Ali ɗan Abu Ɗalib Raliyallahu Anhu
Sunansa da
Asalinsa
Sunansa Ali ɗan Abu Ɗalib ɗan Abdul Muɗɗalib ɗan Hashim. Shi ne ƙanin Manzon Allah, domin kakansu ɗaya shi ne, Abdul Muɗɗalib.
Mahaifiyarsa
kuwa ita ce Fatima ɗiyar Asad ɗan Hashim wadda ita ma ta gama kaka da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama.
Tashinsa
An haifi Ali a shekara ta ashirin
da uku kafin Hijira, an aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a
lokacin Ali yana da shekara goma. Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama ya
girmi Ali da shekaru talatin. Kuma kamar yadda mahaifinsa ya riƙa Manzon Allah ya kula da shi, shi ma Manzon Allah
ya riƙa Ali ya kula da shi.
Darajojinsa
Kasancewar Ali ya tashi a hannun Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tun ba a aiko shi ba, ya bai wa Ali
damar ya shaƙi ƙamshin Musulunci tun a rana ta farko. Ali kuwa bai
yi wata wata ba ya amsa kiran Allah a hannun yayansa kuma mai gidansa. Don haka
Ali shi ne mutum na farko da ya karɓi addinin Musulunci
bayan matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Nana khadijah.
Duk
da kasancewarsa yaro ne ƙarami, amma Ali
ya ba da gudunmawa wajen kafuwar Musulunci. A tare da shi aka yi Bai'atul Aƙaba, wadda Allah ya ce, ya yarda da
waɗanda su kayi ta. Haka kuma ya kwanta a kan shimfiɗar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a
lokacin da zai yi hijira.
A
yaƙin farko da aka yi tsakanin Musulmi da Mushrikai,
yaƙin Badar, Ali ya yi fito na fito da
babban arnen nan Walid ɗan Utbah kuma ya
kashe shi. Sannan ya taimaka ma baffansa Hamza wajen kashe mahaifin wancan na
farkon, Utbah ɗan Rabi'ah. A yaƙin khandaƙ kuma shi ya yi
fito na fito da Amru ɗan wuddu al
Amiri
wanda jarumawa ke fargaban karawa da shi, kuma Ali ya halaka shi. A ranar yaƙin Khaibar kuma shi aka bai wa tuta bayan da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi alƙawarin
bayar da ita ga wanda ya siffanta da cewa, yana son Allah da Manzo kuma Allah
da Manzo na sonsa.
Ali
ya auri 'yar Manzon Allah, Fatimah, wadda bai yi ma ta kishiya ba har Allah ya
karɓi rayuwarta.
Ali
shi ne ya zamo gwamnan Madina a lokacin da Manzon Allah ya fita da mafi yawan Sahabbai
zuwa yaƙin Tabuka. Wannan ya sanya Ali
bai ji daɗi ba don rashin kasancewa tare da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da manyan Sahabbai. Amma Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwantar da hankalinsa da cewa,
matsayinsa a wurin Manzo ya yi daidai da na Annabi Haruna ga yayansa Musa, duk
da yake shi Manzon Allah ba wani Annabi a bayansa.
Ali
ya wakilci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wajen isar da saƙon Suratut Taubah zuwa ga kafiran Makka. Ya kuma je
ne a ƙarƙashin jagorancin
Sayyiduna Abubakar.
Matsayin Ali a zamanin Khalifofi
Ali
ya yi mubaya'a ga Abubakar tun da farko kamar yadda ya gabata a baya. Amma bai
lizimci fadar Sarkin Musulmi Abubakar ba sai bayan rasuwar uwar gidansa Fatimah,
wadda ya kasance yana jinyarta tsawon watanni ukku ko kuma shida.
Ya
halarci yaƙin da Abubakar ya yi da murtaddai
(waɗanda suka fita Musulunci bayan rasuwar Manzon
Allah) da Annabawan ƙarya, da kuma waɗanda suka ce ba sauran ba da Zakka tun daga wafatin Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. A wurin yaƙar musailamatu ne wanda Khalid ɗan Walid ya jagoranta a zamanin Abubakar, Ali ya samu
gajiyar matarsa khaulatu ɗiyar Ja'afar ‘yar
ƙabilar Banu Hanafi, wadda ta haifa masa Muhammad al
Akbar, wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah.
A
zamanin Sarkin Musulmi Umar kuwa, Ali ya karɓi muƙamin alƙalanci, ya kuma
yi gwamna a Madina a lokuta da dama.[1]
Daga
baya kuma, surukuta ta shiga tsakaninsa da Sarki Umar ɗan Khaɗɗabi a lokacin da
'yarsa, Ummu Kulsum, wadda Nana Fatima ta rasu ta barta tana ƙarama ta soma girma, sai Sayyiduna Umar ya yi
sha'awar aurenta. Ali kuwa bai yi wata wata ba ya ɗaura masa aure da ita. Wannan karimci na Ali ya ƙarfafa danƙon zumunci da ƙauna a tsakaninsa da Sarki mai ci a wannan lokaci,
wanda ya bayyana cewa, ba ya da fata kamar ya haɗa
zuri'a da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abin da bai tabbata
ba a surukutarsa ta farko da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama,
domin kuwa 'yarsa Hafsah ba ta haifu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ɗin ba. Wannan
gurin nasa kuwa ya cika domin sharifiya Ummu Kulsum ta haifa masa 'ya'ya guda biyu, namiji da mace
waɗanda ya sa ma su suna Zaidu da Ruƙayyah.
A
lokacin rasuwarsa, Umar ya kafa wani kwamiti na mutum shida waɗanda ya ɗora ma su
alhakin zaɓen sabon Sarki daga cikinsu. Ali yana
daga cikin membobin wannan kwamiti. Ga dukkan alamu Umar ya yi sha'awar a naɗa Ali, amma tsentseninsa da mu ka sani bai bar shi
ya ayyana shi ba, wataƙila saboda
surukutar da ke tsakaninsu, sai ya bar Musulmi su zaɓa da kansu, kuma a cikin ikon Allah zaɓin bai faɗa a kan Ali ba a wannan
lokaci.[2]
Ba za
mu yi mamakin Umar ya yi sha'awar Ali ya gade shi ba domin sun fi kama da juna
a ɗabi'unsu da tsarin rayuwarsu kamar yadda
Usman ya fi kama da Abubakar a wajen sanyin
halinsa da jin kunyarsa.
Da
aka zaɓi Usman kuwa, Ali shi ne mutum na
farko da ya yi masa mubaya'a kamar yadda mu ka gani a baya. Ya kasance a
matsayin wazirinsa mai ba shi shawara ko da yaushe kamar yadda yake yi a
zamanin Umar.
Mun
kuma riga mun
ji irin gudunmawar da Sayyiduna Ali ya bayar wajen kariyar Usman kafin Allah ya
ƙaddari aukuwar abin da ya alƙawarta na shahadarsa a hannun 'yan tawaye, mutanen
Iraƙi.
Ali ya zama Sarkin Musulmi
Bayan
da ajali ya cika da Sarkin Musulmi Usman ɗan Affan,
al'amurra duk sun rikice a birnin Madina. Ga shi kuma ba'a dawo daga aikin
hajji ba wanda Sahabbai da dama suna can, sai 'yan tawaye suka fara tunanin
hanyar da zata fisshe su. Abu na farko da su kayi tunani a kansa kuwa shi ne,
su taka rawa wajen naɗa khalifa na
gaba. A kan
haka sun zagaya wurin Ali da Ɗalhah da Zubairu
da Ibnu Umar, amma duka sai suka yi biris da su, ko wanensu ya ƙi amincewa da ya karɓi
mubaya'arsu domin ba su ne ya kamata su yi wannan ba.[3]
Haka
dai al'amari ya dagule ma su, suka rasa wanda zai fid da su daga wannan rami da
suka auka, ga kuma alhazzai suna kan
hanya sun kusa isowa Madina, sai su kayi barazanar kashe dukkan waɗanda suka nema da wannan al'amari suka ƙiya ma su. Anan ne fa ya zama dole Ali ya karɓi wannan aiki bisa ga shawarar wasu Sahabbai da suka
lura al'amarin zai ida caɓewa ga baki ɗaya.
