GABATARWA

A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN. ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU!


WWW.MUMBARINMALAMAI.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA TARIHIN MUSULUNCI DA TARIHIN MALAMAN SUNNAH MAGABATA DAMA MALAMAM MU NA YANZU ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;{mumbarinmalamai@gmail.com]

Tuesday 17 December 2013

TARIHIN SAYYADINA USMAN ƊAN AFFAN RALIYALLAHU ANHU

 Usman Ɗan Affan Raliyallahu Anhu

 Wane ne Usman?
Sunansa shi ne Usman ɗan Affan Ɗan Abul Ass ɗan Umayyah ɗan Abdu Shamsi ɗan Abdu Manafi. A wajen kakansa na huɗu ne, Abdu Manaf suka haɗu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Kusancinsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta wajen uwa ya fi ƙarfi, domin kuwa shi jikan Baida'u Ummu Hakim, tawainiyar mahaifin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta wajen uwarsa. Ta nan shi taubashin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, wato ɗan gwaggonsa.

 Haifuwarsa
            An haifi Usman a garin Ɗa'if, a shekara ta Arba’in da bakwai Kafin Hijira. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da shekara shida kenan.
            Mahaifin Usman hamshaƙin attajiri ne wanda yake odar haja daga ƙasar Sham. Ya rasu ya bar ɗan nasa yana ƙarami, ya bar masa dukiya mai tarin yawa. Wannan dukiyar kuwa ta zamo dalilin ɗaukakar Usman a tsakanin ƙabilarsa da kuma sauran Larabawa, saboda ya yi amfani da ita ya saya wa kansa girma a wurin mutane ta hanyar irin karimci da halin girma da yake yi.

 Siffofinsa
            Sayyiduna Usman ya shahara da wasu siffofi guda biyu waɗanda ya yi wa kowa fintinkau a cikinsu in ban da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Waɗannan sifofin kuwa su ne; Kunya da Karimci.
            Kunyar da Usmanu yake da ita ba tana nufin rauni ko tsoro ko kasawa ba. Usmanu jarumi ne wanda ba ya sauna, amma saboda kunyarsa har Mala'iku kunyarsa su ke ji. Ya kasance ya na jin nauyin yin tsiraici ko da yana shi kaɗai.
            Game da karimcinsa kuwa har ya kai matsayin samun shedar gafarar Allah saboda yawan amfani da dukiyarsa wajen ɗaukaka addini.

3.2 Musuluntarsa
            Usman yana ɗaya daga cikin mutane goma na farko da suka musulunta.
            Da farko dai ya soma jin labarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne daga wurin innarsa (ƙanwar mahaifiyarsa) wadda take bokanci a zamanin jahiliyyah. Ita ce ta fara yi masa tayin ya musulunta, bayan da ita ta karɓi musulunci, sai ya je ya shawarci amininsa Abubakar. Abubakar kuwa ya yi amfani da wannan dama domin ya janyo shi zuwa ga Musulunci har ma ya ce masa, dattijo irinka ba ya bari ya yi jinkiri a irin wannan lamari. Amma sai Usman ya nemi a bashi dama ya ƙara yin nazari.
            A cikin haka ne wata rana Abubakar ya fito tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai suka haɗu da Usman. Abubakar ya sirranta ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abin da ya gudana tsakaninsu da Usman, ya kuma kwaɗaitar da shi a kan muhimmancin samun irin Usman a cikin wannan da'awa. Nan take Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gabata, ya kira Usman zuwa ga Musulunci in da nan take ya karɓa kiransa.

  Gudunmawarsa Ga Addini
            Usman ya kasance mutum mai arziki kamar mahaifinsa wanda ya bar masa gadon dukiya mai tarin yawa. Ya kuma shahara da kasuwanci da taimakon jama'a. Ya kuma taimaki addinin Musulunci da dukiyarsa a wurare da dama. Misali, shi kaɗai ƙashin kansa ya ɗauki nauyin Jaishul Usra wanda ya je yaƙin Tabuka a dalilin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shelanta buƙatarsa ta a tallafa ma wannan runduna. Ya kuma sayi rijiyar Ruma ya bayar da ita saboda Allah a lokacin da wani Bayahude ya ribaci fatarar ruwan sha da ake yi a Madina ya na sayar da ruwan da tsada ga Musulmi. A nan sai Usman ya share ma su waɗannan hawaye.

