin malamai masu basira. Shuraihu
kuwa bayan da ya gudanar da bincike kan mas’alar sai ya yi hukunci da cewa,
dole ne Sarkin Musulmi ya biya talakka ɓarnar da ya yi masa. Dubin irin ƙwararan
matakan da Shuraihu ya ɗauka na bincike da yadda ya yi ƙarfin halin ba Sarkin
Musulmi rashin gaskiya su suka sa nan take Umar ya naɗa shi alƙali. Sai
Shuraihu ya kasance shi ne naɗaɗɗen alƙali na farko a tarihin musulunci.[10]
Umar ya kan shawarci mutane game da wanda za a
ba muƙami. Kuma a zamaninsa duk gwamnan da aka naɗa sai an ba shi rubutacciyar
takarda da sa hannun Sarkin Musulmi a kanta wadda kuma ta ƙunshi sharuɗɗan
wannan aiki da aka ɗora masa. Ya kan halartar da jama'a don su yi shaida
kamar irin tsarin rantsarwar da ake yi a gaban jama'a a wannan zamani.
A koda yaushe Umar ya kan zaɓar ma mutane shugaba daga
cikinsu. Ba ya ɗora baƙauye a kan 'yan birni saboda rashin dacewar
yanayinsu da al'adunsu da tunaninsu. Ya kan zaɓi masu ilmi don sukarantar da
jama'a. Tausayi shi ma sharaɗi ne kafin mutum ya cancanci shugabanci a
zamaninsa. Don haka, ya fasa naɗa wani mutum daga ƙabilar Banu Sulaim a kan ya ce shi bai taɓa sunbantar
'ya'yansa ba, Umar ya ce, ba ka da jinƙai ke nan, ba za mu shugabantar da kai a kan jama'a ba.
Umar ya hana duk gwamnoninsa yin
kasuwanci ko wane iri don gudun su nemi wani sassauci ko a yi musu rangwame don
la'akari da muƙaminsu sai raini ko jin nauyi ya shiga tsakaninsu da
talakawansu, abin da zai iya hana zartar da adalci a wajen hukunci. A kai a kai
kuma ya kan rubuta wasiƙu na faɗakarwa da jan
kunne zuwa gare su don su zamo masu amana da gaskiya da yin adalci a cikin
aikinsu.
Tsakanin
Umar Da Gwamnoninsa
Ana iya cewa, dukkanin gwamnoni a zamanin khalifancin Umar sun yi tasiri da
tsarin tafiyar da al'amurransa. Mafi yawansu sun kasance masu tsentseni da
gudun duniya kamarsa. Amma kuma duk da haka, Umar sai ya lisafta abin da
gwamnansa ya tara na arziki idan lokacin ƙarewar
aikinsa ya zo. Kuma da yawa waɗanda ya karɓe rabin dukiyarsu ya mayar a taskar
hukuma saboda wasu dalilai da suka shafi tara kuɗi ta wata hanya ba albashi ba,
kamar kasuwanci ko kiyo da sauransu.
Sarkin Musulmi Umar ya umurci duk
gwamnoninsa da su rinƙa zuwa aikin hajji tare da jama'arsu domin su samu
halatar taron shekara shekara da yake yi da su inda yake yi ma su gargaɗi a
game da talakawansu. Ya kan ce da su, "Ban ɗora ku a kan talakawa ba don kuci dukiyarsu ko
mutuncinsu ko ku zubar da jininsu. Na tura ku ne don ku tsayar ma su da Sallah,
ku sanar da su addini, kuyi masu rabo a kan adalci." Ya kan sanar da talakawa cewa, suna da ikon
kawo ƙara idan gwamnoninsu suka cuta masu.
A ɓangaren gwamnoninsa da sauran
sarakuna kuma, Umar ba ya yarda a wulaƙanta su. Don haka, duk talakkan da ya
kuskura ya ci mutuncin basarakensa ko ya yi masa raini wanda bai dace ba to,
Umar ba ya sassauta masa.