An
dai samu natsuwa kaɗan da yin
mubaya'a ga Ali a Madina. Haka kuma bayan mutanen Madina, daga Iraƙi ma (Biranen Kufa da Basrah) in da can ne mafi
yawan 'yan tawayen suka fito, an aiko da mubaya'a, haka ma mafi yawan sojojin Musulmi
waɗanda su ke a wuraren yaƙi sun aiko mubaya'arsu.
Labarin
kisan gilar da aka yi wa Usman ya ci gaba da yaɗuwa
a sauran birane, yana tafiya lokaci ɗaya da labarin
naɗa sabon Khalifa, shi ne Ali. Tambayar da
mafi yawa su ke fara yi ita ce, to, ina 'yan tawayen? Me Ali ya yi game da su
da aka naɗa shi? Wace irin rawa ya taka yana
a Madina a lokacin faruwar wannan lamari?. Rashin samun gamsasshiyar amsa ga wanda
bai san haƙiƙanin
yadda abin ya faru ba ta sanya mutane da dama daga sauran garuruwa kamar Misra
da Yaman da Makka duk ba su yi mubaya'a ba.
Amma waɗanda suka fi kowa adawa da wannan mubaya'a su ne
mutanen Sham[4].
Dalili kuwa shi ne, Sham tana ƙarƙashin riƙon Mu'awiyah ne ɗan Abu Sufyan wanda ɗan
uwa ne na jini ga marigayi khalifa Usman. Mu'awiyah kuwa mutum ne mai farin
jini a wurin talakawansa. Ga shi kuma nan take bayan faruwar wannan ɗanyen aiki aka je da rigar Sayyiduna Usman wadda
take cike da jininsa zuwa wurin Mu'awiyah a cikin yanayi wanda ke sa tausai da
takaici a kan
zaluntar sa da aka yi.
Mu'awiyah ya yi huɗuba mai gauni a kan wannan lamari, kuma ya nemi goyon bayan
talakawansa a kan
ramuwa da ɗaukar fansa a kan 'yan ta'adda. Mutanen Sham kuwa suka
amsa kiransa ƙwansu da
kwarkwatarsu. Har ma matan aure sai da suka ɗauki alwashi ba
za su sake ɗaukar janaba ba
sai an ga ƙarshen 'yan ta'adda.
Ali ya kafa sabuwar gwamnati
Ikon Allah! Duk wannan abin da ke
gudana shi Ali yana can Madina yana yanke shawarar sabunta gwamnati wadda kuma
babu Mu'awiyah a cikinta, kamar yadda babu sauran mafi yawan gwamnoni waɗanda ya gada daga gwamnatin da ta gabata. Da Allah
ya so wannan abu ya zo da sauƙi to, da Ali ya
dakata kamar yadda ƙaninsa Ibnu
Abbas ya nuna masa, ya bari
sai mutanen Sham sun miƙa wuya, idan
tafiya ta yi tafiya sannan sai ya canza Mu'awiyah. To, amma ƙaddara ta riga
fata, domin kuwa ba haka Mabuwayin Sarki ya hukunta ba. Don haka sai Ali ya
zartas da abinda ya yi niyya.
A Makka kuwa, Uwar Muminai Nana
A'ishah tana can ba ta baro ba, domin ta nemi iznin Khalifa Usman a kan zata yi
aikin hajji, daga can ne kuma labarin yadda juyin mulki ya kaya ya ishe ta. Tana
cikin juyayin wannan lamari sai ga Ɗalha da Zubairu
waɗanda suka sulale daga Madina bayan sun
yi wa Ali mubaya'a kuma a asirce, sun nemi Ali ya bari su nemo goyon bayan jama'a daga sauran
garuruwa don a gama da 'yan ta'adda sai Ali ya ce, su dakata. Daga nan sai suka
nuna masa suna da buƙatar fita zuwa
Makka amma bai san abin dasu ke nufi ba.[5]
Shawarwari da tuntuɓar juna sun ci gaba a tsakanin jama'a a garin Makka
bayan da ya tabbata cewa dai mafi yawan 'yan tawayen har sun fice daga Madina
sun nufi garuruwansu. Ɗalha da Zubairu
sun ci nasarar shawo kan
Nana A'ishah don ta fita tare da su ta ƙarfafi jama'a a kan babban jihadin da su
ke son yi a kan
'yan ta'adda. Kuma an yanke shawarar a nemo agaji daga Iraƙi, a kuma fara da ‘yan ta’adda da ke can.
Da suka kama
hanyar zuwa Iraƙi, kafin su je
Basrah sun shuɗa da wani tafki
wanda aka ambaci sunansa al Hau'ab. Jin an faɗi sunansa ke da wuya sai Nana A'ishah ta yi shirin
komawa domin ta taɓa jin Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama yana ce ma matansa: wacce ce a cikinku zata ji kukan
karnukan Hau'ab, ta shiga gumuzun yaƙi har a kashe
mutane a dama da hagunta, kuma ta tsira da ƙyar bayan ta
kusa ta halaka?
Al'amarin da Rabbus Samawati ya
hukunta ba wurin kauce masa. Don haka sai Ɗalhah da Zubairu
suka hana ta komawa, suka ce da ita, ba ruwanki da yaƙi, abin da mu ke so kawai shi ne, 'ya'yanki Musulmi
su gan ki, su san kina da goyon bayan wannan lamari don su samu kuzarin ba da
himma a cikinsa. Nana A’isha sam bata gamsu da haka ba, amma ƙaddara ta riga
fata.[6]
4.5 Yaƙin Basasar Raƙumi
Matsayin Ɗalha da Zubairu
Tun da farko kamar yadda muka gani, Ɗalhah da Zubairu sun nemi Sayyiduna Ali ya ba su dama domin su je Basrah
da Kufa su nemo agajin mayaƙa saboda a
hukunta ‘yan tawaye kafin su bar Madina, amma Ali yana ganin lokacin yin haka
bai yi ba.
Daga baya sai suka neme shi iznin su
je Makka kamar da nufin yin Umrah. Da suka je Makka sai ra’ayinsu ya haɗu da ra’ayin Nana A’ishah a kan nemo taimako domin a tunkari waɗannan ‘yan ta’adda. Da haka ne suka sami damar fita
zuwa Basrah tare da Uwar Muminai a daidai lokacin da Sarkin Musulmi Ali yake
cikin shirin fita zuwa Sham domin ya tilasta mutanenta a kan yi masa mubaya’a
da su da jagoransu Mu'awiyah. Saboda ya aika sabon gwamnansa Sahlu ɗan Hunaifu zuwa
can an koro shi.[7]
A lokacin da labarin fitowar su
Zubairu ya kai ga Sarkin Musulmi Ali sai nan take ya canza shawara daga tafiya
Sham ya tasar ma hanyarsu domin ya dakatar da su daga zuwa Basrah. Saboda bai
kamata su yi gabansu da sha’ani irin wannan ba tare da sun tuntuɓi shugaba ba kuma sun tafi a kan umurninsa. Nufinsa idan ya haɗu da su a kan
hanya sai ya dakatar da su tun ba su kai ba. Amma ina! ƙaddara ta riga
fata. Kafin ya farga tuni sun kai Basrah har sun fara zartas da abinda ya kai
su.
Daga ɓangaren gwamnan Basrah kuwa, Usmanu ɗan Hunaif Raliyallahu Anhu aikawa ya yi da wakilai biyu Imrana ɗan Hussaini da Abul Aswad al Du’ali domin su tattauna
da jagororin mutanen Makka don su ji abin da ke tafe da su. Dukkansu sun faɗi cewa, sun zo ne suna neman agaji domin faɗa da ‘yan ta’adda waɗanda suka kashe Khalifan Manzon Allah a cikin gari mai daraja, a kuma
wata mai alfarma.
Gwamna ya fahimci lalle akwai tashin
hankali domin kuwa kafin isowar su Ɗalha sai da ya
tara mutane a Masallaci domin ya yi shawara da su a kan matakin da zai ɗauka, sai wani mutum ya yi katsalandan kafin gwamnan ya
ce komai, ya ce, Ya ku jama’a waɗannan mutane
suna neman ɗaukar fansar Usmanu ne, mu kuma ba mu muka kashe shi
ba. Idan ko suna neman aminci ne to, ya suka baro garin da ko tsuntsu ba’a
firgitawa a cikinsa? Nan take wani ya tashi ya ce masa, Ai sun zo ne domin mu
taimaka musu a kan waɗanda su kayi
kisa ko suna a cikinmu ko ba su a cikinmu. Sai kawai mutane suka fara jifarsa.