 Iyalansa
            Usman ya auri mata takwas (8) a rayuwarsa, Uku ne a cikinsu su kayi masa wanka. Ya kuma haifi 'ya'ya goma sha biyar (15) tara maza, shida mata.
            Bari mu soma da mafi daraja daga cikin matansa;
            Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa 'ya'yansa Ruƙayya da Ummu Kulsum auren zumunta  ya bayar da su ga Utbah da Atiƙ 'ya'yan baffansu Abu Lahabi tun kafin bayyanar Musulunci. To, da addinin Musulunci ya bayyana, Abu Lahabi ya tsananta adawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wadda ta janyo ya umurci 'ya'yansa da su saki waɗannan 'yan matan guda biyu domin ya baƙanta wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
            Bayan haka ne Sayyiduna Usman ya nemi auren Ruƙayyah aka ba shi ita. Sun yi shekaru da dama. Ta haifa masa Abdullahi, kuma a tare da ita ya yi hijirarsa ta farko zuwa Habasha, Sannan ya yi hijira da ita zuwa Madina in da ta ɗauki cikin da ya zamo ajalinta kafin a dawo daga yaƙin Badar a shekara ta biyu.
            Duk a tsawon wannan lokaci ƙanwarta Ummu Kulsum ba ta sake aure ba. Don haka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake aurar da ita ga mijin yarta. Usmanu bai daɗe tare da ita ba ita ma Allah ya karɓi ranta.
            Banda waɗannan sharifai, Usmanu ya auri Fakhitah ɗiyar Gazwan wadda ta haifa masa Abdullahi ƙarami, wanda aka sa ma sunan ɗan Ruƙayyah wanda ya rasu da shekara shida.
            Ya kuma auri Ummu Amr ɗiyar Jundub wadda ta haifa masa 'ya'ya guda biyar; Amru da Khalid da Aban da Umar da Maryam.
            Haka kuma ya auri Fatimah ɗiyar Walid wadda ta haifa masa; Said da Walid da Ummu Sa'id.
            Sannan ya auri Ummul Banin ɗiyar Uyainah wadda ta haifa masa Abdul Malik.
            Ya auri Ramlah ɗiyar Shaibah ta haifa masa A'ishah da Ummu Aban da Ummu Amr.
            Daga ƙarshe ya auri Na'ilah ɗiyar Farafisah wadda ta haifa masa Maryam.
            Waɗanda su kayi masa wanka daga cikin matan su ne; Ummul Banin da Fakhitah. Ita kuma Na'ilah ta yi shahada a tare da shi, bayan da aka ƙire mata yatsu kamar yadda zamu gani.

  Yadda Usman Ya Zamo Khalifa
            Bayan da Bamajushe ya soki Sayyiduna Umar, kuma Umar ya haƙiƙance cewa, ajalinsa ya zo sai ya fara tunanin wanda zai gade shi wajen ɗaukar wannan muhimmin nauyi da zai sauka daga kansa.
            An bai wa Umar shawarwari da dama waɗanda suka haɗa har da naɗa ɗansa Abdullahi, amma bai natsu da su ba. Daga ƙarshe sai ya kafa kwamiti na mutane shida waɗanda yake ganin sun cancanta, kuma ko wanensu yana iya ɗaukar wannan nauyi domin su zaɓi mutum ɗaya daga cikinsu. Waɗannan mutane sun haɗa da Usman da Ali da Ɗalha, da Zubair da Abdur Rahman ɗan Auf  da kuma Sa'ad Ɗan Abu Waƙƙas[1]. Ya kuma ɗibar ma su wa'adi na kwana uku don su cimma matsaya a kan mutum ɗaya daga cikinsu.
            Sannan Umar ya umurci Abu Ɗalha al Ansari ya yi ma su tsaro a lokacin da za su gudanar da tarukansu na shawarwari. Ya kuma naɗa liman na wuccin gadi, shi ne Suhaib al Rumi. Sannan ya yi izni ga ɗansa Abdullahi ya halarci taron, a matsayin ɗan kallo ba a matsayin ɗan takara ba. Ya yi haka ne kuwa domin a samu damar samar da rinjaye idan aka buƙaci yin ƙuri'a a lokacin da gida ya rabu biyu, uku sun zaɓi ɗaya, uku kuma sun zaɓi wani ɗaya na daban, sai Ibnu Umar ya kaɗa ƙuri'a domin samar da rinjaye ga ɓangare ɗaya.
            Sannan Umar ya wanke Sa'adu daga zargi, domin ya cire shi daga muƙaminsa na jagoran mayaƙa. Sai ya ce, "Idan kun naɗa Sa'adu kun yi daidai. Idan kuma ba ku naɗa shi ba, to, duk wanda aka naɗa ya ba shi wani muƙami, ku sani ban tuɓe shi don ya kasa ko don ya yi wata yaudara ba".[2]
            Bayan da aka yi jana'izar Sarkin Musulmi Umar, kwamiti ya yi taro na farko in da aka gabatar da kwamiti, aka kuma yi bitar shawarwarin da Umar ya bayar kafin cikawarsa. Daga baya Abdur Rahman ɗan Aufu ya ba da wata shawara wadda za ta sauƙaƙe aikin kwamitin. Shawarar kuwa ita ce, a fara rage yawan 'yan takara ta hanyar mutane uku su sauka su bar ma sauran ukun da suka rage.
            Nan take kuwa Zubairu ya ce ya bar ma Ali haƙƙensa[3], Ɗalha ya ce, ya bar nasa ga Usman, shi kuma Sa'adu ya ce, ya bar wa Abdur Rahman.
            Da aka yi haka, sai Abdur Rahman ya sake taƙaita hanyar, inda ya nemi ɗayansu ya janye tare da shi su bar ma ɗaya. Wato ke nan idan Usman ya janye Ali zai zama Khalifa, idan kuma Ali ya janye Usman ne zai zama. To, amma a nan sai aka yi tsit.
            Ganin haka sai Abdur Rahman ya sake nemansu da wata hanya taƙaitacciya, inda ya ce da su, ko za ku yarda ku janye hannayenku, ku bari ni in zaɓi ɗayanku, ni kuma in yi muku alƙawarin ba zan yi son rai ba? Dukansu sai su kayi na'am da wannan ra'ayi.
            Daga nan Abdur Rahman ya soma aikin neman ra'ayin jama'a domin kada ya yi amfani da ra'ayinsa shi kaɗai, ga shi ya yi alƙawarin ba zai bi son ransa ba. Ya shawarci ɗaukacin Sahabbai manyansu da ƙananansu, har ma ya rinƙa bi gida gida yana sauraren jama'a, yana neman ra'ayinsu da na iyalansu. Ya yi kwana uku yana wannan aiki.
            A yayin da kwana uku suka kusa cika, ya rage dare ɗaya wa'adin da marigayi Sarkin Musulmi Umar ya ɗiba ma su ya cika, sai Abdur Rahman ya je gidan ɗan ƙanwarsa, Miswaru ɗan Makhramata inda ya nemi ya gana da sauran membobin kwamiti, kafin daga baya ya sa a kira masa Ali da Usman. An bayyana cewa, ganawarsa da kowanensu ta ɗauki lokaci mai tsawo.
            A cikin wannan ganawar ne ya ɗauki alƙawari ga ko wanensu a kan cewa, idan shi Allah ya bai wa zai yi adalci, idan kuma ba shi Allah ya bai wa ba zai yi biyayya ba zai ta da hankali ba.
            Har zuwa wayuwar gari a rana ta uku babu wanda ya san wane ne zai zama khalifa na gaba sai Allah. Mutane dai suna biye da labarin kwamiti suna jiran su ji wanda Allah zai bai wa wannan al'amari. Sai da aka yi sallar asuba ne a wannan rana, Sannan Abdur Rahman ya miƙe a gaban jama'a ya nemi Ali da Usman su taso, ya maimaita alƙawarin da ya yi da su a gaban jama'a suka tabbatar da shi, Sannan ya miƙa hannunsa ga Usman ya yi masa mubaya'a. Don haka nan take Ali ya miƙa nasa hannun ya yi tasa mubaya'a. Sannan sauran mutane suka biyo baya. Da haka ne Usman ya zama shi ne Khalifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na uku, a ƙarshe ƙarshen watan Dhul Hajji na shekara ta Ashirin da huɗu bayan hijira [4]