2.12 Jihadi Da Faɗaɗar Daular
Musulunci A Zamaninsa
Dukkanin ayyukan jihadi da Sarkin Musulmi Abubakar ya soma sun samu kammala a
khalifancin Umar.
A zamaninsa, an kasa ayyukan jihadi zuwa ɓangare biyu: Gabas wadda ta haɗa da
Iraƙi da garuruwan Farisa har cikin ƙuryarsu, da kuma Yamma wadda ta haɗa da
Sham da Misra da Libiya.
A Gabas an ci garuruwa masu ɗinbin yawa da suka haɗa da; Kaskar, Sabat, Al
Mada'in (Hedikwatar Farisa), Jalula, Tustar, Jundai Sabur, da Nahawand. Sannan
sai Hamadhan, Rayy, Ƙumsi, Jurjan, Ɗabaristan, Azrabijan da Khurasan. Duk waɗannan
yankuna ne da birane da suka kasance ƙarƙashin Farisa.
Sai kuma sashen Turkiyyah da Isɗakhr
da Fasa da Dara Bijird da Kirman da Sijistan da Mukran da dukkan garuruwan
kurdawa.
A ɓangaren yamma kuma, musulmi sun
lashe dukkan biranen Sham waɗanda suka haɗa da Dimashƙa da Fihlu da Bisan da Ɗabriyyah
da Himsu da Ƙinnisrina da Ƙaisariyyah da birnin Ƙudus. Duka waɗannan sun
kasance a ƙarƙashin mulkin Rumawa, sai Allah ya wargaza ikonsu ya bai wa
musulmi nasara a kansu zamanin khalifancin Umar ɗan Khaɗɗabi.
Daga nan kuma sai ƙasar Misra wadda ita ce yanki na biyu a cikin riƙon
Rumawa. Ita ma an samu nasarar buɗa garuruwanta kamar su Bilbis da Ummu Danin
da Iskandariyyah da duk garuruwan da ke tsakaninsu. Sannan musulmi suka wuce
zuwa Barƙa da Ɗarabulus a ƙasar Libya, suka kuma samu cikakkiyar
nasarar shigar da su a cikin daular musulunci.
Kafin ƙarshen khalifancinsa Umar ya gama da manya manyan dauloli biyu da
su ke da ƙarfin yaƙi da tattalin arziki a duniya wato, Farisa da Ruma. Ya kuma
shigar da karantarwar addinin Musulunci har abinda ya kai birnin Sin ta gabas,
ya kuma game kusan dukkan yankuna na duniyar wancan lokaci.
Da haka ne Musulunci ya wayi gari shi ne addini mafi ƙarfi wanda kuma
hukumarsa ita kaɗai ce mai faɗa aji a duniya. Don haka sai aka kau da ƙabilanci
da faɗace faɗacen al'ada da aka saba. Mutane suka samu walwala da 'yanci a ƙarƙashin
mulkin Musulunci.
Siyasar Yaƙe - Yaƙen Umar
Khalifa Umar ya kasance ya na gudanar da duk yaƙe - yaƙen da ake yi daga
hedikwatarsa ta Madina. Kafin ya ba da ko wane umurni kuwa sai ya nemi a
siffanta masa wuraren yaƙi da yanayinsu. Ya na kuma biye da labaran abin da ke
gudana daki daki. Ya kan fita da kansa bayan gari ya na
tarbon labarai daga matafiya da 'yan saƙon da aka aiko masa.[11]
A wajen zaɓin shugabannin mayaƙa, Umar ya kasance ya kan zaɓi masu tsoron Allah, masu natsuwa
wajen ɗaukar matakai ko yanke hukunci, masu ƙarfin hali da jarunta da sha'awar
yaƙi, masu kaifin basira da sanin dabarun faɗa da abokan gaba.