Duka wannan ya faru a lokacin da labari ya game gari cewa, rundunar Makka tana
bisa hanya amma tukuna ba su riga
suka iso ba.
Da jama’ar Ɗalha suka iso Basrah ba su shiga a cikin gari ba sai da suka yada zango a
wani wuri da ake kira Mirbad in
da masu goyon bayan tafiyarsu suka je suka same su. Shi ma kuma gwamnan sai ya
tafi da tawagarsa domin ya tattauna da su.
A lokacin da suka isa, Ɗalhah da Zubairu
sun yi jawabai suna masu bayyana takaici a kan abinda ya faru a Madina, suka kwaɗaitar da mutane a kan ɗaukar fansa. Amma wasu mutane da ke cikin tawagar ɗan Hunaif – gwamnan Basrah – sun mai da martani a kansu.
Nana A’ishah ma sai da ta sa bakinta. Nan take
sai aka fara jefe jefe, wasu kuma daga cikin mutanen Basrah suka ƙara runtuma cikin rundunar Uwar Muminai. Daga baya dai
hankali ya kwanta.
Ba a watse daga wannan haɗuwar ba sai ɗaya daga cikin
‘yan tawaye waɗanda suka je wurin kashe Khalifa Usman ana ce da shi
Hakimu ɗan Jabalah wanda kuma shi ke jagorantar ɓangaren mahaya dawakai a rundunar gwamnatin Basrah ya
yi ƙoƙarin tada faɗa. Duk ƙoƙarin da Nana A’isha ta yi a kan ganin an kwantar da hankali bai yi
amfani ba, domin kuwa sai da wannan taƙadarin ya hasa
wutar yaƙi. An dai wuni ana gwabzawa a tsakanin rundunonin guda
biyu, kuma aka wayi gari aka ci gaba, aka yi hasarar rayuka da dama daga ko
wane ɓangare, aka kuma jikkata mutane da dama.
A lokacin da rundunar Makka ta samu
sa’a sai suka kama gwamna a hannu, amma Nana
Aishah ta sa baki aka sake shi, sannan ta yi umurni aka rinƙa kamo waɗanda aka sani
cikin ‘yan ta’adda mutanen Basrah, aka kuma kashe da yawa daga cikinsu. Sai dai
wasu kam sun gagara domin danginsu sun fito sun taimaka masu sun basu kariya.
Misali wani mashahuri a cikinsu ana ce masa Hurƙusu ɗan Zuhairu, mutum dubu shida suka fito daga cikin ƙabilarsa - Banu Sa’ad – don kariyarsa shi kaɗai. Abin da Ali ya hango ya fara tabbata kenan. Amma
dai shi Alin yana kan
hanya bai iso ba tukuna.
Da Sarkin Musulmi Ali ya kusanto Basrah
sai ya aika wani jarumi mai suna Ƙa’aƙa’u ɗan Amru don ya
kira Ɗalha da Zubairu zuwa ga ɗa’a da dawowa ƙarƙashin shugaba saboda a haɗa kan
jama’a. Ga yadda tattaunawarsu ta kasance:
Isowar Ƙa’aƙa’u ke da wuya sai ya tunkari Uwar Muminai ya tambaye
ta abinda ya fito da ita, sai ta gaya
masa cewa, ta fito ne domin ta yi gyara a tsakanin mutane. Sai ya ce da ita, ki
aika a kira Ɗalhah da Zubairu domin su ma in ji ta bakinsu. Da suka
zo ya tambaye su sai suka ba da amsa irin ta Nana A’ishah, sai ya ce da su, zan
tambaye ku, shin kuna a kan
biyayya ga Sarkin Musulmi ko kun fita daga ɗa’arsa? Idan kuna a kan
biyayya to, ku faɗi irin gyaran da kuke nufi sai a gaya masa ya yi. Sai suka ce masa, mu abinda
ya dame mu shi ne, ƙyale waɗanda suka kashe
Khalifa Usman, domin ƙyale su yin
watsi ne da hukuncin Alƙur'ani.
Ƙa’aƙa’u ya ce, to ga shi kun kashe kusan mutane ɗari shida, amma ga mutum ɗaya ya gagare ku, kuma mutane dubu shida sun ba shi kariya daga gare ku.
Idan ku ka ƙyale shi kun yi watsi da littafin Allah a cewarku,
idan kuma kun ce sai kun kashe shi ɓarnar da za ku
janyo ma wannan al’umma tana da yawa. Yanzu dai kun tono ƙabilancin jahiliyyah ke nan a tsakanin Musulmi.
Da Nana A’ishah ta ji wannan jawabi
nasa sai ta ce, to yanzu mine ne shawara? Sai ya ce, a kwantar da hankalin
mutane. Idan Ali ya iso ku shiga cikin jama'arsa, kowa ya san cewa, kalmarmu ta
zama a haɗe, duk wani kangararre zai ji tsoronmu, fansar jinin
Usmanu kuma sai in da ƙarfi ya ƙare.
Ana iya cewa kusan kowa ya gamsu da
wannan bayanin kuma an tsayu a kansa. A sakamakon haka an yi musayar saƙonni daga ɓangaren Ali da
na mutanen Makka (ina nufin jama’ar Uwar Muminai da su Ɗalhah) kome ya fara komawa daidai.
To, a lokacin da Sarkin Musulmi Ali
ya tasar ma isa Basrah sai ya yi wata huɗuba wadda a cikinta ya ɗauki mataki mai
tsauri a kan
duk wanda aka san yana da hannu wajen kashe Usman, kuma ya sanya dokar kada
wanda ya bi shi daga cikinsu. A nan ne ‘yan tawaye suka fahimci cewa, kashinsu
ya bushe idan suka bari
wannan gyara ya tabbata. Don haka sai suka koma kan teburin shawara, suka kuwa haɗu a kan
sake tada fitina da hasa gobarar yaƙi a tsakanin Musulmi.
A daidai lokacin da Uwar Muminai ta
ke jiran isowar Ali sai ga labari ya zo mata, ta wurin Ka’abu ɗan Sauru, alƙalin garin Basrah
cewa, ga yaƙi can ya sake ɓarkewa a tsakanin mutane. Ya ce, ki yi gaggawa wataƙila Allah zai kwantar da wannan tarzoma idan kika sa
baki. Nan ta ke Nana A’ishah ta hau raƙuminta ta tasar ma wurin da ƙura ta ke tashi, sai ta tarar da Sayyiduna Ali yana ta famar dakatar da
rikici. Da farko Ka’abu ne yake jan ragamar raƙuminta, amma sai ta umurce shi da ya je gaba ya kira mutane zuwa ga
littafin Allah. Tuni ‘yan ta’adda suka kashe Manzon na A’ishah, ita kuma su kayi
ta jifar raƙumin da ta ke a kansa.
Ɗalhah ya samu rauni mai tsanani wanda a sakamakonsa ya koma cikin garin
Basrah bisa ga shawarar Ƙa’aƙa’u, kuma a can ne ya gamu da ajalinsa. Zubairu kuma da
ya lura da sauyawar al’amari sai ya zame jiki daga wurin yaƙin, amma duk da haka sai da wata ƙungiya ta 'yan tawaye a ƙarƙashin jagorancin Amru ɗan Jarmuzu suka bi shi suka kashe shi.
Cibiyar yaƙi ta koma a wurin raƙumin da Uwar
Muminai ta ke a kansa. Sama da mutane arba’in suka rasa rayukansu nan ta ke.
Sayyiduna Ali ya lura da haɗarin wannan
lamari sai ya ba da umurnin a soke wannan raƙumi. Wannan dabarar tasa kuwa sai ta yi nasara domin soke raƙumin ke da wuya sai mutane suka watse daga wurin. Sannan
ya umurci ƙanenta Muhammad ɗan Abubakar tare da Budailu ɗan Warƙa'u da su fitar da ita daga rumfar wannan raƙumi, su nisantar da ita daga fagen yaƙi. Sannan Muhammad ya wuce da ita cikin garin Basrah a
ƙarshen dare in da ta samu mafaka a gidan Safiyyah ɗiyar Harisu uwar gidan Abdullahi ɗan Khalaf.