 Usman Ya Fara Fuskantar Matsala Ta Farko
            Kama aikinsa ke da wuya sabon Khalifa ya fuskanci wata matsala a gabansa. Wannan matsalar kuwa ita ce, yadda zai hukunta fursunan da aka tsare kafin kama aikinsa. Wannan fursunan guda ɗaya an tsare shi ne a kan kisan da ya yi wa mutane guda uku bisa tuhumar suna da hannu wajen kashe babansa.
Ubaidullahi ɗan marigayi Umar ɗan Khaɗɗabi ya samu tabbacin cewa, Abu Lu’lu’ata ba shi kaɗai yake da hannu ba a wajen kashe babansa, domin kuwa bayan da al'amarin ya auku, Abdur Rahman ɗan Abubakar ya sheda cewa, ya gan shi tare da mutane biyu suna ganawa. Waɗannan mutanen kuwa su ne; Banasaren nan Juhainah da kuma Hurmuzan, wani basaraken farisa da ya daɗe yana faɗa da Musulunci, sojojin Musulmi suka kamo shi suka zo da shi Madina, kuma daga baya ya raya cewa ya musulunta duk da yake mutane ba su gamsu da musuluntarsa ba saboda la'akari da su kayi da irin ɗabi'unsa na kafirai.[5] Abdur Rahman ya ce, bayan da suka farga da shi suna ganawa wani makami ya faɗi a tsakaninsu wanda yake da kai biyu da maɗauri a tsakiyarsa. Da Abdur Rahman ya ba da wannan sheda sai aka diba aka tarar da wannan makamin shi ne Abu Lu'lu'a ya yi amfani da shi wajen wannan aika aikan.
Bisa ga haka ne shi kuma Ubaidullahi ya garzaya gidan waɗannan mutanen da ake tuhuma ya kuma samu sa'ar kashe su gaba ɗaya. Bayan haka kuma sai ya zarce a gidan Abu Lu’lu’ata - da yake shi ya kashe kansa - sai ya sami ƙaramar yarinyarsa wadda an ce tana furta Musulunci, ya kashe ta.
A cikin gigita da ɗimuwa Ubaidullahi ya zama wata barazana ga mutane a Madina yana cewa, sai ya kashe duk wani bare da ke garin Madina. Ya kuma yi faɗa da Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas da Usman ɗan Affan a kan sun hana shi cim ma wannan manufa. Da ƙyar aka shawo kansa bayan da Amr ɗan Ass ya samu dabarar raba shi da makamin da ke hannunsa. Sannan sai aka kama shi aka tsare shi.
Wannan duka ya faru a lokacin da babu wani Khalifa wanda zai hukunta shi. To, yanzu da yake an kafa sabuwar gwamnati wadda ta ke da ikon hukunta shi ya zama wajibi Khalifa Usman ya yi wani abu a kan wannan matsala.
Ra'ayin wasu magabata daga cikin Sahabbai, cikinsu har da sayyiduna Ali shi ne, a kashe Ubaidullahi tun da yake ya ɗauki doka a hannunsa, ya kashe waɗanda jinainansu haramtattu ne don Shari'a ba ta yi bincike ta tabbatar da laifinsu ba. To, amma wannan hukunci yana da nauyi ga al'ummar Musulmi, ganin cewa, kwana uku ke nan kacal da aka kashe wannan bawan Allah, ga kuma shuB.H.a mai ƙarfi wadda ta ke nuna hannunsu a cikin wannan ɗanyen aiki. Bugu da ƙari ma dai shi Juhainah Kirista ne, Hurmuzan kuma ba a gamsu da rayawar da yake yi cewa ya musulunta ba domin ba a ga Musulunci a aikace ba a wurinsa. Ita kuma ɗiyar Abu Lu'lu'a yarinya ce ƙarama wadda babanta ya zartas da mugun nufinsa a kan Umar. To, ya za a kashe Ubaidullahi saboda waɗannan mutane?
Khalifa Usman ya damu ainun a kan wannan al'amari. Amma shi Amr ɗan Ass ra'ayinsa shi ne, tun da Allah ya sa Ubaidullahi ya yi wannan aiki a lokacin da babu doka da oda a gari to, wajibi kawai shi ne, Sarkin Musulmi ya ba da diyyar waɗanda aka kashe gaba ɗaya. Hakan kuwa aka yi. Amma wasu riwayoyi sun nuna cewa, sai da Khalifa ya miƙa Ubaidullahi ga Ƙamazban ɗan Hurmuzan don ya yi masa ƙisasi Sannan mutanen Madina suka bi shi suna roƙon ya yafe masa har suka shawo kansa. Bayan haka ne Usmanu ya biya diyyar mutanen guda uku.