Wani abinda zai bayyana mana siyasar Sarkin Musulmi Umar a sha’anin jihadi shi
ne, gaggawar cire Khalid ɗan Walid daga jagorancin mayaƙa da ya yi kai tsaye
bayan fara aikinsa, alhali kuwa Khalid ya yi fice tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma lokacin Abubakar saboda ɗinbin
nasarorin da Allah ya ba shi a kan maƙiya. Masanan tarihi sun tofa
albarkacin bakinsu game da wannan lamari. A ra'ayin wasu, Umar ya yi haka ne
saboda kusancin ɗabi'arsu. Domin kaifinsu iri guda ne, sai suka dace su zamo
ma'aikata a gwamnatin Abubakar wanda aka sani da sanyin hali. Amma a yanzu bai
dace jagora na sama da na ƙasa duk su zamo masu gauni ba. Don haka ya zama
tilas a canza shi.
Wata riwaya kuma daga Umar ɗin kansa ta nuna fargaban da ya ke da shi game da
yadda mutane suka canfa Khalid a wajen yaƙi, abinda ya ke iya shafar imaninsu
game da cewa, Allah shi kaɗai ne mai bada nasara idan ya so.
Duk yadda lamarin yake dai, Umar ya zaɓi Abu Ubaidah a madadin Khalid. Abu
Ubaidah shi kuma sai ya raba aikinsa kashi kashi, ya naɗa wasu ƙananan jagorori
waɗanda ya zaɓa daga cikin mayaƙan da ke ƙarƙashinsa, a cikinsu kuwa har da shi
Khalid kansa, da Yazid Ɗan Abu Sufyan da Shurahbil ɗan Hasanah da Habib ɗan
Maslamah, shi kuma ya zama mai kula da aikinsu gaba ɗaya. Khalid kuwa bai nuna
damuwa ba a kan cire shi da Umar ya yi, bai kuma ƙi
ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihadi ba tun da ya ke aikin na Allah ne, kuma
nasarar addini ake nema da yardar Maɗaukakin Sarki.
Wasu Darussa
Daga Waɗannan Yaƙe - Yaƙe
Da yake ba zai yiwu a irin wannan taƙaitaccen littafi a fayyace labarin yaƙe -
yaƙen da suka kai ga cin garuruwan da muka ambata ba. Zai yi kyau mu bayyana kaɗan
daga cikin darussan da ake iya koyo daga cikinsu.
Darasi na Ɗaya: Haɗin kan Sahabbai a Yaƙe - yaƙen
Muna iya cewa, dukkanin waɗanda suka cancanci zuwa yaƙi a wancan lokaci sun
taka irin tasu rawa wajen samar da nasara ga yaƙin buɗar birane da khalifa Umar
ya shelanta.
An ba da labarin cewa, a yaƙin Ƙadisiyyah kawai sama da mutane saba'in daga
cikin mayaƙan Badar suka halarta. Fiye da mutane ɗari ukku daga masu Bai'atur Ridhwan, fiye da ɗari ukku daga jarumawan Fathu Makkah, fiye da mutane ɗari bakwai daga
'ya'yan Sahabbai. Kai kusan ana iya cewa, ba wani ƙwararre ko gwani da bai fito
da ƙwarewarsa ko ya bayyana bajintarsa ba a wannan yaƙin.
Darasi na
Biyu: Mayaƙa sun bayyana jarunta da Amana da Imani
Babu irin nau'in haƙuri da jarunta wanda Musulmi ba su nuna ba a lokacin yaƙe -
yaƙen da mu ke magana a kansu. A Farisa misali, Majusawa sun firgita da irin ƙarfin
halin musulmi, wanda ya kai ga su ratsa kogin Dijla ba tare da jirage ba.
Fitattun jarumawa irin Ƙa'aƙa'u ɗan Amru da Nu'umanu ɗan Miƙrin sun ba da himma
matuƙa a yaƙin Nahawand da Tustar.
A game da amana kuwa, Sarkin Musulmi da kansa sai da ya jinjina masu bisa ga
irin tarin dukiyar da suka aiko da ita daga fagen fama zuwa fadarsa, ya na
cewa, lalle waɗanda suka kawo wannan dukiya amintattu ne. Ali ya ce masa, kai
ne ka zamo amintacce don haka talakawanka suka bi sawunka. Daga cikin ganimomin
da suka iso fadar Khalifa Umar kuwa har da takobin Kisra shugaban ƙasar Farisa da na Hiraƙlu shugaban Ruma da ababen ado
da na more rayuwa iri iri da kuma kayan alfahari na tarihi da suka mallaka waɗanda
kakanninsu ke bugun gaba da su.