A ranar litinin 14/6/36 bayan hijira Sarkin Musulmi ya
shiga birnin Basrah bayan da ya jagoranci sallar jana’iza ga dukkan mamatan ɓangarorin guda biyu, kuma ya yi addu’a da neman
gafarar Allah ga duk wanda yake da tsarkakakkiyar niyya daga cikinsu. Sannan ya
haɗu da Nana A’ishah suka jajanta ma juna bisa ga abin da
Allah ya ƙaddara, ya yi mata rakkiya, ya umurci ‘ya’yansa da
wasu mata arba’in daga Basrah su taka ma ta. A wurin bankwana Nana A’ishah da
Ali sun yi wani jawabi mai ban tausai matuƙa, in da ko wannensu ya bayyana juyayinsa ga abinda ya faru da yadda aka
keta umurninsu cikin wannan lamari. Nana A’ishah ta yabi Sarkin Musulmi Ali
tana mai nuni ga tashinsa a gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ta ce kuma bai taɓa muzguna mata ba a tsawon zamansa a gidan a matsayin ƙanen mijinta. Shi kuma a nasa ɓangaren sai ya nanata ma al’ummar Musulmi irin matsayin da Nana A’ishah
ta ke da shi, ya ce kuma, ita matar Annabinku ce a duniya da lahira.
Haka dai yaƙin da ‘yan tawaye suka haddasa ya zo ƙarshe. Mafi ingancin bayani game da hasarar rayuka kuwa shine an rasa
mutane ƙimanin dubu biyu da ɗari biyar (2500) daga rundunar su A'ishah, da kuma dubu huɗu (4000) daga ɓangaren Ali.
Dalillai sun nuna barrantar ko wane ɓangare na Ali da na Aishah daga wannan yaƙi. Alal misali, wanda ya kashe Zubairu ya zo ya yi bushara ga Sayyiduna
Ali cewa ya kashe abokin faɗansa, amma sai
Ali ya nuna ɓacin ransa kuma ya yi masa bushara da wuta! Nana
A'ishah kuma ta yi nadama matuƙa, kuma ta kan yi kuka sosai har
sai ta jiƙe mayafinta wajen goge hawaye. A dalilin haka ne kuma
ta sauya ra'ayinta na yi mata ƙabari a cikin ɗakinta kusa da mijinta (Manzon Allah SAW) da
mahaifinta (Abubakar).[8]
Ali shi ma ya ji takaicin faruwar
wannan al'amari. Ba haka aka so ba, amma ƙaddara ta riga
fata. Ikon Allah! bayan wata biyu kacal da tsaida wannan yaƙi, sai ga wani irinsa ya sake ɓarkewa.
Yaƙin Basasar Siffin
Har Yanzu Mu'awiyah
Raliyallahu Anhu Bai Yi Mubaya'ah ba
Bayan da aka ƙare yaƙin basasar raƙumi, Ali ya aika wani Manzo mai suna Abu Muslim al
Khaulani domin ya jawo hankalin Mu'awiyah a kan haɗewa da sauran al'ummar Musulmi waɗanda su kayi mubaya'a. Amma ga alama wannan karon Mu'awiyah ya fi
tsananin cijewa ma fiye da in da aka fito.
Ali ya sake aika shahararren Sahabin
nan Nu'uman ɗan Bashir, shi ma dai bai ci nasara ba. Daga nan ne
Ali ya yanke shawarar yaƙarsa. Ya fara
tura runduna wadda ta ƙunshi mayaƙa kimanin 6000 zuwa 7000 ƙarƙashin jagorancin Ashtar An Nakha'i domin su fara kai
farmaki a kansa.
Kafin Ali ya aike da rundunarsa kuwa
sai da ya jinjina ƙarfin Mu’awiyah da jama’arsa. Hanyar da ya bi wajen
gano ƙarfin Mu’awiyah ita ce, ya aika wani mutum wanda ya
nuna alamun shi matafiyi ne daga Iraƙi yana mai sanar
da Mu’awiyah cewa, ga Ali nan tafe da rundunarsa zai yaƙe ku. Da Mu’awiyah ya ji wannan labari sai ya sa aka tara
dukkan mutanen Sham in da ya yi huɗuba yana neman
shawarar jama’a game da matakin da za a ɗauka, amma ba wanda ya ɗaga kansa sama
ko yace uffan saboda biyayya. Daga bisani wani mutum da ake kira Zul kila’i ya kada
baki yace masa, kai ne mai yanke hukunci, mu namu shi ne zartarwa. Manzon Ali
ya garzaya ya faɗo masa abinda ya gani. Amma dai Ali bai karaya ya fasa
abinda ya yi niyya ba.
Bayan da Mu’awiyah ya haƙiƙance Ali ya fito
da rundunarsa sai shi kuma ya shirya tasa runduna mai irin yawan waccan, ya kuma
fito domin karawa da su. Amru ɗan Ass ya kawo
masa gudunmawa a daidai wani ruwan tafki da ake kira Siffin. A kan wannan ruwan ne ma aka
ɗan samu gumuzu kafin hankali ya kwanta a
soma tattaunawa tsakanin wakilan Ali da na Mu'awiyah, har a cimma yarjejeniyar
yin amfani da ruwan tare da juna.
Da yake Ali ya gano muhimmancin
mutanen kufa a yaƙin da aka yi a baya, ya aika Manzo na musamman wanda shi ne
Hashimu ɗan Utbata ɗan Abu waƙƙasi don ya sake nema masa goyon bayansu ta hanyar
gwamnansu
Abu Musa Al Ash'ari. Shi kuwa Abu Musa kamar yadda muka faɗa a baya, yana daga cikin masu ra'ayin farko na
ganin bai cancanta ayi yaƙin ba. Wannan
kuwa shi ya janyo Ali ya tuɓe shi daga
kujerarsa, ya naɗa Ƙurazah ɗan Malik a madadinsa.
Sannan ya sanya Ammar ya je ya janyo hankalin mutane don su ba da goyon baya.
Ya kuma nemi ɗansa al Hassan
da ya rufa masa baya, duk da yake shi ma ba mai ra'ayin yaƙin ne ba. Al Hassan kuwa ya yi ɗa'a ga mahaifinsa, amma ba inda yake cewa uffan, sai
dai ya zauna saman mimbari, Ammar kuma ya gabatar da huɗuba a ƙasa da shi.
Mutanen
kufa kuwa sun amsa wannan kira na Sarkin Musulmi domin sama da mutane dubu goma
sha biyu ne suka fita don mara masa baya.
Ammar
ya ci gaba da bayar da goyon bayansa ga Ali har ajalinsa ya cim masa a hannun ɗaya daga cikin mutanen Mu'awiyah. Babu shakka kuwa
mutuwarsa ta kawo ruɗani mai yawa a tsakanin
jama'ar Mu'awiyah. Domin kuwa da yawansu (musamman ma dai Sahabbai daga
cikinsu) sun canza sheƙa daga wajen Mu'awiyah
suka koma ɓangaren Ali saboda la'akari da
wani sanannen hadisi a tsakaninsu wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama yake cewa, Ammar zai gamu da ajalinsa a hannun wata ƙungiya mai tsallake iyaka.
Mu'awiyah
daga nasa ɓangaren, ya yi riƙo da cewa, wannan ƙungiya
jama'ar Ali ake nufi da ita, domin kuwa su suka fidda Ammar suka kai shi
mahalaka.
Abin
da ya fi kome ban mamaki a wannan yaƙin shi ne, irin
yadda abokan faɗa suka rinƙa hulɗa da junansu.
Idan aka tsaya Sallah kowa yana iya shiga a ɗaya ɓangaren ya yi bukatarsa. A wuri ɗaya suke ɗibar ruwa (bayan
an yi yarjejeniya a kan
haka). In yamma ta yi aka tsaida buɗa wuta Ali ne yake
yin Sallah a kan
mamatan ɓangarorin gaba ɗaya. In aka kama
fursuna ba'a kashe shi sai dai a ƙwace masa
makami, in ya rantse ba zai ci gaba da yaƙi ba a sake shi,
in ya ƙiya aci gaba da tsare shi. Haka
kuma ba maganar ganima a wannan yaƙi. Wannan shi ya
sa malamai suka ce ba'a taɓa irin wannan yaƙi ba kafinsa, suka gina hukunce hukuncen yaƙi da 'yan tawaye a kansa.