 Ayyukan Usman A Zamanin Mulkinsa
            A cikin shekaru goma sha biyu da ya yi a kan karagar mulki Sayyiduna Usman ya samu kammala dukkan ayyukan da magabacinsa Umar ya fara har ma ya ƙara da dama a kansu. Alal misali ta ɓangaren yaɗa addini Usman ya ci gaba daga in da Umar ya tsaya har sai da ya tsallake tekun Sindi. Mu na iya cewa, shekarunsa goma na farko a cike su ke da nasarori ga Musulunci da Musulmi. Sai dai abin baƙin ciki shi ne irin fitinun da suka taso a shekaru biyu na ƙarshen mulkinsa waɗanda suka mantar da manazarta tarihi duk irin nasarorin da ya samu a baya.
            Kafin mu fayyace yaƙe - yaƙen da Usman ya zartas wajen ɗaukaka addinin Musulunci da kuma maganar waɗancan fitinu da mu ka yi nuni zuwa gare su bari mu ba da haske game da wasu muhimman ayyukansa.
            A shekara ta Ashirin da shida B.H. khalifa Usman ya yanke shawarar faɗaɗa masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan ya faru ne kuwa a sanadiyyar yawaitar jama'a masallata waɗanda a wannan lokacin Masallacin ya fara yi mu su ƙaranci. Da wannan ne Usman ya zama shi ne Khalifa na farko da ya fara yalwanta Masallacin na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.[6]
            A lokacinsa ne kuma a ka sake tattara Alƙur'ani karo na biyu bayan tattarawar da aka yi a zamanin khalifa Abubakar. Banbancin nasa aikin da na magabacinsa kuwa shi ne, an tattara ƙira'oi a wuri guda, aka yi tsayayyen kwafi wanda yake iya ɗaukar sauran fuskokin ƙira'oin da suka zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sannan sai aka kwafe wannan Alƙur'anin aka rarraba shi a sauran jihohi, aka kuma janye wanda ke hannun mutane wanda suka rubuta da irin nasu salo na rubutu.[7]
            Wani abinda ya cancanci nuni a cikin ayyukan Usman shi ne, kasancewar gwamnatinsa ita ce ta fara kafa rundunar mayaƙan ruwa a Musulunci. Amma da yake wannan ya shafi aikin jihadi ne, bari mu koma kan maganar jihadin kai tsaye.

 Siyasar Usman Wajen Jihadi
            Tun da farko yana da kyau mu yi nuni ga banbancin da aka samu a tsakanin siyasar gudanar da jihadi a zamanin Umar da sabuwar siyasar da Usman ya fito da ita. A zamanin Khalifa Umar an dakatar da yaƙe - yaƙe na buɗa birane tun daga lokacin da Amr ɗan Ass ya kai hari a Tarabulus ta ƙasar Sham. Haka kuma duk ƙoƙarin da Mu'awiyah ya yi don samun izni daga Umar a lokacinsa don ya yi yaƙi ta hanyar teku bai ci nasara ba. Amma a nasa zamanin Usman ya ba da damar a ci gaba da faɗaɗa biranen Musulunci don isar da addinin Allah zuwa ga bayinsa, a ciki har da yaƙi a kan teku.[8]
            Wannan siyasar da Usman ya ɗauka kuwa duk da irin alherin da take tattare da shi, ta gamu da matsala ɗaya, ita ce, faɗaɗar daular Musulunci ya mayar da ita zuwa matsayin da ba zai yiwu a samu cikakkiyar kulawa ba ga dukkan wuraren da suke hannun Musulmi, kuma kwarjinin da Musulmi su ke da shi a idon maƙiya sai ya rage sosai saboda ganin rabuwar hankalinsu gidaje da dama.
            A dalilin haka ne garuruwa da dama da suka miƙa wuya tun da farko suka janye daga yarjeniyoyin da aka yi da su na bada jizya da makamantansu. Alal misali, a shekara ta Ashirin da biyar bayan hijira Iskandariyah ta warware alƙawarin da aka yi da ita tun zamanin Khalifa na biyu. A shekara ta Talatin da uku bayan hijira Ifriƙiya ta bi sawunta. Mutanen Jurjan kuwa, waɗanda a da sun bayyana musuluntarsu, ridda su kayi daga addinin baki ɗaya. Ita ma dai Khurasana ba a bar ta a baya ba wajen kwance alƙawari. A ɓangaren Gabas kuwa Arminiya da Azrabijan dukkansu sun kwance alƙawarin da su kayi da Huzaifa tun a zamanin Umar. To, amma fa Usmanu bai bar ko wanensu ya sha da daɗi ba domin kuwa sai da aka yi amfani da ƙarfi aka sake shimfiɗa mulkin Musulunci a waɗannan wurare gaba ɗaya.
            A shekara ta Ashirin da tara bayan hijira Usman ya ba da umurni ga gwamnoninsa da ke Khurasan da Sijistan su ci gaba da yaƙi, inda suka ci Fargana da Kabul da Isɗakhr har suka kai tekun Sindi.
A shekara ta Talatin da ɗaya bayan hijira gwamnan Masar Abdullahi ɗan Sa'ad ɗan Abu Sarh ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar runduna a wani yaƙi da aka fi sani da suna Dhatus Sawari. Shugaban Rumawa Ƙusɗanɗin ya fito da kansa a cikin jiragen ruwa fiye da ɗari biyar domin karawa da Musulmi. Gagarumar nasarar da Musulmi suka samu kuwa sai da ta tilasta Ƙusɗanɗin ya gudu da ƙafafunsa domin neman ya tsira da ransa.
            Ita ma Farisa abin da ya faru gare ta ke nan, domin sai da rundunar Abdullahi ɗan Amir ta tilasta Yazdajrid – Sarkin Farisa – ya gudu zuwa Kirman.
            A shekara ta Talatin da biyu bayan hijira Usman ya aika wasiƙa zuwa Kufa yana umurnin gwamnansa Sa'id ɗan Ass ya tayar da runduna a ƙarƙashin jagorancin Salman ɗan Rabi'ah al Bahili don ya yaƙi yankin al Bab.
            A zamanin Usman Sahabbai da yawa su kayi yaƙi. Misali, a lokacin da Mu'awiyah ya je yaƙar birnin Ƙubrus yana tare da Sahabbai irin su Ubadah ɗan Samit wanda ya tafi tare da matarsa Ummu Haram da kuma Miƙdadu ɗan Amr da Shaddadu ɗan Aus da Abu Dharril Gifari.
            A cikin yaƙin Khurasana kuwa wanda Sa'id ɗan Ass ya jagoranta akwai Hassan da Hussaini 'ya'yan Ali, da Abdullahi ɗan Abbas, da Abdullahi ɗan Umar da Abdullahi ɗan Zubair. Daga nan ne kuma suka zarce zuwa Ƙaumas, da suka buɗe ta sai suka wuce har zuwa Jurjan.
            Kafin ƙarshen mulkin Usman duka manyan dauloli na duniya sun ruguje a hannun mayaƙan Musulmi, kalmar Allah ta ɗaukaka, daga wanda ya musulunta sai wanda ya yi saranda ya aminta da Musulunci yaci gaba babu jayayya.