Dangane da kishin addini kuwa, muna iya fahimtarsa daga labarin wani ladani mai
kiran sallah wanda ya rasu a fagen fama, mutane duk su ka nuna sha’awarsu ga muƙamin
nasa, sai da har aka kai ga yin ƙuri’a a tsakaninsu.[12]
Yadda Sarkin
Musulmi Umar Ya Gamu Da Ajalinsa
A ƙarshen shekara ta Ashirin da uku bayan hijira ne Umar ya yi mafarkin wani jan
zakara ya saƙƙwace shi sau biyu. Da ya labarta ma Asma'u ɗiyar Umais (matar da
Ali ya aura bayan ta yi wa Abubakar wankan takaba) wadda an san ta da fassarar
mafarki, sai ta ce masa, wani ba'ajame zai kashe ka.
A tsarin gwamnatin Umar duk namijin da ya balaga daga cikin kafirai ba a bashi
damar zuwa Madina. Amma Mughirah ɗan Shu'ubah, gwamnansa na Kufa ya nemi
izninsa domin ya turo masa wani yaro mai hazaƙa daga cikin 'ya'yan farisa ana
kiransa Abu Lu’lu’ata wanda kuma bai musulunta ba. Yaron ya ƙware wajen
sana'oin hannu kamar ƙira da sassaƙa da zane da makamantansu. Umar ya ba da
izni.
Bayan da Abu Lu’lu’ata ya tare a Madina, ya nemi sassaucin harajin da Mughirah
ya ɗora masa a wajen Sarkin Musulmi Umar. Umar ya tambaye shi nawa ka ke biya a
shekara? Ya ce, Dirhami ɗari. Umar ya ce, mene ne sana'arka? Ya ce, ƙira da
sassaƙa da zane. Sai Umar ya ce, to in haka ne ai Dirhami ɗari ba su yi ma yawa
ba.
A daidai lokacin da Sarkin Musulmi ya ba da umurnin a rage ma Abu Lu’lu’ata
haraji, shi kuma yana can yana shirin ganin bayansa.
A safiyar 26 ga watan Dhul Hajji 23 bayan hijira Sarkin Musulmi Umar ya fito zuwa
Masallaci kamar yadda ya saba, ba tare da ɗan rakiya ko wani jami'in tsaro ba.
Da aka ta da Sallah Umar ya shiga gaba, ya daidaita sahun mutane Sannan ya
kabbarta. Gama Fatiharsa ke da wuya sai aka ji tsit, waɗanda su ke wajen
Masallaci ba su san abin da ke gudana ba. Can kuma sai aka ji muryar Abdur
Rahman ɗan Aufu yana ci gaba da Sallah, kuma ya taƙaita ta sosai.
Daga cikin Masallaci kuwa, waɗanda ke kusa sun shedi Abu Lu’lu’ata ya kutsa a
tsakanin mutane yana sukarsu da wuƙa, sai da ya soki mutane 13 kafin ya kai
zuwa ga liman, ya kuma yi masa suka shida a wurare daban – daban cikinsu har da
wata guda ɗaya a kuiɓinsa. Umar bai kai ƙasa ba sai da ya janyo Abdur Rahman ɗan
Aufu ya sanya shi a matsayinsa don ya ci gaba da ba da Sallah ga mutane.
Bamajushe ya yi gaggawa don ya gudu, amma wani daga cikin mamu ya cire mayafinsa
ya jefa masa. Da ya lura ba makawa za a kama shi sai ya soka ma kansa wuƙar a
cikinsa nan take ya ce ga garinku.