Dakatar Da Buɗa Wuta
A lokacin da yaƙi ya yi zafi, duka ɓangarorin
biyu sun sha wuya, kuma jama'a kamar ƙara ingiza su ga
yaƙin ake yi, sai Mu'awiyah ya nemi a
tsagaita wuta bisa ga shawarar na hannun damansa Amr ɗan Ass. Ali bai yi wata wata ba sai ya karɓi wannan tayin. Daman
dai an gaji da wannan al'amari, kuma an ɗanɗani ɗacinsa har a maƙoshi. An dai cimma yarjejeniyar kafa kwamiti wanda za
a ɗora masa alhakin fito da hanyar samun
zaman lafiya da fita daga wannan kiki kaka da Musulmi suka samu kansu a cikinsa.
Kuma Ali ya soma nadama akan shawararsa ta yaƙar
waɗanda ya kira 'yan tawaye, domin ya lura
babu wani alheri da zai auku a dalilin wannan yaƙi,
gurinsa na tanƙwasa mutanen
Sham da tilasta su yin mubaya'a ya zamo abu mai matsananciyar wuya, ga kuma
jinainan Musulmi ana ta zubarwa.
Daga cikin abin da ke bayyana Ali
ya soma nadama ya fara komawa ga ra'ayin waɗanda suka nuna masa
kar ayi yaƙi shi ne, wakilta Abu Musa da ya
yi a cikin kwamitin sulhu da aka kafa, mun kuma sani shi Abu Musa ra'ayinsa ke
nan wanda a kansa Ali ya tuɓe shi daga muƙaminsa, Sannan ya ƙaurace
ma yaƙin kuma ya rinƙa kiran mutane a kan kar su bai wa ko wane ɓangare goyon baya.
An dai shata ranar aikin wannan
kwamiti, wadda ita ce ranar 27 ga watan Ramadan 37 bayan hijira.
An kuma sanya wurin haɗuwarsu, shi ne, Daumatul
Jandal. Wanda ya ƙaddamar da wannan
kwamiti a gaban jama'a shi ne, Ash'asu ɗan ƙais, a
madadin ɓangarorin masu jayayya da juna.
Ash'as, wanda ke goyon bayan Ali, ya bai wa jama'a tabbacin za a yi aiki da duk
hukuncin da wannan kwamiti ya zartas.
Riwayar Imamul Zuhuri ta nuna
cewa, a wannan yaƙin basasa na
Siffin an yi hasarar jama'ar da yawansu ya janyo aka rinƙa yi musu ramukan tarayya, ana haɗa kimanin mutum hamsin a ƙabari ɗaya.
Game da fursunonin da aka kama, Mu'awiyah
ya fara sakin wani mutum ɗaya wanda ya
neme shi alfarma a cikin wata ƙissa mai ban
dariya. Domin kuwa wannan fursuna ya taso ne da mari (sarƙa) a ƙafarsa ya faɗi a gaban Mu'awiyah, sai ya ce, ka yi mini alfarma
ka sake ni domin kai kawuna ne. Sai Mu'awiyah ya ce masa, to ya aka yi ni ban
sanka ba? Sai ya ce, ai ni ɗa ne daga cikin ɗiyan ƙanwarka Ummu
Habiba (Uwar Muminai), don haka kai kawuna ne, kuma kawun ko wane mumini.
Bayan ƙare yaƙin, Ali daga
nasa ɓargaren ya saki dukkan fursunonin
jama'ar Mu'awiyah da suka rage a wurinsa, abinda ya sanya Mu'awiyan shi ma ya saki
fursunonin ɓangaren Ali. Da
haka wutar yaƙin ta kwanta.
Yaƙin
basasar Siffin dai ya gudana daga ranar Laraba zuwa jum'ah a farkon shekara ta Talatin
da bakwai bayan hijira. Kuma an yi hasarar rayuka masu ɗinbin yawa daga ko wane ɓangare kamar yadda riwayoyi su ke nunawa.[10]
Banbancin Ra'ayin
Sahabbai Dangane Da Wannan Yaƙin
Sahabban
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun kasukashi uku dangane da
wannan yaƙin.
Kashi
na farko su ne waɗanda su ke da
ra'ayin cewa, yaƙin bai ma dace
ba gaba ɗaya. Kuma kan al'umma ya wajaba ya haɗu a wuri ɗaya maimakon yaƙi a tsakanin junansu. Irin waɗannan bayin Allan sun yarda da khalifancin Ali kuma
sun yi masa mubaya'a, amma dai yaƙin ne ba su
aminta da aukuwarsa ba. Waɗannan su ne
akasarin Sahabbai[11],
a cikinsu har da Sa'adu ɗan Abu Waƙƙas, Muhammadu ɗan Maslamah,
Abdullahi ɗan Umar bin khattabi, Abu Musa al
Ash'ari (Gwamnan Kufa), Abu bakrata Al thaƙafi, Abu Mas'ud
al Ansari da makamantansu. Hujjojin waɗannan bayin
Allan suna da dama, kuma sun haɗa da duk
hadissan da ke magana a kan
barin yaƙi lokacin fitina. A cikinsu ma
har da waɗanda Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi alƙawari da su
cewa, duk halin da aka shiga kar su yi yaƙi da Musulmi.[12]
Kashi na biyu kuwa, suna ganin
cewa, tun da yake Ali shi ne naɗaɗɗen Sarkin Musulmi, wanda ya wajaba a yi wa biyayya,
wajibi ne a yaƙi dukkan wanda
ya fanɗare masa. A kan haka suna yaƙi tare da shi a kan Mu'awiyah da jama'arsa. Suna kuma kafa
hujja da dalillai na Alƙur'ani da hadisi
masu nuna wajabcin biyayya ga shugabanni.
Daga cikin waɗanda suka ɗauki wannan
matsayin har da fitattun Sahabbai irin su Abdullahi ɗan Abbas, Ash'as ɗan ƙais, Ammaru ɗan Yasir, Maliku
ɗan Ka'abu al Hamdani da dai sauransu. Ga
wata tattaunawa da ta gudana a tsakanin Ammaru da Abu Mas'ud al Ansari (daga
cikin masu ra'ayin farko na ƙauracewa yaƙin) a kan
wannan mabanbancin ra'ayin nasu, Buhari ya ruwaito ta kamar haka:
Abu
Mas'ud: Ya kai Ammar! Ka sani duk a cikin tsaranka babu wanda ya kai matsayinka
a wurina. Kuma ba ka taɓa sanya kanka a
cikin wani lamari ba wanda yake aibanta ka a wurina sai gaggawar da kake yi a
cikin wannan fitina.
Ammaru:
Ya kai baban Mas'ud! Ni kuma wallahi ba ka da wani aibi a gurina kai da
abokinka (Amr ɗan Ass) wanda yake
aibata ku tun bayan rasuwar Manzon Allah kamar janye jikinku daga wannan lamari
(yana nufin taimaka ma Ali).
A yayin da kashi na uku na Sahabbai
su ko su ke ganin cewa, Mu'awiyah ne yake da haƙƙen
ya nemi fansar jinin ɗan uwansa
khalifa Usman, kuma dole ne a taimaka masa don ya cimma biyan wannan buƙata. Suna kafa hujja da ayar Suratul Isra'i wadda
Allah a cikinta yake cewa,
) وَمَنْ قُتِلَ مَظْلُومًا
فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِ سُلْطَانًا فَلَا يُسْرِفْ فِي الْقَتْلِ إِنَّهُ
كَانَ مَنْصُورًا (33)( سورة
الإسراء: 33
Ma'ana:
Wanda duk aka
kashe shi a kan
zalunci to, haƙiƙa mun sanya hujja ga waliyyinsa (a kan ya nemi fansa), sai dai kar ya wuce iyaka
a wajen kisan (ramuwa), domin lalle shi abin taimakawa ne.