 Fitina Ta Kunno Kai A Zamaninsa
            Duka nasarorin da muka ambata a baya ba su sanya maƙiyan Musulunci suka karaya ba, sai dai sun canza salo a maimakon faɗa da makami wanda suka ga ya buwaye su zuwa wani salon yaƙi wanda ba ya buƙatar makami. Sun yi amfani da irin sanyin halin Khalifa Usman don ganin sun cimma gurinsu.
            Sun yi amfani da garuruwan Iraƙi, musamman Kufa, saboda ƙarancin Sahabbai a cikinsu, da yaɗuwar jahilci da yanayin tsageranci da aka san mutanen Iraƙi da shi. Da farko sun yi koken gwamnan da aka kai mu su Mughirah ɗan Shu'bah, sai Usmanu ya cire shi ya sanya ma su Sa'ad ɗan Abu Waƙƙas. Shi ma suka kai ƙararsa, ya cire shi ya sa Walid ɗan Uƙbah. Da abin yai ma su daɗi shi ma sai suka koka game da shi, Usmanu bai gaji ba ya canza ma su shi ya sanya Sa'id ɗan Ass. Daga nan shi ma bai jima ba ya samu canjin aiki aka kai ma su Abu Musa al Ash'ari, shi ma bai yi mu su daidai ba, har cewa su kayi wai bai iya Sallah ba!! Abinda su ke nufi dai kar a zauna lafiya.
            Wani salo da suka ɗauka na faɗa da gwamnatin Usman shi ne, yaɗa jita - jita. Sukan yaɗa labarai game da gwamnoninsa suna sukar su da yin zalunci da musguna ma mutane. Duk in da kaje za ka ji wannan magana, amma ba wanda zai ba ka tabbacin ta faru ko da ga mutum ɗaya. Muna iya lura cewa, ƙarancin hanyoyin sufuri da na sadarwa a wannan lokaci suna iya sanya labarin ƙarya ya zauna daram da gindinsa har tsawon lokaci kafin a samu wanda zai iya warware shi, a wannan lokacin kuma ya riga ya zaunu a cikin zukata ya aikata ɓarnar da masu makida suka shirya shi saboda ita.
            Shi kansa Usman ɗin ba su bar shi ba sai da suka zarge shi da abubuwa da dama cikinsu har da wai yana fifita 'ya'yan gidansu – Banu Umayyah – a kan sauran mutane. Hujjarsu wai ita ce, ya ba su muƙamai. Da gangan suka ƙi yin la'kari da cewa, mafi yawansu ya iske sayyiduna Umar ya naɗa su, wasu ma tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ke a kan maƙamansu, babu kuma wani dalilin da zai sa ya cire su don suna 'yan uwansa matuƙar dai sun cancanta. Kuma ma dai duka danginsa a cikin ma'aikata guda 8 ne daga jimlar ma'aikata hamsin da ɗaya (ƙasa da kashi 16% ke nan)[9]. Suka kuma rufe ido ga duk irin ƙoƙarin da Usmanu yake yi na sa ido a kan ma'aikatansa, inda ta kai ma har ya tsayar da haddi a kan wani gwamna daga cikin danginsa, ya kuma tuɓe shi daga muƙaminsa.[10]
            Sun kuma zargi Usman da cewa, ya hana bisashen talakawa su haɗu da na gwamnati a wajen kiwo.
            Abin takaici da ban dariya wai daga cikin laifuffukansa har da ya tattara Alƙur'ani ya rubuta shi a littafi ɗaya ya rarraba kofi daban daban zuwa sauran jihohi! Kuma wai tun a zamanin Manzon Allah shi bai je yaƙin Badar ba, bai yi mubaya'a da aka yi a hudaibiya ba!! Kuma da aka yi yaƙin Uhud wai yana cikin waɗanda suka ranta cikin na kare!!![11]
A kan irin waɗannan dalilai marasa tushe aka tattara jahilan Kufa da wasu daga Basrah da Masar suka tasar ma birnin Madina domin su tuntuɓi Usman su nuna masa kurakuransa ko da zai gyara.