Umar ya suma a kan zafin wuƙa da ta ratsa jikinsa. Ana gama sallah shi kuma
yana farfaɗowa, sai ya tambaya, jama'a sun yi Sallah? Aka ce masa, eh. Ya ce,
babu rabo a cikin Musulunci ga wanda bai yi Sallah ba. Ya umurci Ibnu Abbas ya
duba masa wane ne ya kashe shi, da ya ji cewa bamajushe ne sai ya gode Allah a kan ba
mai Sallah ne ya kashe shi ba. Sannan ya nemi ruwa domin ya yi alwala ya sake
Sallah, amma sau uku duk lokacin da ya yi alwala sai zafin ciwo ya buge shi har
ya suma, sai a na uku ya samu ya yi sallarsa ta ƙarshe.
Da farko mutane ba su yi tsammanin Umar zai mutu ba sai da wani likita ya zo ya
haɗa wani magani ya ba shi ya sha. Da ya sha sai maganin ya fito ta inda aka
soke shi a ciki. Anan ne likitan ya umarci Sarkin Musulmi da ya yi wasiyyah.
Mutane sun soma kuka a kan jin cewa, za su yi rashin Umar, amma Umar ya hana ayi masa
kuka yana mai kafa hujja da hadisin da ya ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa,
ana azabtar da matacce da kukan rayayyu a kansa.
Sahabbai sun kewaye Sarkin Musulmi Umar suna taya shi murnar samun shahada,
suna tuna irin kyawawan abubuwan da ya gudanar a rayuwarsa, da ayyukansa a
zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da
kuma adalcinsa a cikin mulkinsa tare da yaba masa, da kuma yi masa fatar
alheri. Amma duk a cikinsu babu wanda maganarsa ta yi wa Umar daɗi kamar Ibnu
Abbas wanda bayan da ya ƙare jawabinsa Umar ya tambaye shi, za ka shede ni da
wannan a gaban Allah? Nan take Ali Ɗan Abu ɗalib ya ce ma Ibnu Abbas, amsa masa ni ma
ina tare da kai. Amma dai shi Umar kamar yadda yake cewa, fatar da nike in
tsira da ladar jihadina tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama, wannan aikin naku kuwa in na tashi
ba lada ba zunubi to, ba kome.[13]
Umar ya umurci ɗansa Abdullahi ya duba yawan bashin da ake bin sa, sai ya gaya masa
cewa, bashin ya kai Dirhami dubu tamanin da shida (Dirh. 86,000). Umar ya ce,
ka tattara abin da mu ka mallaka ka biya bashin, idan bai isa ba ka nemi
danginmu Banu Adiyyin su taimaka, idan sun kasa ka nemi ƙuraishawa kar ka wuce
su.
Sannan ya umurce shi da ya nemo masa iznin Uwar Muminai A'ishah don yana son a
rufe shi a cikin ɗakinta kusa da aminnansa guda biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da
Abubakar Siddiƙ. A'ishah ta tausaya ma Umar ta ce, na aminta na bar masa haƙƙina,
amma a da wurina ke nan da na so a rufe ni tare da mahaifina da mijina. Da Umar
ya ji wannan bayani sai ya ce da ɗansa, ka sake neman izni idan aka ɗauko
gawata za a shigar. Domin wataƙila ta ji kunyar rayuwata ne, idan ta sauya
ra'ayinta kar a damu, a kai ni maƙabartar sauran Musulmi, ba kome.
Ana haka ne wani saurayi ya shigo domin ya jajanta ma Umar ya ba shi haƙuri, ya
kuma yi masa addu'a kamar yadda sauran Musulmi su ke yi. Da ya ba da baya sai
Umar ya lura da suturarsa ta zarce haddin Shari'ah, Umar ya sa aka kira shi ya
yi masa nasiha yana mai cewa, ka ɗaga zaninka don ya fi tsafta kuma ya fi
daidai da yardar Allah.