Suratul Isra'i,
Aya ta 33
Haka kuma suna kafa hujja da
hadissan da suka bayyana cewa, fitina zata auku, kuma idan ta auku Usman shi yake
a kan gaskiya
tare da mutanensa. Sai suna ganin su ne mutanen Usman tun da su ke faɗa dominsa.
Daga cikin masu wannan ra'ayi
akwai Sahabbai kamar Amru ɗan Ass, Ubadata ɗan Samitu, Abud Darda’i, Abu Umamata al Bahili, Amru
ɗan Ambasata da dai sauransu.
Ƙaddara Ta Riga Fata
Muna
iya lura daga abinda ya gabata cewa, duk yaƙe - yaƙen nan ba wanda aka yi shi don a tunɓuke Ali daga muƙaminsa, hasali
ma a yaƙin Siffin shi ne ya kai hari,
kuma ya fara yaƙin. A Jamal kuma
ya iske fitina an riga
an rura wutarta, sai aka jawo shi da ƙarfi da shi da
su Ɗalhah a cikinta.
Idan
muka yi la'akari da hadisin da Ali ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama cewa, A yi bushara ga duk wanda ya kashe Zubairu da wuta,
da hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma Ɗalhah bushara da zai yi shahada za mu gane cewa, suna
da uzuri a yaƙinda ya shiga tsakaninsu
da Ali. Domin kuwa dama ba shi suka zo yaƙa ba, cim masu ya
yi suna faɗa da makasan Usman, ya zo ya kira
su zuwa bin doka da mayar da al'amarin a hannun gwamnati don kada bangon Musulunci
ya ida tsagewa, ana haka sai 'yan fitina suka tada yaƙi a tsakaninsu.
Wannan
ra'ayin da Ali ya yi tsayin daka a kansa na kar a kashe 'yan tawaye sai hankali
ya kwanta ba shi da wani banbanci da ra'ayin shi wanda aka kashen, don kuwa
Usmanu ai shi ya hana tun da farko a karkashe su, shi ma yana gudun irin abin
da shi ne Ali ke gudu a yanzu.
Shi
ma Mu'awiyah a kan
wannan batu ne su kayi yaƙi da Ali, shi yana
ganin haƙƙinsa ne a ba shi makasan ɗan uwansa ya gama da su, ko a bar shi da su a gani.
Shi kuma Ali na cewa, in kana son haka, ka amince da shugabancin da aka naɗa tukuna, sai ka kawo ƙara
ga gwamnati ta duba ta yi magani. Mu'awiyah na nan a kan bakarsa, ni ba zan yi
ma ka mubaya'ah ba in dai har ba za ka iya ɗaukar fansar
wanda ya gabace ka ba, kuma ba za ka ba ni dama ni da ni ke da haƙƙe ba.[13]
Ikon
Allah, wai na kwance ya faɗi! To, ya za ka
yi da wannan lamari? Idan ka diba kowa da hujjarsa, ko da yake hujjar Ali ta fi
ƙarfi. To, amma yaƙin ba wani alfanu a cikinsa. Don haka ne ma waɗanda suka ɗauki matsayin ƙaurace ma yaƙin suka fi
rinjaye ta fuskar samun madogara a Shari'ah, kuma shi ya sa Ali ya gwammace da
ma ya bi ra'ayinsu har ma ya kan
ce ma ɗansa al Hassan, kaicona da na bi
shawararka! Ina ma na mutu tun shekaru ashirin da suka wuce![14].
Ganin haka ya sa al Hassan da ya karɓi mulki bayan
mahaifinsa ya yi gaggawar samar da kwanciyar hankali ta hanyar sauka daga haƙƙensa wanda Musulmi suka zaɓe shi kamar yadda za mu gani a nan gaba. Kuma Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yaba masa a kan wannan abin da zai yi tun ma bai yi shi
ba.
Laifin
Mu'awiyah wanda mu ke fatar Allah ya yafe masa tare da sauran duk waɗanda abin ya shafa shi ne, rashin yin mubaya'ah a lokacin
da ya cancanta, amma kuskure ne mu ɗauka cewa, yana
neman khalifancin ne tun da farko.
Sannan
yana da kyau mu sani cewa, ko wannensu, Ali da Mu'awiyah sun ji zafin abinda ya
faru daga baya. Ali ya kasance yana cewa, "kaicona da na mutu tun shekaru
ashirin da suka gabata".[15]
Shi kuma Mu'awiyah ya yi nadama a lokacin da ya je aikin Hajji, ya je ziyarar Madinah
sai ya samu wasu Sahabbai waɗanda suka haɗa da Sa'adu ɗan Abu Waƙƙas da Abdullahi ɗan Umar da kuma
Abdullahi ɗan Abbas. Anan ne Sa'ad ya ba shi
labarin cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma Ali,
"Kana tare da gaskiya, kuma gaskiya na tare da kai duk in da ka
juya". Mu'awiyah ya zare masa ido yana mai barazanar cewa, sai ya kafa
masa hujja a kan
cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faɗi haka. Wannan ya sa suka tashi gaba ɗaya suka je wurin Nana Ummu Salamah wadda ta
tabbatar masu da gaskiyar maganar. Anan ne fa Mu'awiyah ya bayyana nadamarsa
yana cewa, Ya baban Ishaƙ! Ba abin zargi a
kanka bayan ka ji wannan daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
sai ƙin bin Ali da ka yi.[16]
Ni kam da na ji wannan daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
Wallahi da na yi hidimarsa har ƙarshen rayuwata.[17]
Bango Ya Tsage A Rundunar Ali
Ga
dukkan alamu abin da Sayyiduna Ali ya kauce ma a lokacin da ya karɓi zaɓin yin sulhu na
rabuwar kan Musulmi
sai da ya auku. Domin kuwa dawowarsa daga wannan yaƙi ke da wuya sai ya lura da wata sabuwar ƙungiya ta fita daga cikin jama'arsa. Sun dai warware
mubaya'arsu daga Ali har ma sun naɗa wani shugaba
mai suna Shabas
ɗan Rib'iyyu, sun kuma naɗa limamin da zai rinƙa
ba su Sallah, shi ne, Abdullahi ɗan Kawa. Wannan ƙungiya ita ake kira Khawarij.
Dalilin
warewar Khawarij kuwa shi ne, a cewarsu, wai kafa kwamitin da aka yi kafirci
ne. Saboda an sanya 'yan kwamiti a matsayin ɗagutu (masu
yanke hukunci) koma bayan Allah, har ma suka kafa hujja da zancen Allah da yake
cewa,
(إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا
لِلَّهِ)
Ma'ana:
"Hukunci bai
zamo ba face ga Allah".
Suratul
An'am: 57
Wannan
sabon ƙalubalen ya daɗa dagula lissafin Sarkin Musulmi Ali, ya kuma ƙara ɗauke hankalinsa
daga ɗamarar da ya sha ta karya ƙarfin mutanen Sham. Amma kuma ya bi abin a hankali
ta hanyar aikewa da saƙonni da manufar
fahimtar da su. An kuma ci nasara a kan wani ɓangare
nasu, amma har wayau an samu waɗanda suka cije,
adadinsu ba zai kasa dubu huɗu ba (4000) a ƙarƙashin jagorancin
Abdullahi ɗan Wahbu wanda kuma aka sani da
Rasibi. Daga ƙarshe ya zama
tilas Ali ya yaƙe su.
Tsugunne Ba
Ta Ƙare Ba
Da
ranar haɗuwar kwamiti ta zo, jama'a sun
hallara a wurin da aka shata don su shedi abin da wakillan nan biyu za su
tattauna. Daga cikin waɗanda suka shedi
wannan lamari daga ɓangaren Ali
akwai: ƙaninsa Abdullahi ɗan Abbas da Ash'as ɗan
ƙais da Abdullahi ɗan Ɗufail da Uƙbatu ɗan Ziyad da Hujru
ɗan Yazid a cikin mutane da dama.
Daga
ɓangaren Mu'awiyah kuwa, an samu halartar
ƙaninsa Utbah ɗan Abu Sufyan da Abul A'war al Sulami da Mukhariƙ ɗan Haris da
Subai'u ɗan Yazid da Abdur Rahman ɗan Khalid ɗan Walid, su ma a
cikin mutane da dama.