  Dattijo Mai Halin Dattaku
            Da suka zo Madina Usman ya yi maraba da su, ya mutunta su, ya saurari dukkan ƙorafinsu, Sannan ya ba su amsar tambayoyinsu guda guda. Masu niyyar kirki daga cikinsu sai suka gamsu, suka kuma ba da shawarar su komawarsu gida.
            Bayan da suka tafi ne sai aka sake ƙulla wata wadda a wannan karon ba a buƙatar a saurari Usman, ana son ne kawai a tsige shi. Sahabbai sun yi tsaye a wannan karon suna son su yi maganinsu amma Khalifa ya hana su. Wasu daga cikin magabatan Sahabbai kamar Ali da Ɗalhah da Muhammad ɗan Maslamah sun samu tofa albarkacin bakinsu cikin wannan sha'ani. Shi kuma Usman ya karɓi dukkan bukatunsu, ciki har da cire wasu gwamnoni da sauya hanyoyin rabon arzikin ƙasa. Suka nuna sun gamsu, suka kama hanyar tafiyarsu.[12]
            'Yan tawaye dai sun bayyana komawa gida. Amma shugabanninsu na can suna shirya wata maƙarƙashiya. Abin da suka shirya shi ne, sun rubuta takarda da sunan Sayyiduna Usman wai yana umurni in sun koma garuruwansu a kashe su. Nan take wannan takarda ta yaɗu a cikin rundunar jahillai, aka ce wai an kama wani masinja da ita. Maganar komawa gida ta ƙare kenan. Saboda haka sai suka dawo suka kewaye gidan Khalifa suka neme shi da ya fito ya kare kansa.
            Da suka dawo Madina kuma sai suka nemi Ali ya raka su zuwa wajen Sarkin Musulmi domin su kafa hujja a kan cin amanar da suka ce ya yi musu. Ali ya ce ba zai je ba. Sai suka ce, to, me yasa ka aiko mana da takarda? Ali ya ce, shi bai san wannan Magana ba. Ita ma Nana A’ishah sun raya cewa, ta aika masu takarda a kan su zo su yi fito na fito da Usman, su kashe shi, amma ita ma ta fito a bainar jama’a ta ƙaryata su. Wannan yana nuna kisisina ce da yaudara ta shugabannin ‘yan tawaye, waɗanda ke nuna ma mabiyansu cewa, abin da suke yi suna tare da goyon bayan Sahabbai.
Sarkin Musulmi Usmanu ya yi rantsuwa a kan bai san da wannan takarda ba. Amma jahilai suka ƙaryata shi. Ya neme su da su kafa masa shaidu a kan gaskiyar wannan takarda sai suka amsa masa da cewa, ai kai yanzu munafiki ne.[13] Abin da muke so kawai ka yi murabus daga muƙamin Sarkin Musulmi.
            Usman yana biye da sawun wasiccin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Don haka bai sauka daga muƙaminsa ba. Kuma duk ƙoƙarin da Sahabbai su kayi na ganin ya ba su damar su fatattaki 'yan tawayen bai ci nasara ba. Ya nace a kan cewa, ba zai bari a zubar da jinin kowa ba a kansa.[14]
            Daga bisani 'yan tawayen sun hana Usman fita Masallaci har sai ya miƙa takardar ajiye aikinsa. A maimakonsa sai suka naɗa wani sabon liman daga cikinsu shi ne, Gafiƙi ɗan Amru. Daga bisani kuma suka hana a kai masa ruwan sha a cikin gida. Sai da Sayyiduna Ali ya yi musu jan ido sosai sannan ya samu canza wannan yanayi. Uwar Muminai Ummu Habibah ita ma ta gwada kai ma Sarkin Musulmi ruwa amma da ƙyar ta tsira daga hannunsu.
Haka dai aka ci gaba, Usman bai yi murabus ba, su kuma 'yan tawayen ba su ƙyale shi ba. Da al'amarin ya kai wani matsayi sai 'ya'yan Sahabbai Hassan da Hussaini da Muhammad ɗan Ɗalhah da Abdullahi ɗan Zubair da makamantansu suka taru suka je gidan Usman suna neman ya bar su da waɗannan shaƙiyyai. Usman ya yi rantsuwa da Allah a kan ba za a yi yaƙi saboda shi a cikin Madina a keta alfarmarta ba. Sai suka yanke shawarar ci gaba da zama a ƙofar gidansa suna gadinsa.
            Duka wannan ya faru a cikin watan Dhul Ƙi'da na shekara ta Talatin da biyar bayan hijira. Da lokacin tafiya aikin hajji ya yi, sai Usman ya kira Abdullahi ɗan Abbas wanda ke cikin masu tsaronsa ya yi masa Amirul Hajji na wannan shekara. Ibnu Abbas bai so haka ɗin ba saboda ya fi son ya ci gaba da fakon gidan Sarkin Musulmi har yadda hali yayyi. Musulmi suka tafi aikin hajji suna cike da fargaba game da abin da baya ka iya haifuwa a Madina.
Labarin abin da ake ciki a Madina ya kai ko ina. Dukkan gwamnoni sun shirya rundunoni domin su kai ɗauki a can. Tuni Mu'awiyah – gwamnan Sham – ya aiko da tasa runduna.