Allahu Akbar! Haka dai zafin ciwo bai hana Umar yin aikin da ya saba na wa'azi
ba. Kuma zai gama mulkin duniyar Musulmi bayan shekaru 12 amma ana bin sa
bashin Dirh. 86,000.[14]
Da yamma ta yi, Umar ya lura da kusantowar ajalinsa sai ya umurci ɗansa da ya
saukar da kansa daga cinyarsa ya ajiye shi a kan ƙasa don ya yi tawali'u ga Maɗaukakin
Sarki. Ya ci gaba da furta kalmomi na neman gafarar Allah har mala'ikan mutuwa
ya karɓi rayuwarsa.
Umar bai bar duniya ba sai da ya shata ma Musulmi yadda za
su zaɓi wanda zai gade shi, ya kuma bar wasicci mai tsawo ga duk wanda aka zaɓa.
Za muyi magana a kan wannan idan mun zo kan zaɓen khalifa na uku in Allah ya so.
Sahabi Umar ya shugabanci musulmi tsawon shekaru goma da
wata biyar da kwana ashirin da ɗaya.
[1] Wannan shi ne asalin aikin 'yan doka (ko abinda aka sani da
suna “Patrol” na 'yan sanda a wannan zamani). Sayyiduna Abubakar ya kasance
yana tura Abdullahi ɗan Mas'ud don ya yi wannan sintiri a cikin dare. Amma a
zamanin Umar shi ne ya kan je da kansa shi kaɗai ko kuma da rakkiyar
wani bawansa mai suna Aslam ko kuma ya tafi tare da abokinsa Abdur Rahman ɗan
Auf.
[5] Faslul Khiɗab Fi Sirati Amiril Muminina Umar ɗan Khaɗɗab, na Dr. Ali Muhammad As Silabi, Darul Fajr, Alƙahira, Shafi
na 200-201.
[6] Duba: al
Tarikh, na Ya’aƙubi, (2/153) al Ɗabaƙat, na Ibnu Sa’ad
(3/213-214) da Al Kharaj, na Abu Yusuf, Shafi na 43-44.
[8] Su wane ne masoyan Ahlulbaiti, na Muhammad Mansur Ibrahim, bugun maɗaba’ar Al Ihsan, Jos,
2006, shafi na 76-79.
[11] Wani abin ban sha'awa da ban dariya shi ne yadda
manzon Sa'adu wanda ya zo da busharar nasarar da aka samu a Ƙadisiyyah ya gamu
da Umar ya na jiran saƙo a bakin gari, sai Umar ya tambaye shi, daga ina? Ya faɗa
masa. Ya ce, ina labari? Ya ce, Allah ya tarwatsa Arna. Umar ya ce, ƙara min
bayani. Ɗan saƙo ya ce, sauran bayani sai wurin Sarkin Musulmi! Haka Umar ya bi
shi suka shiga gari, Ɗan saƙo na kan dokinsa ya na suka, shi kuma
Umar ya na biye da shi ya na neman labari har suka shiga gari. Da suka isa sai
mutane suka rinƙa gai da Sarkin Musulmi! A nan ne gogan naka ya gane abokin
tafiyarsa. Sai ya faɗi ya na roƙon gafara. Umar ya ce masa, ba ka da laifi. Tashi
dai ka ba mu labari!! Duba cikakken labarin a Tarikhul Umam Wal Muluk na
Ɗabari (4/408).
[13] Wannan shi ne halin mutanen
Allah waɗanda idan suka aikata alheri sai zuciyarsu ta rinƙa kaɗawa suna tsoron
ko ba su yi daidai ba, ko Allah bai karɓa ba. Siffarsu ta zo a cikin Alƙur'ani.
Duba Suratul Mu'minun aya ta 60.
[14] Wannan bashin fa daga cikin kuɗin hukuma ne waɗanda yake
bayarwa daban ba cikin tsarin aiki ba, kamar wasu kyaututtuka da yake yi sai
yana lissafa su a takarda daban da nufin idan shi ya samu nasa ya biya har
ajali ya cim masa ga shi kuwa sun taru da dama. Masu yin sama da faɗi da amanar
Allah idan aka danƙa ma su sai su ɗauki darasi daga wannan.
DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO
Allah ya biya
ReplyDeleteAllah y qara lfy na qaru sosai, Allah y qara basira
ReplyDelete