Tattaunawar waɗannan
'yan kwamiti ba ta yi nisa ba sai da suka cimma matsaya cewa, wannan lamari
yafi ƙarfin su yanke shi su kaɗai, don haka suka nemi a gayyato mutanen Shura, ana
nufin waɗanda su Umar ya wakilta a lokacin
rasuwarsa don su yi zaɓen shugaba.[18]
To, amma anya kuwa za a cimma wata manufa ko da an kira su, bayan kunnowar kan da khawarij su kayi?
Tun a wannan lokaci dai Ali ya
fahimci cewa, tsugunne fa ba ta ƙare ba, ga shi dai
yanzu ana son a raba hankalinsa gida biyu. Daga nan ne ya yanke shawarar ƙyale mutanen Sham domin ya fuskanci haɗarin da ke gabansa na cikin gida daga ɓangaren khawarij. Su ma khawarij ɗin Ali ya yi masu jinkiri har sai sun bayyana wani
abin da zai wajabta yaƙarsu a fili.
Ana cikin haka ne khawarij suka
kashe wani Sahabi ana ce da shi Abdullahi ɗan khabbab tare
da matarsa wadda suka soke cikinta suka fitar da ɗan
da ke cikinta. Matakin farko da Ali ya ɗauka kuwa shine,
ya aike masu wani ɗan saƙo da zai isar masu da gargaɗi, sai nan take suka kashe shi wannan ɗan saƙo.
Daga nan ne Ali ya shelanta yaƙarsu a madadin yaƙar Mu'awiyah, ya
fatattake su har ya kasance ba waɗanda suka tsira
sai kaɗan daga cikinsu.
Wani abin ban mamaki ga khawarij shi ne, yadda
su kayi fice wajen kafirta Musulmi amma kuma suka fi kowa yawan ibada, kamar
yawan salloli da azumi da karatun Alƙur'ani har ma
ana yi masu suna Ƙurra'u (Makaranta ko
Masu karatu). Ga su kuma da tsananin haƙuri a wajen
karawa da abokan gaba. Dalillan da suka sa wasu daga cikin rundunar Ali suka ji
tsoron yin arangama da su.
Amma wani abin sha'awa da yake
nuna tsarkin zukatan Sahabbai shi ne cewa, duka ɓangarorin
can guda uku da muka ambata a baya, a wannan karo sun goyi bayan Ali a kan wannan yaƙi. An samu da dama daga cikin kashin farko waɗanda mu ka ce sun ƙaurace
ma yaƙar Mu'awiyah sun zo a wannan karon sun
yaƙi Khawarij a ƙarƙashin tutar Ali. Wataƙila
wannan ba zai rasa nasaba da hadissai da shi Ali da kuma wasu Sahabbai suka
ruwaito ba a kan
yaƙar Khawarij da falalarsa da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana.[19]
Hujjar da ba za a same ta a yaƙar Mu'awiyah da
mutanen Sham ba domin shi wannan ijtihadi ne daga Sarkin Musulmi, ba umurni ne
daga Annabi ba.
Ali Ya Yi
Shahada
Waɗanda
suka tsira daga yaƙin da muka
ambata daga cikin Khawarij su ne suka zama ajalin Sarkin Musulmi Ali tun kafin
babban kwamiti wanda ya haɗa mutane biyu na
farko da muka ambata tare da mutanen shura su fara zama don gano bakin zaren
wannan matsala. Khawarij dai sun shirya wata maƙarƙashiya wadda ke da nufin kawo ƙarshen Ali da Mu'awiyah da Amru ɗan Ass baki ɗaya, waɗanda su ne ɗagutai na wannan
zamani a cewarsu. Sun kuma shata rana da lokacin da za su gudanar da wannan ɗanyen aiki. Ranar kuwa ita ce, ranar 17 ga Ramadan, shekara
ta Arba’in bayan hijira a daidai lokacin da ko wanensu yake
fitowa sallar asubahi.
Bisa ga haka ne, Abdul Rahman ɗan Muljam ya tasar ma Kufa, mazaunin Sayyiduna Ali.
Al Barak ɗan Abdullahi shi kuma ya je Sham,
mazaunin Mu'awiyah, a yayin da Amru ɗan Bakr al
Tamimi zai tasar ma wajen Amru ɗan Ass. Da
lokaci ya yi, ko wannensu ya zartas da abin da aka ɗora masa.
Shi dai Al Barak da ya je wajen Mu'awiyah,
bai samu sa'arsa ba, saboda an ɗago shi tun bai
kammala mugun aikin ba. Sai dai ya ji ma Mu'awiyah rauni a cinya, wadda ya yi
kwanukka yana jinyarta. A kan
wannan dalili Mu'awiyah ya nemi matsara a karon farko a tarihin sarakunan Musulunci.
Shi ma dai Amru kwanansa suna gaba, domin a ranar da aka shirya yin wannan
ta'asa an yi dace ba shi da lafiya. To, da yake cikin duhun asubahi ne, ɗan saƙon khawarij sai
ya kashe limamin da ya bayar da Sallah a rannan zaton cewa, gwamnan ne da
kansa. Don haka Na'ibi wanda kuma shi ne kwamandan 'yan sanda, kharijah ɗan Huzafa sai ya yi shahada a madadin mai gidansa.
Amma a kufa, an zartar da wannan aika aika kamar yadda khawarij suka tsara ta,
domin ɗan Muljam ya kai hari ga Sarkin Musulmi
Ali a kan
hanyarsa ta zuwa Masallaci, ya kuma same shi ta inda yake buƙata. Da wannan ne khalifan Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama na huɗu ya samu
shahada kamar yadda magabatansa guda biyu (Umar da Usman) suka samu, ya kuma
huta da waɗannan fitinu da suka dabaibaye
mulkinsa na tsawon shekaru huɗu.
An bayyana cewa, Mu’awiyah ya
nuna damuwa ainun akan kisan Ali, har sai da matarsa tace masa, ba kai ne jiya
ka gama yaƙarsa ba? Ya ce mata, kin san irin
mutumin da aka yi hasara kuwa?[20]
Ali ya yi shahada a ranar 17 ga
Ramadan 40 bayan hijira. Don haka mulkinsa ya kasance
shekaru uku da wata tara . Ya kuma bar zuri'a
mai yawa wadda ta haɗa da 'ya'ya maza
14 da ‘ya’ya mata 17. Da yawansu sun yi shahada a karbala tare da wansu Hussaini kamar yadda za
mu gani a nan gaba. Waɗanda suka bar
zuri'a daga cikinsu sun haɗa da Hassan da Hussaini
(ta wajen ɗansa Abubakar Zainul Abidin) da
Muhammad (wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah) da kuma Abbas da Umar.[21]
[1]
A Madina ba a yin gwamna
na din din din a wannan lokaci, saboda Khalifa shi yake riƙe da ita kamar yadda yake a zamanin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama. Amma duk lokacin da Khalifa zai fita daga Madina saboda
wani dalili to, ya kan
naɗa ma ta gwamna wanda aikinsa zai ƙare da zaran Khalifa ya dawo. Da Allah zai ƙaddara wafatinsa kuwa to, da gwamnan Madina shi zai
yi riƙon ƙwarya kafin
al'umma ta tsai da sabon shugaba. Don haka matsayin gwamnan Madina a lokacin ya
kai ace masa mataimakin sarkin musulmi.
[2]
Dalilin wannan magana shi
ne, Abdullahi ɗan Umar ya shiga
wurin babansa bayan da ya kafa wancan kwamiti, sai shi Khalifa ɗin ya ce masa, in da mutane za su zaɓi mai sanƙon can tabbas ya
ɗora su a kan hanya. Sai ɗan nasa ya ce masa, to, me zai hana ka ayyana shi?
Sai ya ce, a'a, ba zan ɗauke ta a raye
ba kuma in ɗauke ta bayan na
mutu.
[3]
Wannan yana ƙara nuna maka cewa, waɗannan
ja'irai ba Usman su ke nufi da yaƙi ba, domin kuwa
duk wanda ya shirya juyin mulki za ka tarar yana da wani tsayayyen ɗan takara da zai kafa. To, su kam ba su da kowa.
Gurinsu dai shi ne fitina, kuma duk yadda ta kaya sun aminta.