 Wane Ne Ummul Haba’isin Wannan Fitina?
            Wataƙila mai karatu anan zai buƙaci sanin amsar wannan tambaya, ita ce, wane ne jagoran wannan fitina, wanda ya nace akan hasa wutarta? Kuma don me yake yin haka?
            Amsar wannan tambaya tana a cikin mafi yawan littafan tarihi, na malaman Sunnah da na Shi’ah baki ɗaya.[15]
            Kamar yadda muka faɗa a baya dai, arna tuni sun haƙiƙance Musulunci ya gama galaba akansu. Kuma ta hanyar makami basu da wata fatar sake cin nasara akansa. Don haka ba abinda ya rage musu sai hanyar yaudara. Anan ne wani bayahude mai suna Abdullahi ɗan Saba’i ya yi musu wannan aiki inda ya tattara nasa ya nasa ya tare a ƙasar Musulunci yana mai raya cewa, ya amshi kiran na Musulunci. Shi ne kuma ya jagoranci wawaye da jahilan da suka yi duk wata aika aika a zamanin khalifa Usman. Bayan gamawa da wannan gwamnati kuwa ya koma bayan khalifa na huɗu ya ci gaba da dagula al’amurra har in da yaƙin basasa ya auku a tsakanin Musulmi kamar yadda zamu gani anan gaba. Haka kuma shi ne ya ƙago ƙungiyar Shi’ah da sunan kariyar Ali Raliyallahu Anhu. Daga bisani abin ya wuce nan ya koma maganar kariyar iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga wai waɗanda suke gaba da su, kuma waɗanda suka danne haƙƙensu. Yana nufin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama!.

3.9 Usman Ya Yi Shahada                      
Da 'yan tawaye suka samu labarin rundunonin da su ke bisa hanya har ma rundunar Sham ta kawo Wadil Ƙura kusa da Madina sai suka nemi su kutsa cikin gidan Usman, 'ya'yan Sahabbai suka hana su. Sai suka zagaya ta baya a tsakanin gidan Sarkin Musulmi da gidan maƙwabcinsa Umaru ɗan Hazmi suka ƙona ƙofar gidan suka kutsa a ciki.
            Sun shiga a cikin gidan suka sami Usman yana karatun Alƙur'ani. Nan take sai limaminsu Gafiƙi, ya kai duka da wani ƙarfe a kansa. Matarsa Na'ilatu ta yi kukan kura a cikinsu tana kariyar mijinta. Tana ce masu ya zaku kashe mutumin da ya ke witirin raka'a ɗaya da Alƙur'ani gaba ɗaya?[16] Nan take Ƙutairatu ya kai mata sara inda ya katse yatsun hannunta. Wasu mutane biyu su ma sun kai ɗoki a kan Khalifa, su ne, Sudanu ɗan Humranu da Kinanata ɗan Bishru al Tujibi. Wani kuma daga cikinsu mai suna Amru ɗan Hamiƙu shi ne ya ƙarasa kashe shi.
            A wannan lokaci barorin da ke cikin gidan kawai suka ganar ma idonsu abin da ake ciki.  Ɗaya daga cikinsu har ya kashe Sudanu, shi kuma Ƙutairatu ya kashe shi, Sannan ya gamu da gamonsa a hannun wani daga cikin barorin na Sarkin Musulmi. Bayan haka suka washe duk abin da ke cikin gidan. Suka garzaya Baitul Mali suka yaye dukiyar gwamnati.
            Allahu Akbar! Wannan shi ne ƙarshen tarihin Sarkin Musulmi Usman wanda ya yi shahada a ranar 18 ga watan Dhul Hajji na shekara ta Talatin da biyar bayan hijira. Ya kuma yi sarauta ta tsawon shekaru Goma sha biyu ba kwana goma sha biyu. Ya rasu yana da shekaru Tamanin da biyu a duniya.
           


[1] Biyu na farko dangin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ta wajen mahaifinsa. Biyu na tsakiyar kuma danginsa ne ta wajen mahaifiyarsa. Sauran biyun kuwa fitattun musulmi ne da Annabi ya ba su sheda game da sha'anin jagoranci a wannan al'umma. Dukkansu sun cancanta. Wanda duk Allah ya ba a cikinsu ba matsala. Daga cikin mutane goma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yiwa bushara da aljanna mutum ɗaya ne ya rage wanda Umar bai shigar da shi cikin kwamitin ba, shi ne Sa’idu ɗan Zaid. Umar ya ƙi sanya shi a cikinsu saboda dangantakar jini da ke tsakaninsu.
[2] Duba Sahihul Bukhari tare da sharhinsa Fathul Bari (7/59-62) hadisi na 3700.
[3] Nan gaba za mu ga wasu abubuwa sun faru a tsakanin Zubair da Ali. Kar mu manta da wannan don mu san ba ƙiyayya a tsakaninsu. Ya za a yi kuwa Zubairu ya ƙi Ali alhalin ya san matsayinsa a addini ga shi kuma taubashinsa ne, ɗan gwoggonsa Safiyyah!
[4] Duk a khalifofi babu wanda ya samu goyon bayan da ya kai na Sayyiduna Usman a wajen naɗinsa. Don haka ne malamai ke cewa, ijma'i ya haɗu a kan khalifancinsa kamar yadda za mu lura daga abin da ya gudana. Duba littafin As Sunnah,  na Imam Al Khallal, shafi na 320.
[5] Ƙari a kan wannan ma shi ne, bai musulunta ba bayan zuwansa wurin Umar sai da ya bi hanyoyi na yaudara suka kasa fitar da shi. Sannan Umar ya rantse zai kashe shi, ganin haka sai ya musulunta don kare kansa. Duba cikakken labarin a Tarikh na Ɗabari, (5/66) da kuma Al Mukhtasar Fi Akhbaril Bashar, na Abul Fida', za ka same shi a duniyar gizo a kan wannan layin http://www.alwarraƙ.com.
[6] Al Ibar Fi Khabari Man Gabar, na Dhahabi, ana samunsa a http://www.alwarraƙ.com, (1/5).
[7] A nan banbancin yanayin rubutu ne aka kawar wanda idan ya ci gaba zai iya faɗaɗa ya haifar da wasu ƙira'oi waɗanda ba Annabi ne ya karantar da su ba. A yanzu dai a duniya ba wani kofi na Alƙur'ani face daga wancan na Usman ne aka kwafo shi. Wannan shi ya sa ake cewa Al Mushaf Al Usmani.
[8] Kar a manta cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bada busharar cewa, al’ummarsa zata yi yaƙi a kan teku, ya nuna alfahari da su mayaƙan, kuma ya ce, runduna ta farko da za ta yi wannan yaƙi ‘yan aljanna ne. Duba Fathul Bari (6/22). Sayyiduna Mu’awiyah na cikin waɗanda suka samu wannan falala domin da shi aka yi yaƙin.
[9]  Duba littafin Nazaratun Hadi'ah ma'a Ashriɗati ƙisasin minat tarikh al Islami na Khalid al Gais, Darul Andalus al Khadra', Jiddah, Saudi Arabia, Bugun Farko, Shafi na 19-23.
[10]  Wannan gwamnan shi ne Walidu ɗan Uƙbata wanda wasu talakawansa suka tuhumce shi da shan giya. Sayyiduna Usman ya shawarci Ali ɗan Abu Ɗalib sai ya bada shawarar ayi masa haddi, nan take Usman ya aminta da shawararsa, ya kuma waƙilta shi ga wannan aiki. Anan ne Ali ya nemi ɗansa Al Hassan da ya zartar da wannan hukunci, sai Al Hassan yace, baba ina ruwanka da shi? Shi kuwa ya yi haka ne don rashin gamsuwa da hukuncin saboda shedu biyu ba su cika ba don ɗayan cewa ya yi ya gan shi ya na amaye ta amma bai ga ya sha ba. Anan ne Ali ya sa ɗan ɗan uwansa Ja’afaru ɗan Abu Ɗalib, Abdullahi, ya zartar da wannan haddi akan Walid. Sannan Usman ya tuɓe shi daga gwamna. Duba Sahihu Muslim, Kitabul Hudud, Babin haddin shan giya, Hadisi na 3220.
[11]  Duba cikakkiyar amsa a cikin Al Awasim Wal Ƙawasim, tahaƙiƙin Muhibbuddin Al Khaɗib, Bugun Darul Ma’arifah, na Farko, Morocco, 1406/1986, Shafi na 54-109.
[12] Mai karatu zai yi mamaki me ya sa Usman yake ta wannan haƙuri da su, yana biye ma buƙatunsu? Don me ba zai bari Sahabbai su gama da su ba? Amsa ita ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya gaya ma Usman faruwar waɗannan abubuwa, kuma ya aza shi ga shawarwari waɗanda su ne yake a kansu.
[13] Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama su ne ya kira munafukai a in da ya ce da Usman: "Idan Allah ya jiɓintar da kai wannan al'amari a wata rana, sai munafukai suka nemi ka tuɓe rigar da Allah ya sanya maka, kar ka tuɓe ta" Duba Sahihu Sunan Ibn Majah, na Albani, (1/25).
[14]  A nan ma mai karatu zai so ya san hikimar da ta sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana Usman yin murabus idan haka ta faru. Abin da wasu masu nazari suka hango shi ne, waɗannan fitinannun ba fa da Usman su ke faɗa ba, kuma ba kashe shi ne gurinsu ba. Al'ummar musulmi ce su ke so su hargitsa, su haddasa fitina a tsakanin jama'arta, su kawar da kwarjinin masarautarta. Idan kuwa aka buɗe ƙofar duk sarkin da bai yi ma su daɗi ba su kewaye gidansa su ce ya yi murabus to ai babu sauran wata alfarma ga Sarkin Musulmi. Duba Littafin Tahƙiƙu Mawaƙifis Sahabah fil Fitnah, na Furofesa Muhammad Amhazun, Shafi na 343 -  346.
[15]  Duba alal misali, Al Maƙalat Wal Firaƙ na Ƙummi, shafi na 20 da Firaƙus Shi’ah na Nubakhti, shafi na 22 da Tahdhibul Ahkam na Ɗusi (2/322) da Kitabur Rijal na Hilli, shafi na 469 da Al Bahruz Zakkhar na Ahmad Al Murtadha, shafi na 39, da Masa’ilul Imamah na Anbari, shafi na 22-23, da Tanƙihul Maƙal na Mamaƙani (2/183-184) dukkansu daga Malaman Shi’ah. Amma game da Malaman Sunnah sai ka duba sunayensu a littafin Taudhihun Naba’ An Mu’assisis Shi’ah Abdillahi Bin Saba na Abul Hassan Ar Razihi, bugun Darul Iman, Iskandariyyah, Misra, ba kwanan wata, shafi na 85-101.
[16] Duba Tarikhul Madinah, na Umar bin Shabbah, (2/1272).


DAGA LITTAFIN ƘADDARA TARIGA FATA NA SHEIK Dr. MANSIR SOKOTO

No comments:

Post a Comment