[5]
Duba Imam Ali, na
Rashid Ridha, bugun Darul Kutub Al Ilmiyyah, 2001, shafi na 74. Kar dai mu
manta cewa, Zubairu fa shi ne ya janye haƙƙensa ya bar wa
Ali a lokacin da suka yi takara bayan rasuwar Umar. Ko bayan mutuwar Usman ma
Zubairu yana cikin waɗanda aka nema
don a naɗa shi amma ya kauce. Saboda haka
kada wani ya yi tunanin Zubairu yana da wata jayayya ne ga karɓar ragamar mulki da Ali ya yi. Banbancin ra'ayinsu
anan shi ne na lokacin tunkarar 'yan ta'adda. Kuma Zubairu da ire irensa su na
ganin ra'ayin Ali ya yi sassaucin da ba za su iya ɗauka ba. Don haka suka yi gabansu da ɗaukar matakin da suka ga ya dace. Babu shakka kuwa
sun yi kuskure a wannan mataki, amma Allah zai ba su ladar ijtihadinsu na ganin
sun aza al'umma ga abin dasuka ƙudurta shi ne
daidai kamar yadda Allah zai ba Ali ladar nasa ijtihadin na yaƙar waɗanda suka ƙi yi masa mubaya'a tare da cewa da ya barsu, ya yafe
sashen haƙƙensa da wannan ya fi zama alfanu
ga Musulunci da Musulmi.
[6]
Wannan
ingantacciyar magana ce duk da ya ke Malam Ibnul Arabi ya yi suka a kan ta a cikin
littafinsa Al Awasim Minal Ƙawasim. Don tabbatar da
ingancinta ka duba Al Musnad na
Imam Ahmad (6/52) da Al Mustadrak na Hakim (3/120) da Fathul Bari na Ibnu Hajar
(13/45) da kuma Silsilatul Ahadis As Sahiha na Albani (1/473). Amma shi
Malam Ibnul Arabi ya damu ne da riwayar maƙaryata wadda ta
ce, Ɗalha da Zubairu sun yi mata shedar ƙarya suka ce wannan wurin ba shi ne Hau'ab
ba, don haka sai ya raunana labarin gaba ɗaya.
[7]
Wannan dai shi ne
hukuncin Allah. Domin kuwa a Makka ma an koro sabon gwamnan da Ali ya tura, shi
ne, Khalidu ɗan Ass. Amma
sababbin gwamnonin da ya tura a Yaman (Ƙaninsa Ubaidullahi ɗan
Abbas) da Masar (Ƙais ɗan Sa'ad) ba su gamu da wata tsangwama ba. A Makka ɗin ma dai daga baya ya naɗa ƙaninsa Ƙusamu ɗan Abbas, kuma
ya samu karɓuwa.
[9]
Yana
da kyau mu san matsayin waɗannan Sahabban
guda biyu. Shi dai Abu Musa daɗaɗɗen ma'aikaci ne kuma gogaggen ɗan siyasa (idan za mu iya kiran sa haka, domin
siyasa tana nufin mulki). Ya yi gwamna a zamanin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama har sau biyu, a garuruwan Zubaid da Adan. Duk a tsawon
mulkin Umar kuma shi ne gwamnansa na Basra ,
daga baya ya samu canjin aiki zuwa Kufa a zamanin Usman. Ali bai cire shi daga
muƙaminsa ba da farko sai bayan da
al'amurra suka rikice. Haka kuma yana cikin waɗanda
suka hardace Alƙur'ani tun a
zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sa'annan ƙwararren masanin Shari'a ne wanda har an ƙirga shi daga cikin masanan Shari'a guda shida waɗanda ke fatawa a Masallacin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama tun a zamaninsa. A lokacin mulkin Ali kuma an shedi cewa,
ba wanda ya kai ilminsa in ban da Ali. Shi kuma Amr ɗan Ass shi ne wanda Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yaba da cewa, mutane sun musulunta, amma Amru ya yi imani
(yana nuni ga ƙarfin
addininsa). A lokacin da ya musulunta da kansa ne ya yi hijira zuwa Madina
bayan sulhin Hudaibiyah, a lokacin al'amarin Musulunci bai yi ƙarfi ba. Saboda kaifin basirarsa, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya taɓa sa ya yi
hukunci a tsakanin wasu mutane, in da har ya ce, in yi hukunci a gabanka Manzon
Allah? Ya ce, eh. Ka yi, shi mai hukunci idan ya yi hukunci ya yi daidai yana
da lada biyu, idan ya yi kuskure yana da lada ɗaya.
(Duba wannan ƙissar a cikin Sahihul
Bukhari, Kitabul I'tisam 8/157). Shi ma dai Amru ɗan Ass ya fara riƙa muƙami ne a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama sa'adda ya jagorantar da shi ga yaƙin
da aka sani da suna Dhatus Salasil.
[10]
Sai dai wasu riwayoyin
sun wuce hankali. Domin kuwa yaƙin gaba ɗayansa bai wuce kwana uku ba, ana tsayawa a yi
Sallah, kuma ba a yi da dare. Idan aka tara
sa'oin yaƙin ba za su wuce awa 30 ba. Amma
sai ga wasu riwayoyi na cewa, an kashe sama da mutum 70,000. Ko a Ƙadisiyyah kuwa mutum 8,500 ne a ka kashe, kuma duk
masana tarihi sun haɗu a kan cewa, yaƙin Siffin bai yi zafin na ƙadisiyyah ba. Haka dai ma su ƙarin gishiri a labari su ke yi a ko wane lokaci.
Duba littafin Asmal Maɗalib Fi Sirati
Amiril Mumina Ali bin Abi ɗalib, na Dr. Ali
Muhammad al Silabi, (2/653-654).
[11]
Al Hassan ɗan Abil Hassan al Basri – ɗaya daga cikin manyan tabi'ai da suka yi zamani da
Sahabbai - ya ce, a lokacin da fitina ta auku Sahabbai da su ke raye yawansu ya
kai dubu goma, amma ba ka samun talatin daga cikinsu a waɗannan fitinu. Imamu Ahmad ya ruwaito wannan a
Musnad. Ibnu Taimiyyah ya ce isnadin wannan magana na daga mafi ingancin isnadi
da ake riwaya da shi a bisa doron ƙasa. Duba Minhajus
Sunnah nasa (3/186).
[12]
Duba Sahih al Bukhari,
kitabul Fitan, (8/95) da Sunan al Tirmidhi, kitabul Fitan, (3/332) da
kuma Musnad Ahmad (4/225).
[16]
Sa'adu
bai bi Ali ba don yana ganin ko Ali na da haƙƙi barin haƙƙin yafi zama alheri. Ali kuma daga baya ya yaba ma
matsayin Sa’adu da Abdullahi ɗan Umar na
rashin shiga wannan yaƙi kamar yadda
yazo a Fathul Bari na Ibnu Hajar (12/67).
[17]
Duba
Tarikhu Dimashƙ na Ibnu Asakir,
(22/246). Wannan Hadisin kuwa yana cikin littafin Al Mustadrak na Hakim, (3/119) kuma ya inganta shi.
[18]
To, amma fa ba ana nufin
su sauke Ali su zaɓi wani shugaba
ba, domin Ali shugaba ne zaɓaɓɓe wanda dukkansu 'yar majalisar shurar sun yi masa
mubaya'a a Madina. Ba akan shugabancinsa ake jayayya ba, a kan haƙƙensa na mubaya'a
da haƙƙen Mu'awiyah na ɗaukar fansa, yaya za a yi a sasanta? Maganar cewa
wai, 'yan kwamiti sun zartas da a cire Ali, ko kuma Amru ya yaudari Abu Musa na
daga cikin batutuwa marasa tushe waɗanda wasu maƙaryata da ba su san girman waɗannan mutanen ba suka ruwaito.
[19]
Ka duba hadissan falalar
yaƙar khawarij a cikin Sahihul Bukhari,
Kitabul Fitan, Babu Ƙatlil Khawarij.
[21]
Duba
Itti'adhul Hunafa Bi Akhbaril A'immatil Faɗimiyyin Al Khulafa, na Maƙrizi, juz'i na ɗaya, za
ka same shi a duniyar gizo a kan
wannan layin: http://www.alwarraƙ.com.
No comments:
Post a Comment